Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya taya jagoran jam’iyyar APC na kasa kuma zababben shugaban kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu murnar cika shekaru 71 a duniya.
A cewar wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasa, Femi Adesina ya fitar, shugaban ya bi sahun iyalan zababben shugaban kasa, musamman ma uwargidansa, Sanata Oluremi Tinubu, abokan huldar kasuwanci da abokan siyasa wajen murnar kara shekara.
- Atiku Ba Zai Yi Ritaya Daga Siyasa Ba -Dino Melaye
- Dalilin Da Ya Sa Kotu Ta Dakatar Da Ayu Daga Shugabancin PDP
Shugaba Buhari ya yi amanna cewa soyayya, sada zumunci da karamcin Asiwaju ya kafa zai samar da tsarin shugabanci na gari da bunkasar tattalin arzikin kasa, da kuma karfafa jarin shugabannin da suka shude.
A yayin da zababben shugaban kasa ke shirin karbar ragamar shugabancin kasar nan, yana da shekaru 71, shugaban ya tabbatar da cewa siyasarsa tun daga shekarun baya, rawar da ya taka a siyasar jam’iyya, zaben Sanata kuma daga bisani ya zama gwamnan Jihar Legas, da kuma taka rawar gani wajen tafiyar da tsarin shugabanci.
Shugaba Buhari ya yi addu’ar Allah ya kara inganta lafiyar Asiwaju da ta iyalansa.