Fitaccen dan kasuwan nan da ke Zariya a Jihar Kaduna, Alhaji Umaru Shagalinku ya kai ziyarar ban girma ga Shugaban kasa, Muhammadu Buhar a fadar gwamna-tin tarayya da ke Abuja.
A lokacin wannan ziyarar, Alhaji Shagalinku ya bayyana cewa Shugaba Buhari ya yi iya bakin kokarinsa wajen kawar da matsalolin da suka addabi Nijeriya.
Ya yaba wa Shugaban Buhari na yadda a shekara takwas da suka gabata ya yi duk abin da ya dace domin kawo karshen matsalolin da suke addabar Nijeriya da ku-ma ‘yan Nijeriya baki daya.
Alhaji Shagalinku ya ci gaba da cewa duk wanda ya san halin da Nijeriya ke ciki kafin zaben 2015, ya san Shugaban Buhari ya dauki matakai da dama domin kawo karshen matsalolin tsaro da ke neman durkusar da Nijeriya da kuma ‘yan Nijeriya, amma matakan da Shugaba Buhari ya dauka ya kawo mafita masu yawan gaske ga ‘yan Nijeriya, musamman a jihohin arewa da matsalolin tsaron suka fi yin ka-mari a baya.
A cewar Shagalinku, wadannan matakai da ya fara samun mafita ga matsalolin tsaro yana fatan zai ci gaba da nuna wa zababben shugaban kasa, Alhaji Ahmed Bola Tunubu hanyoyin da ya tsaya a kansu, domin samun mafita na karshe ga matsalolin tsaron Nijeriya.
A game da bangaren noma kuma, Shagalinku ya ce an sami shekaru masu yawa da gwamnatocin da suka gabata ba su fito da tsare -tsaren da Shugaba Buhari ya fito da su ba, wanda duk wanda ke Nijeriya ya san an sami ci gaba a harkar noma, musamman a bangaren noman shinkafa da suka haifar da da mai ido ga manoman shinkafa a Nijeriya.
Ya shawarci sabon shugaban kasa mai jirar gado da ya dora daga wajen da Shugaban Buhari ya tsaya, domin al’ummar Nijeriya su dogara da shinkafar da ake nomawa a cikin gida.
Da yake mayar da jawabi, Shugaban Buhari ya fara da nuna jin dadinsa da wan-nan ziyara da Alhaji Umaru Shagalinku ya kai ma sa a fadar gwamnatin tarayya a Abuja.
Shugaba Buhari ya kuma yaba wa Alhaji Ummaru Shagalinku na yadda ya kwashe shekaru a harkar kasuwanci a sassan Nijeriya wanda ya samar wa dubban ‘yan Nijeriya sana’o’in dogaro da kai.