Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya amince da nadin dan majalisar wakilai mai wakiltar karamar hukumar Kano Municipal mai barin gado, Honorabul (Dr) Sha’aban Sharada, a matsayin Babban Sakataren Zartarwar Hukumar kula da Almajirai da Yara Marasa zuwa Makaranta da kudirin kafa Hukumar ya samu sahalewa a 2023.
Sharada ya yi Digirinsa na farko a bangaren aikin aikin Jarida a Jami’ar Bayero ta Kano, sannan kuma ya yi Digiri na biyu a fannin harkokin kasuwanci daga Jami’ar Chichester da ke Birtaniya.
Sanarwar nadin ta fito daga Malam Garba Shehu, mataimaki na musamman ga shugaban kasa a ranar Lahadi 28, ga Mayun 2023.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp