Kamar yadda muka sani yara wasu amana ce da Ubangiji ya rataya mana a wuyanmu. A rayuwa mun sani cewa duk abin da aka kira shi da amana to fa wannan abu ya kasance wani nauyi ne me wahalar saukewa.
A wannan zamani da muke ciki haihuwa ta kasance abu mafi sauki ana yawan hayayyafa wanda hakan ba laifi bane, amma kuma abin tambayar a nan shi ne, iyaye na iya sauke nauyi da kuma amanar da aka basu?.
- Shugaban Kasar Sin Ya Yi Tattaki Zuwa Wani Karamin Kauyen Da Bala’in Ambaliyar Ruwa Ya Shafa
- Tinubu Ya Amince Da Gina Gidaje 1,000 A Jihohin Arewa 7 – Shettima
In muka duba za mu ga cewa ‘ya’ya a wannan zamani sun kasance abin banzatarwa abin sakaci wanda hakan kuskure ne.
Uwargida ki sani cewa ke da mahaifin wadannan yara hakkine mai girma da ya rataya a wuyanku.
Da yawa za mu ga cewa iyaye ba sa iya zaman minti biyar da ‘ya’yansu, sai ka ga suna hantararsu, su fita waje ita kawai damuwarta su je waje su yi wasa, ba ta damu da in sun fita waye za su hadu da shi ba, wadanne irin abokai za su gamu da su , wane irin kuma wasa za su yi ba, duk wannan bai damu iyayen wannan zamani ba.
Yawanci za mu ga cewa yaran wannan zamani rayuwar su rabi a waje suke yi, maimakon uwa tun da ita ke wuni da su a gida ta kasance manne da ‘ya’yanta ta zauna kusa da su ta ji damuwarsu, a’a ita dai kawai su fita waje su je wasa.
Me ya sa yawan fyade da sace-sace ya yi yawa saboda rashin jan yaro a jiki ne, da yawa za ka ga an yi wa yarinya fyade amma saboda rashin kula irin na uwa sai ka ga ta kwana ta wuni ba a lura ba har sai ta kai ga ko yarinyar ta zo fitsari ko kuma an zo mata wanka a wannan lokacin ne wai za a gane halin da take ciki.
‘Ya’ya maza,
Idan kina da da namiji uwargida kar ki kasance mai kora shi ki ce wai jeka waje ko kuma jeka gidan su wane ku yi wasa to su wadanda kika turawa dan ai suma hakuri suka yi da gidansu suka zauna har kika yi sha’awar tura danki.
Uwargida kasance mai yawan tunasar da yaranki game da lamarin duniya, kar ki kasance ke komai sai dai babansu ke ma dan azkar din nan, dan yadda ake koyon Sallah nuna wa yaro, kar ki kau da kai ki ce wai ai bari babansa ya dawo.
Kasance mai jan ‘ya’yanki a jiki ta wannan hanyar ne za ki san meye damuwarsu, sannan kuma meye suke so da kuma irin rayuwar da suke ciki a makarantunsu.
Kalmar shugabanci na daga sanannu kuma wasu shahararrun kalmomi da aka saba ji dare da rana, kaka da kakanni. Kalma ce mai saukin ji, ko fada, sai dai wajen aikatata a aikace, lamarinta kan gagari kundila.
A Nijeriyar jiya da yau, kowa na da burin a yabi nasa, koko shi a kankin-kansa a yaba masa, yayinda suke bisa kujerar shugabanci, ko bayan saukarsu. Kowace kabila yau cikin Nijeriya, na da irin nasu gwarzayen shugabannin da kwata-kwata tarihi bai da karfin gaban da zai sanya sunayensu cikin kwandon shara!!!.
Ba ya ga mabanbantan bangarori da kabilun Kasar da kowa cikinsu gwani ne wajen kare irin shugabanninsu na-dauri, haka ma abin yake ga mabiya addinai iri daban-daban a Kasar. Sai dai ga dukkan alamu, kabilun wannan Kasa da mabiya addinansu na wannan lokaci, ba a shirye ne suke ba, wajen bin sawun magabatansu na kwarai. A kullum, sai dai kawai a buge ne da yabon magabata daga tsoffin jagorori ko a ce shugabannin Kasar. Kawai, a na furtawa ne a baki, kuma ba a shirye ake na aikata irin kyawawan aiyukan wadancan shugabannin da ake ta kan kururuta aiyukansu dare da rana ba.
