• English
  • Business News
Saturday, September 6, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Bukatar Inganta Rayuwar Daurarru A Gidajen Yarin Kasar Nan

by Bello Hamza and Sulaiman
4 months ago
in Ra'ayinmu
0
Daurarru
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Biyo bayan rahotannin da aka wallafa na kwanan baya cewa, masu zaman Jarun a Gidan Gyaran hali na fadin kasar nan, suna fama da karancin abinci, musamman mai gina jiki, hakan ya nuna a zahairi, kan mayar da hankali da ya waba mahukuntan kasar su dauka, a kan irin kayan da ake amfani da su, a Gidajen.

 

Kazalika, rahotannin sun kuma bayyana irin zargin rashin adalaci, tauye hakkin masu zaman Jarun da kuma irin matsanta masu da ake yi a Gidajen na Gyaran hali, saboda kawai, sun tsinci kansu a Gidajen kan laifukan da suka aikata.

  • Ranar Ma’aikata: Gwamnan Kano Ya Biya Basussukan Fansho, Ya ƙirƙiro Sabbin Ma’aikatu
  • Kasar Sin Ta Yi Kiran Kawar Da Makaman Nukiliya Bisa Tsarin Tsaro Na Bai Daya

Biyo bayan zargin da ake yiwa Hukumar Kula da Gidan Gyaran Hali ta Kasa, na barin masu zaman Gidan Hari a cikin halin yunwa,, wanda hakan ya janyo mutuwar wasu daga cikinsu masu zaman a gidan Kason da kuma zargin cin hanci da rashawa, a watan Satumbar shekarar 2024, Ministan Kula da Harkokin Cikin Gida Olubunmi Tunji-Ojo ya kama kwamiti mai zaman kansa da zai gudanar da bincike kan zargin.

Dakta Uju Agomoh Sakatariyar Kwamitin a taron manema labarai a watan Marisa din 2025 ya sheda masu cewa, binciken da Kwamtin ya gudanar kan wannan batun, ya gano cewa, akasarin Gidajen Gidan Gyaran Hali da ke a fadin kasar masu zaman Jarun din, na mutuwa saboda rashin ba su abinci yadda ya kamata da kuma karancin abinci, a Gidajen na Gyaran Hali.

Labarai Masu Nasaba

A Daina Gaggawar Murnar Samun Nasara Kan Ta’addanci A Nijeriya

Bukatar Hukunta Masu Jagorantar Kashe-kashe A Nijeriya

A cewarta, Kwamtin a watan Fabirairun 2025, ya kai ziyarar da Kwamitin ya kai a daya daga cikin Gidajen Gyaran Halin, inda ya gano cewa, Hukumar Kula da Gidan Gyran Hali ta Kasar, ba ta tanadarwa masu zaman Jarun abincin da aka aminta za akalla na mako daya ba.

Wannan batun ya nuna a zahii na irin dimbin cinkoson da ake da shi, a Gidajen Gyaran Halin kasar, mussamn duba da cewa, Gidan na nan yadda suke kamar jiya iyu, tun bayan samun ‘yancin Nijeriya daga Turwan mulkin mallaka.

Ga masu kai ziyara Gidajen, babu abinda suke gani, illa yanayi na irin lalacewar da Gidajen ke ciki, musamman duba da rashin tanadar kayan duba lafiyar masu zaman Jarun da yanayin lalacewar da Gidajen suke cikin, wanda hakan ya nuna cewa, ana kawai cin zarafin tsarin Shari;ar kasar ne, musamman ganin yadda ake ci gaba da take ‘yancin Bil’adama.

Idan za a iya tunawa Kwamtin Majalisar Dattawa da ke sanya ido kan kula da harkokin cikin gida, a watan Okutobar 2021, ya amince da kara yawan abincin da ake ciyar da mazu zaman Jarun na kowacce rana, daga Naira 450 zuwa Naira 1, 000.

