Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai halarci taron kolin shugabannin kasashen yankin tekun Guinea da za a gudanar a Accra babban birnin Kasar Ghana.
Cikin wani sako da fadar shugaban kasa ta wallafa a shafinta na Twitter, ta ce Buhari zai bar Nijeriya a ranar Talata 25 ga watan Afrilu domin halartar taron, wanda shugaban kasar Ghana Nana Akuffo-Ado zai jagoranta.
- Sin Na Ingiza Matakan Cin Gajiyar Basira Domin Bunkasa Ikon Mallakar Fasaha
- Tanzaniya Ta Yi Maraba Da Zuwan Tawagogin Yawon Shakatawa Na Sin
Ana sa ran shugaba Buhari zai gabatar da jawabi a taron wanda zai tattauna dabarun karfafa zaman lafiya da tsaro da yaki da masu aikata miyagun laifuka a gabar tekun yankunan kasashen.
Yayin halartar taron, Buhari zai samu rakiyar ministan harkokin kasashen waje, Mista Geoffrey Onyeama, da mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Babagana Monguno (mai ritaya), da daraktan hukumar tattara bayanan sirri ta kasa Ahmed Rufai Abubakar, da sauran jami’an gwamnatin tarayya.