Yusuf Shuaibu" />

Buhari Ya Umurci Kara Wa Asibitin Koyarwa Na Jami’ar Maiduguri Tagomashi

Jami’ar Maiduguri

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa, akwai bukatar kashe makudan kudade wajen inganta harkokin lafiya, domin kaucewa bulluwar saban cututtuka.

Shugaba Buhari ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis, wajen kaddamar da ayyukan asibitin koyarwa na jami’ar Maiduguri da ke Jihar Borno. Haka kuma shugaban kasan ya bai wa shugaban ma’aikatan tarayya da ofishin kasafin umurnin kara yawan ma’aikata da kudade ga asibitin koyarwa na jami’ar Maiduguri.

A cikin bayanin wanda mai bai wa shugaban kasa shawara a bangaren yada labarai, Mista Femi Adesina ya rattaba hannu, shugaban kasa Buhari ya bayyana cewa, kara ma’aikan da kudade zai bunkasa ayyukan asibiti ta hanyoyn daban-daban.

A cikin ayyukan da shugaban kasa ya kaddamar a asibitin dai sun hada da sabon dakin tiyata da sabon dakin kwantar da majinyata da cibiyar bayar da bayanan kudade wanda gwamnan Jihar Borni, Farfesa Babagana Zulum ya gina.

Haka kuma shugaban kasa Buhari ya bude sabon wajen kwanan ma’aikatan asibitin koyarwan da gwamnatin tarayya ta gina. Shugaban kasan ya bayyana cewa, wannan ayyuka suna da matukar daraja wanda za a dunga gudanar da ragakafin cututtuka, ba za a iya kayyade irin anfannan da kasar nan za ta samu da wannan aiki musamman wajen yaki cutar Korona. Ya kara da cewa, kammala wannan aiki za yi matukar bunkasa harkokin lafiya a yankin Arewa Maso Gabas.

“Ya zama wajibi a kashe kudade masu yawa wajen dakile yaduwar cututtu a cikin kasar nan. Wannan gini zai yi matukar taimakawa wajen rage ayyukan ta’addanci a Jihar Borno,” in ji shi.

Shugaban kasa Buhari ya ci gaba da bayyana cewa, gwamnatin tarayya ta aiwatar da wannan aiki ne domin bunkasa harkokin lafiya a cikin kasar nan. Shugaban ya bukaci ‘yan kasa da su yi kokarin cin moriyar alfanun bunkasa harkokin lafiya da gwamnati take yi a halin yanzu. Shugabann kasa ya sha alwashin shirya wani tsari a asibitin koyarwa wanda zai samu hadin kai kasa da kasa  da kungiyoyi wadanda ba na gwamnati ba wajen bunkasa harkokin lafiya a cikin kasar nan.

A nasa jawabin, gwamnan Jihar Borno Farfesa Babagana Zulum ya gode wa gwamnatin tarayya wajen taimaka wa jihar domin magance harkokin lafiya, bisa gina wasu yankuna a wannan asibitin koyarwa mai albarka.

“An gudanar da aikin a dai-dai lokacin da ake bukatarsa bisa da la’akari da iren matsalolin lafiya da jihar take fuskanta sakamakon ayyukan ‘yan ta’adda. Domin haka, gwamnatin jihar za ta ci gaba da hada kai da asibitin koyarwa na jami’ai Maiduguri tare da bayar da horo na musamman ga ma’aikatan lafiya da kuma duk sauran abubuwan da suke bukata a wurin gwamnatin Jihar Borno.

“Mun yaba wa gwamnatin tarayya karkashin jagorancin shugaban kasa Buhari wajen bunkasa harkokin lafiya a jihar. Wannan asibitin koyarwar bai taba samun irin wannan aiki ba tun da aka kirkire shi,” in ji shi.

Gwamnan ya bayyana cewa, gwamnatin jihar tana shirye-shiryen gina asibitin koyarwa na jami’an jihar a nan gaba kadan.

An dai samu kyakkyawan sako daga bakin ministan harkokin lafiya, Dakta Osagie Ehanire da wakilan Hukumar Lafiya ta Duniya da kwamitin bayar da agajin gaggawa na kasa da kasa.

Exit mobile version