Ta Yaya Yabon Fatar-baki Zai Haifar Da Shugabanci Nagari A Kasa?
Sama da kashi casa’in (90%) na kabilu da mabiya addinai da ke raye cikin Nijeriyar yau, ba su damu da samar da shugabanci nagari cikin Kasar ba a aikace, sai dai kawai a mafarkance. Za a iya gane hakan ne ta hanyar nazartar aiyukansu hada da furuce-furucensu!!!.
Da daman mutane ba sa zabar wani kansila da zuciya guda, sai don ya dare kujerar ne ya biya musu bukatunsu na daidaiku. Haka Ciyaman, haka “yan Majalisun jiha, haka Gwamna, haka” yan Majalisun taraiya, haka ma kujerar Shugaban Kasa. A tunanin akasarin mutane a yau, bukatunsu na daidaiku, shi ne mazaba, shi ne karamar hukuma, shi ne jiha, kai, kacokan ma shi ne Nijeriya. Saboda haka, wajen samun biyan wadancan bukatu, komai na iya faruwa, a duk sa’adda wani lamari ya tasamma zame musu wani tsaiko, a kan hanyarsu ta cimma irin wadancan bukatu ko muradai, sawa’un, masu kyau ne ko gurbatattu.
Irin wadancan halaye na bukatar-kai linzami, shi ne mafi munin ta’adar da ke kange kowace irin nahiya ko kasa a Duniya daga samun ci gaba. Da Ciyaman ba shi da hali irin na bukatar-kai linzami, da tuntuni dubban daruruwan jama’ar karamar hukumarsa sun jima da tsallake mummunan kangin wahalar rayuwar da suke ciki tsundum a yau. Ta fuskar sama musu aiyukan-yi na hakika tare da tallafarsu zuwa ga samun jari da sauran samun damarmaki a rayuwa. Sai suka gwammace su hade kai da baki da gwamna da sauran “yan majalisu, wajen yin wa-kaci ka-tashi da dimbin miliyoyin kudaden da aka rantsar da shi cewa zai kare su. Amma sai aka wayigari son-kai da son-zuciya sun maishe su rakuma da akala. Babu aiyukan-yi kwarara a kananan hukumomin nasu, sun gaza yi wa gwamna tsayuwar-gwamin-jaki wajen kare muradun al’umarsu, amma a duk inda aka je aka zo, sai a samu cewa talakawa raunane ke dandana kudarsu dare da rana, amma ba Ciyaman ba, kuma ba Gwamna ba. Duk inda gwamnoni za su kai ga rike kudaden majalisun kananan hukumomi, ciyaman ya fi karfin ci da sha, mallakar gida, harkar lafiya, duka da shi da iyalansa. Ke nan, da gwamna da ciyaman, likkafar rayuwarsu ta ci gaba, sauran mutane ne aka yasar a tasha.
Tuntuni cikin wannan Kasa, jagoranci da shugabancin da ake gudanarwa a matakan jihohi da can matakin gwamnatin taraiya suka gurbace. Gwamnoni nawa ne a Kasar, bayan sun zubar da hawaye game da aiyukan “yan ta’adda a jihohinsu, aka ji, ko aka ga, sun sauka daga kan kujerunsu, don ba da dama ga wasu mutanen da za su iya maye gurbinsu tare da murkushe tarnakin ” yan ta’addar sama da su?. Kawai sai dai a ga gwamna na zub da hawaye tare da damke kujerersa kamkam tamkar nonon uwa. Babu shakka akwai duk wani nau’i na yaudara cikin wannan surkullen gajiyawa da gwamnoni ke yi dare da rana. Sannan, a duka cikin kudanci da arewacin Kasar akwai irin wadancan gwamnoni, wadanda suka yi likimo bisa kujerun mulkin tamkar na gado.
