Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi ta’aziyyar rasuwar fitaccen dan siyasa kuma dan kasuwa, Alhaji Musa Musawa, wanda ya taba zama Sanata a baya, inda ya ce al’ummar kasar nan na cikin alhinin rashin wannan jigo na siyasa kuma dan Nijeriya na gaskiya.
Shugaba Buhari a cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Garba Shehu, ya fitar a ranar Laraba, ya bayyana marigayin a matsayin “babban dan siyasa ne mai fahimtar al’amuran siyasa.
“Ya yi rayuwar da ta dace, ya bar mu da abubuwan tunawa marasa adadi a matsayinsa na dan siyasa, dan kasuwa da kuma shugaban al’umma. Za mu yi kewarsa da yawa,” in ji Shugaban.
“Allah ya jikansa, ya bai wa iyalansa da gwamnati da al’ummar Jihar Katsina hakurin rashinsa,” in ji shugaba Buhari.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp