Babban Bankin Nijeriya (CBN), ya aike da Naira biliyan 100 tare da buhun takin zamani miliyan 2.15 ga Ma’aikatar Aikin Noma da Samar da Abinci, domin rage radadin hauhawan farashin kayan abinci a daukacin fadin kasar nan.
Gwannan Babban Bankin, Olayemi Cardoso ne ya bayyana hakan, a yayin wata ganawa da ya yi da Babban Ministan Ma’aikatar Aikin Gona da Raya Karkara, Abubakar Kyari da kuma Karamin Ministan Maia’ikatar, Mohammad Abubakar; a shalkwatar ma’aiktar da ke Abuja.
- Nijeriya Ce Kan Gaba Wajen Lashe Kyaututtuka A Wasannin Kasashen Yammacin Afirika Na Bana
- Abincin Da Ya Kamata Mai Azumi Ya Ci Da Wanda Bai Kamata Ba
Cardoso ya ci gaba da cewa, yana da yakinin wannan taimako da aka yi wa wadannan manoma, zai rage radadin hauhawar farashin kayan abincin da wannan kasa ke ci gaba da fuskanta kwarai da gaske a halin yanzu.
Har ila yau, ya kara da cewa, bankin ya bayar da wannan taimako ne, domin habaka noma tare da daidaita farashin kayan abinci a fannin aikin noma a fadin Nijeriya baki-daya.
Shi ma a nasa bangaren, Abubukar yabawa ya yi da bayar da wannan taimako, inda ya sanar da cewa; wannan hadaka za ta taimaka kwarai da gaske wajen kara samar da wadataccen abinci a fadin wannan kasa.
Haka zalika, ya sanar da cewa; hauhawar farashin kayan abinci na ci gaba da zama wata babbar barazana a dukkanin fadin wannan kasa, amma a halin da ake ciki yanzu Ma’aikatar Aikin Noma da Samar da Wadataccen Abinci, na ci gaba da yin nata kokarin wajen lalubo mafita tare da magance wannan matsala da ake ciki.
Shi kuwa a nasa bangaren Ministan Gona, Abubakar Kyari, ya sanar da cewa; gwamnatin tarayya na da yakinin cewa, ko shakka babu; wannan dauki zai yi matukar taimakawa wajen daidaita farashin kayan abinci a kafatanin lungu da sako na fadin wannan kasa.