Bugu da kari, a kasafin kudi na 2023, jami’an Hukumar Kula da Gidan Gyran Hali ta Kasa, sun bayyana a gaban Kwamtin Majalisar Dattawa da ke sanya ido kan kula da harkokin cikin gida, domin kare kasafin Naira 750 na ciyar da masu zaman Jarun din ako wacce rana, inda Kwamitin ya ce, Naira 750 ta yi kadan, ya kara kudin zuwa Naira 1, 000, duba da cewa, haka bisa ka’idar yanayin tattalin arzikin Gidan Gyaran Hali na Kasar.

Bayan tsohon Shugaban Gidan Gyaran Halin na kasa ya sanar da karin a hukumnce, masu zaman Jarun din a daukacin Gidan Gyaran Halin na kasa , sun bayyana farin cikinsu na ganin za a kara masu yawan abincin da ake ciyar da su, kai tsaye.

Bayan watannin bakwai, sai murnar su, ta koma ciki, biyo bayan rahoton da aka wallafa ya nuna cewa, ba a yi wani kari, kan kudin ciyar da masu zaman Gidan Jarun din ba, duk da ikirarin da karin da aka ce, Gwamnatin Taryya, ta amince da yin karin.,

Kazalika, idan za a iya tunawa aranar 31 na watan Yulin 2019, Hukumar Kula da Gidan Gyran Hali ta Kasa ta kirkiro da doka a 20219 wadda ta cike gurbin dokar Hukumar ta 2004, wana ta .yi hakan ne, saboda matsalolin da ake da su a cikin tsohuwar dokarta ta P 29 ta 1972.

Manufar dokar ta Hukumar ta 2019, shi ne, domin a sabunta tsarin Gidajen Gyaran Halin na Kasa, yadda za su kasance, daidai da irn na fadin duniya, musamman kan kare ‘yancin Bil Adama, gyaran Gidajen da bayar da kulawar da ta dace, ga masu zaman Jarun na kasar.

Dokar ta ta 2019 ta nuna banbacin da ake da shi, na tafiyar da Gidajen Gyaran Kasar, da suka hada da, manufofi, gudanar da ayyuka, bayar da kariya, wanzar da matakai da sauransu, wadanda suka sha banban da tsari irin na baya.

Sashi na 2 1 a cikin Baka da A a cikin Baka, ya bai wa Hukumar bin ka’ida ta kasa da kasa, ta kare ‘yancin Bil Adama.

An kafa tsarin tafiyar da Gidan Gyaran Halin kasar ne, wanda ya yi daidai na duniya kan tsari uku da suka hada da, dokar Final Kod da dokokin kasa na 81 ta 1990 da kuma dokar aikata manayn laifuka ta 80, ta kasa ta 1990 sai kuma dokar Shari’a ta jihohi 12 na kasar nan, a wancan lokacin.

Kafa wannan dokar ya nuna cewa, Hukumar Gidan Gyaran Halin Kasar, ta nuna cewa, wata Cibiya ce, da ya wajaba ta rinka saita matasan da suka aikata laifuka, wanda hakan zai sanya, a samu ragin masu aikata laifuka, a cikin alumma.

Nijeriya na da adadin Gidajen Gyaran Hali 256, wanda ya zuwa ranar 3 na watan Maris din 2025, jimlar masu zaman Jarun, cikinsu har da wadanda suke ci gaba da fuskantar Shari’a, sun kai 80,183, inda kuma aka ruwaito, yawan jami’an sun kai 50,153.

Daga cikin wannan adadin, akwai jimlar masu zaman Jarun 3,688 da a yanzu, suke jiran hukuncin rataya a daukacin Gidajen Gyaran Hali, na fadin kasar, wanda hakan yawan ya kai kaso 136.7, inda hakan ya kara haifar da karancin kudaden da za a tafiyar da Gidajen da kuma rashin kayan aiki.

