Daga Abubakar Abdullahi, Lafia
An bukaci ‘yan kasuwa a Jihar Nasarawa da su sassauta farashin kayayyakinsu ga mabukata domin kawo saukin matsanancin hali da al’umma ke ciki. Shugaban ‘yan kasuwar jihar, Alhaji Shammasu Dantsoho ne ya mika wannan bukatar jim kadan bayan kammala bikin rantsar da shi a matsayin shugaban kungiyar karo na biyu da sauran sabbin jami’an kungiyar a Lafia babban jihar.
Ya ce, mambobin kungiyar suna da rawar da za su taka wajen tabbattar da daidaito ga tattalin arzikin kasar nan ta hanyar daina boye da guje wa tsawwala farashin kayyayyaki. Ya ci gaba da cewa, kamata ya yi ‘yan kasuwa su rika kasancewa masu gaskiya da adalci cikin harkokinsu ta hanyar yin la’akari da halin da ‘yan Nijeriya ke ciki domin rage musu radadin yanayin.
Da yake yaba wa mambobin kungiyar kan goyon baya da suka ba shi na sake zabar sa a matsayin shugaban kungiyarsu, Dantsoho ya ce zai bai wa marada kunya dangane da amanar da suka damka masa. Yana mai cewa, zai kasance mai himma wajen sauke duk nauyin da aka dora masa.
Da yake jawabi a wajen bikin rantsarwar mai martaba Sarkin Lafia wanda ya samu wakilcin Tafarkin Lafia Alhaji Aliyu Ibrahim, ya shawarci sabbin shugabanin ‘yan kasuwar jihar da su kasance masu sadaukar da kai wajen tafiyar da harkokin kungiyar domin samar da cigaba. Sauran sabbin shugabannin da suka saba layar kama aiki sun hada da; Alhaji Baba Ali a matsayin mataimakin shugaba da Ibrahim Tanko a matsayin sakatare da dai sauransu.