Jam’iyyar PDP ta nada Umar Damagum a matsayin shugaban riko na jam’iyyar na kasa.
Ya maye gurbin Iyorchia Ayu wanda shiyyarsa ta dakatar da shi a Jihar Benue.
- Buhari Ya Taya Tinubu Murnar Cika Shekara 71 A Duniya
- Kotun Tarayya Ta Kori Dan Majalisar Adamawa Daga Mukaminsa
Har zuwa nadin nasa Damagum shi ne mataimakin shugaban jam’iyyar PDP na kasa na shiyyar Arewa.
Talla
Debo Ologunagba, kakakin jam’iyyar PDP ne, ya bayyana hakan a ranar Talata a wani taron manema labarai a Abuja.
Nadin ya biyo bayan umarnin wata babbar kotu da ta hana Ayu bayyana kansa a matsayin shugaban jam’iyyar na kasa.
Talla