Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jajantawa wadanda suka rasa ‘yan uwansu a hare-haren ta’addanci na baya-bayan nan a jihohin Sokoto, Kaduna da Filato, inda ya umurci jami’an tsaron kasar da su kawo karshen kashe-kashen.
Shugaban, a wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban, Garba Shehu, ya fitar a ranar Talata, bayan rahotannin da aka samu kan asarar rayuka da dama a hare-haren, ya kuma kara ba da tabbacin goyon bayan gwamnatin tarayya ga jihohi, inda ya kara da cewa “Mun ba Shugabannin tsaro cikakken ‘yanci don kawo karshen ‘yan Ta’adda da munanan ta’asarsu.”
“Na yi Allah-wadai da wadannan munanan hare-haren a kasar nan. Ina so in tabbatar wa jihohi cewa duk wani goyon baya da ya dace, don kawo karshen Hare-haren ‘yan Ta’adda daga gwamnatin tarayya zamu tabbatar musu.
“Damuwa ta a kullum tana tare da iyalan Wadanda suka rasa ‘yan uwansu da abokansu.
“Allah ya sa wadanda suka ji rauni su warke cikin gaggawa,” in ji shugaba Buhar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp