Tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya yi kakkausar suka dangane da wani ikirari da ke yawo a kafafen sada zumunta da ke nuna cewa ya bukaci magajinsa, Bola Ahmed Tinubu da ya daina binciken wasu tsoffin jami’an gwamnatinsa.
Da yake bayyana rahotannin a matsayin “labaran karya,” mai magana da yawun Buhari, Garba Shehu, a wata sanarwa da ya fitar, ya bukaci jama’a da kada su amince da irin wadannan bayanai marasa tushe.
- Mataimakin Shugaban Kungiyar Miyetti Allah Ya Bace
- NLC Za Ta Yi Zama Kan Hana Wasu Ma’aikatan Kano Albashi
A cewar Shehu, da gan-gan Buhari ya zabi ya ci mutuncinsa da kuma kaucewa jawo hankalinsa domin kaucewa duk wani abu da zai kawo wa sabuwar gwamnati cikas.
Da yake neman zaman kadaici, ya ce tun da farko tsohon shugaban ya koma mahaifarsa ta Daura amma ya ga an gagara samun kwanciyar hankali da ake bukata saboda yawan masu ziyara.
Sakamakon haka, Shehu ya ce tsohon shugaban ya koma wani wurin da aka kebe, inda yake fatan samun hutun da ya ke nema.
Shehu ya nanata muhimmancin yin watsi da wadannan ikirari marasa tushe, inda ya jaddada bukatar mayar da hankali kan bayanai na gaskiya da tabbatar da gaskiya.
A cewarsa, babban abin da tsohon shugaban kasar ya sa a gaba shi ne zaman lafiyarsa, tare da tabbatar da cewa gwamnatin Tinubu za ta yi aiki yadda ya kamata wajen cika alkawurran zaben da suka yi.
Ya ce “Idan za a yi imani da kafafen sadarwa na zamani, tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari yana rokon magajinsa, Bola Ahmed Tinubu da kada ya binciki wasu tsoffin jami’an gwamnatinsa.
“Karya ne, ba a tattauna wani abu makamacin haka ba. Wannan labarin karya ne, kuma ba wani abu ba. Alhamdulillahi ba kowa a dakin da suka hadu sai shugabannin biyu, don haka babu wanda ya isa ya kawo labarin tattaunawar tasu.
Duk mai yiwuwa, tsohon shugaban kasar yana fatan ya kasance a waje da abin da ya faru don kada ya dauke hankalin sabuwar gwamnati.
“Ya zabi ya koma gida Daura da fatan ya samu hutu ya kuma bai wa gwamnatin damar yin aikinta.
Ya ci gaba da cewa, “Ba abin da yake fatan samu face hutu, kuma gwamnatin Tinubu ta samu yanayi mai kyau na yin aiki kan cika alkawuran da suka dauka.”