Tabbas, Gidajen na ci gaba da fuskantar cunkos da tauyewa ‘yan Jarun hakkinsu, wanda hakan, ke haddasa ake yawan samun wasu masu zaman Jarun, ke fasa Gidajen su arce.

Jinkirin da ake samu na yanke hukunci da Kotuna ba su yi, musamman yanke hukuncin da ya shafi kisa, hakan na kara janyo samun cunkoso, a Gidajen.

A lokuta da ban da ban, Gwamnatin Tarayya ta sha nuna sha yin alkarin samar da sauye-sauyen a tsarin Shari’a, musamman a bangaren aikata manyan laifuka.

Sai dai, abin takaici, duk da shawarwarin da Hukumomin da Kwamitocin na bangaren Fadar Shugaban kasa har da wadanda suka shude, suka bayar na samar da sauye-sauye a bangaren Shari’a, shawarwain sun koma tamkar Tatsuniyar Gida da Kaki.

Dokar Hukumar ta 2019 ta fuskanci kalubale, wajen wanzar da ita ciki har da karancin kudi na tafiyar da Gidajen, rashin kayan aiki da kuma kare lafiyar jami’an Gidajen.

Tun a 2010, Nijeriya ta sha fuskantar fasa Gidajen Gyran Hali, wanda hakan ya sanya, arcewar, masu zaman Jarun da suka kai 7,000, ciki har da ‘yan ta’adda.

Wasu daga cikin fitattun fasa Gidajen shi ne, na Kuje a watan Yulin 2022, wanda masu zaman Jarun guda 879 suka tsere, ciki har da ‘yan ta’adda 64.

Akasari dai, an alakanta cin hanci da rasahawa, rashin samun bayanan sirri, rashin daukar matakan da suka dace na tsaro, a matsayin manyan matsalolin da Gidajen Gidajn Gyran Halin Kasar, ke ci gaba da fuskanta.

Damuwar mu a nan ita ce, duba da kalubalen da kayan aiki na Gidajen Gyaran Halin Kasar ke ke ci gaba da fuskanta, zai yi wuya a inganta zamantakewar masu zaman Jarun, kamar yadda dokar da ta kafa Gidan ta tanada.

A ra’ayinmu, matukar ba a samar da kayan aikin da suka da ce, ba da kuma smar da kyakyawan yanayin da ya kamata, sauye-sauyen da ake tunanin samar wa a Gidajen, abin zai zama ne tamkar a furtawa, amma ba cika wa.

Ya zama wajbi Gwamnati ta fitar da kudi da kuma bayar da goyon baya wajen gyara tsarin tafiyar da Gidajen, musamman domin inganata rayuwar masu zaman Jarun.

Lalubo da mafita kan wadannan kalubalen abu ne da zai kasance ba na dare daya ba, musamman batun rage cunkoso, inganta rayuwar masu zaman Jarun, kara karfafa shirye-shiyen yiwa Gidajen kwaskwarima da kuma kara horas da jami’an Gidajen Gyaran Halin Kasar.

Wannan dai ya hada da kara gina wasu Gidajen Gyaraaan Hali, musamman domin a rage cunkos da kuma tabbatar da an samar da ababen more rayuwa.


Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

ShareTweetSendShare
Previous Post

Shimfida A Kan Aikin Hajji Da Bayani A Kan Mikatin Da Manzon Allah (SAW) Ya Sa

Next Post

An Cafke Saurayi Bisa Zargin Yi Wa ‘Yar Budurwarsa Fyade A Bauchi

Related

An Damke Basarake Da Wasu Mutum 10 Bisa Zargin Hada Baki Da ‘Yan Bindiga A Kudancin Kaduna
Ra'ayinmu

A Daina Gaggawar Murnar Samun Nasara Kan Ta’addanci A Nijeriya

1 week ago
Ra'ayinmu

Bukatar Hukunta Masu Jagorantar Kashe-kashe A Nijeriya

1 month ago
Yadda Rashin Isassun Malaman Turanci Da Lissafi Ke Shafar Ingancin Ilimi A Nijeriya (3)
Ra'ayinmu

