Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya isa jihar Legas a ranar Litinin da yamma domin ziyarar aiki ta kwanaki biyu tare da kaddamar da jerin ayyuka da gwamnatin jihar Legas ta gudanar.
LEADERSHIP ta rawaito cewa an yi wa bikin taron lakabi da cewa bikin kaddamar da ayyuka don bunkasa ci gaban jihar Legas da kyautata rayuwar al’uma.
- An Jibge Jami’an Tsaro A Ko’ina Gabanin Ziyarar Da Buhari Zai Kai Jihar Legas
- Mutum Daya Ya Mutu Bayan Da Gini Ya Rufta Masa A Legas
Buhari ya sauka a filin sauka da tashin Jiragen sama na Murtala Muhammad da ke Legas da misalin karfe 3:30 na yammaci Litinin.
Gwamnan Jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, da tawagar Jami’an gamnatin Jihar ne suka tarbe shi yayin ziyarar aikin.
Daga bisani Shugaba Buhari ya kaddamar da katafaren aikin tashar Jirgin ruwa ta Lekki.
Sauran ayyukan da ya kaddamar sun hada da kamfanin sarrafa shinkafa a Imota da babbar hanya mai nisan kilomita 75 da ta tashi daga Eleko zuwa Epe, da aikin Jirgin kasa mai amfani da wutar lantarki zango na farko daga Mile 2 zuwa Marina da kuma cibiyar John Randle da aka yi domin bunkasa al’adun Yarbawa da inganta tarihi.
Shugaban zai kuma kaddamar da wani aiko na MRS Lubricant a yankin Apapa.
Gwamna Biodun Oyebanji na Jihar Ekiti da Dapo Abiodun na Jihar Ogun tare da tsoho gwamnan Jihar Ekiti, Dr. Kayode Fayemi da sauran jiga-jigan Jam’iyyar APC na cikin masu tarbar shugaban kasar yayin ziyarar aikin.