Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da dakatar da Kwamishinan Zaben Jihar Adamawa, Hudu Yunusa Ari, har zuwa lokacin da Sufeto Janar na ‘yan sanda zai kammala bincike a kansa.
Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da daraktan yada labarai ya fitar a ofishin sakataren gwamnatin tarayya, Willy Bassey.
- Bunkasuwar Kasar Sin Mai Inganci Ta Ingiza Kwarewar Jama’arta
- Xi Ya Aika Sakon Murnar Cika Shekaru 100 Da Kafa Jami’ar Yunnan
Shugaban kasa ya ba da umarnin gudanar da bincike cikin gaggawa tare da gurfanar da shi gaban kuliya.
Har ila yau, shugaban kasa ya ba da umarnin binciken babban sufeton ‘yan sanda, da darakta-janar na ma’aikatar harkokin waje, da kwamandan rundunar tsaron farin kaya ta Nijeriya, game da rawar da jami’ansu ke takawa wajen bayar da taimako da gudanar da ayyuka ga Barista Hudu Yunusa Ari idan har aka same shi da laifi.
Tun da fari dai Kwamishinan zaben ya ayyana ‘yar takarar jam’iyyar APC, Sanata Aishatu Dahiru Binani a matsayin wadda ta lashe zaben gwamnan Jihar Adamawa, tun kafin kammala tattara sakamakon zaben.
Lamarin da ya haifar da rudani a Jihar.