Akwai Bukatar Daina Cin Zarafin Malaman Makaranta

2 months ago
Bikin Ranar Muhalli Ta Duniya: Akwai Babban Aiki A Gaban Nijeriya
Ra'ayinmu

Bikin Ranar Muhalli Ta Duniya: Akwai Babban Aiki A Gaban Nijeriya

3 months ago
Bukatar Kara Yawan Masu Fitowa Kada Kuri’a A Zabuka Nan Gaba
Ra'ayinmu

Bukatar Kara Yawan Masu Fitowa Kada Kuri’a A Zabuka Nan Gaba

3 months ago
Wajibi A Mayar Da Hankali Kan ‘Yancin Yara
Ra'ayinmu

Wajibi A Mayar Da Hankali Kan ‘Yancin Yara

3 months ago
Next Post
Zargin Yaudara: Wani Tela Ya Kashe Tsohuwar Masoyiyarsa A Kaduna

An Cafke Saurayi Bisa Zargin Yi Wa 'Yar Budurwarsa Fyade A Bauchi

LABARAI MASU NASABA

Sashen Cinikayyar Bayar Da Hidima Na Sin Ya Bunkasa Cikin Watanni Bakwai Na Farkon Shekarar Bana

Sashen Cinikayyar Bayar Da Hidima Na Sin Ya Bunkasa Cikin Watanni Bakwai Na Farkon Shekarar Bana

September 5, 2025
Kasar Sin Ta Yi Nasarar Harba Wani Sabon Tauraron Dan Adam

Kasar Sin Ta Yi Nasarar Harba Wani Sabon Tauraron Dan Adam

September 5, 2025
Jami’an Kasa Da Kasa Sun Yi Matukar Jinjinawa Jawabin Xi Jinping

Jami’an Kasa Da Kasa Sun Yi Matukar Jinjinawa Jawabin Xi Jinping

September 5, 2025
Za Mu Riƙe Wa Minista Tijjani Muƙaminsa Bayan Hamɓarar Da Tinubu A 2027 – El-Rufai 

Ana Ci Gaba Da Caccakar El-rufai Kan Kalamansa Game Da Tsaron Kasa

September 5, 2025
Kasar Sin Ta Kasance Muhimmin Karfi Dake Tabbatar Da Zaman Lafiya Da Ci Gaban Duniya

Kasar Sin Ta Kasance Muhimmin Karfi Dake Tabbatar Da Zaman Lafiya Da Ci Gaban Duniya

September 5, 2025
Yadda Al’ummar Da Ke Zaune Da ‘Yan Bindiga Ke Rayuwa A Zamfara

Duk Da Sulhu Da ‘Yan Bindiga Ana Ci Gaba Da Kai Hare-hare Wasu Yankunan Zamfara

September 5, 2025
Antonio Guterres Ya Yi Maraba Da Shawarar Inganta Jagorancin Duniya Da Sin Ta Gabatar

Antonio Guterres Ya Yi Maraba Da Shawarar Inganta Jagorancin Duniya Da Sin Ta Gabatar

September 5, 2025
Ban Yi Kuskure Wajen Zaben Kashim A Matsayin Mataimaki Ba – Tinubu

Ban Yi Kuskure Wajen Zaben Kashim A Matsayin Mataimaki Ba – Tinubu

September 5, 2025
Xi Ya Aike Da Wasikar Taya Murna Ga Bikin Baje Kolin Masana’antun Kirkirarriyar Basira

Xi Ya Aike Da Wasikar Taya Murna Ga Bikin Baje Kolin Masana’antun Kirkirarriyar Basira

September 5, 2025
Mahara Sun Kai Hari Banki A Kogi

’Yansanda Sun Kama Masu Garkuwa Da Mutane 2 Da Wasu 156 Kan Aikata Laifuka A Jigawa

September 5, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.