Ba gwamna kawai ba, hatta akasarin kwamishinoni da ke karkashin gwamnoni, sun fi mayar da hankali ne, ta yaya lalitarsu za ta cika ta batse?. Gwamnoni sun aza su bisa kujerunsu ne kadai, don su dafa musu wajen samar da shugabanci nagari a matakan jihohi, sai dai, tsawon lokaci kwalliya ta gaza biyan kudin sabulu!!!. A kullum kalaman da ke fitowa daga bakunan kwamishinonin, ba ya wuce cewa, mai girma gwamna fa ya ki sakin kudade ga masana’antun nasu. Duk da haka, daga lokacin da wata jam’iyyar adawa ta amshe mulkin jihar, sai a ji sama da miliyan dubu na naira, sun yi batan-dabo daga ofishin Hon. Kwamishina.
An dauki lokaci, ba tare da samun gudanar da shugabanci abin koyi daga jerin irin wadancan kwamishinoni. Idan gwamna ya nada ka aiki, sai ya hana ka kudaden gudanar da aiyuka, mene ne alfanun ci gaba da aiki a karkashinsa ga al’umar jiha?. Sai dai da yake, a na rabar gwamna ne don cimma bukatar kashi-kai linzami, sai Mr Kwamishina ya ci gaba da nanikar gwamna, ko babu komai, ba zai rasa ci da sha da sauran bukatun rayuwa har zuwa saukarsu daga kujerun mulki. Ke nan, akwai yawo da hankali a ji kwamishina na cewa, gwamna ya ki sakin kayan aiki. Uzurin rashin sakin kayan aiki, ka iya karbuwa, muddin gwamnatin na kasa da Watanni shida (6) ne bisa karagar mulki. Sabanin haka akwai ayar tambaya (?)
Babu shakka, mu na wani lokaci ne da mutum zai hanga gabas da yamma kudu da arewacin Nijeriya, sai ya gajiya wajen samun sahihan mutanen da shugabanci na adalci ke maraba da su. Sai lamuran ke neman zama tamkar kowane gauta… tattare da manyan kabilun Kasar uku, gurbatattun shugabannin cikinsu, sun ninka nagartattun cikinsu sau malala gashin tinkiya. Alhali, a can baya, kowannensu na da sahihan mutane nagartattu, abin koyi, wajen iya tafiyar da shugabancin da yai hannun riga da hadama da zalama, sabanin yanzu.
Sai aka wayigari, hadamammun shugabanni hatta a kungiyar masu sana’ar shayi ko sayar da masara, sune a kullum aka tsaya zabe ke lashewa, su ke da kudaden badawa a matsayin cin-hanci, don su ci gaba da dauwama bisa kujerun shugabancin da babu fansho ko giratuti tattare da su. Son zuciya da zarmewar, game da mugun son shugabanci tare da rashin ba da hakkinsa, lamarin ya wuce batun kungiyoyin Siyasa da masu sayar da Shayi, hatta cikin rigar Addini ma lamura sun yi gurbatar da ake zare manyan bindigogi a na kashe kai, da sunan a na bisa tafarki. Me ke faruwa da batun masu ikirarin jihadi a gabashin arewacin wannan Kasa?
Me ke faruwa a Maidugiri da Yobe a yau? Da yawan mabiyansu na yin ribas, tare da mika wuya ga rundunar Sojojin Nijeriya, tamkar irin yadda manyan “yan Siyasa da kanana ke yin hijirar canja jam’iyya, daga A zuwa B, ko daga C zuwa D. Suma rukunin “yan ta’adda ba a bar su ba a baya, wajen gudanarwa da mutanensu gurbataccen shugabanci, hakan ke zama silar yi wa jagororinsu gadar zare, tare da rufta su ciki, irin yadda Sojojin Niger suka yi wa shugaba Baazou!
Ta Ina Ne Za A Gyatta Lamarin Shugabancin?
Daga kan shugaban Kasa ne za a faro gyaran, ko kuwa daga kan kujerar Kansila?. Koko daga limaman Masallatai ko na Coci-coci?. Daga jagororin Kotu kotu ne za a fara gyaran, koko daga kamfanin wutar lantarki?. Daga jagororin tsaro ne gyaran zai fara, koko daga shugabannin tasha ko na kasuwanni?. Koko uwa uba, za a faro gyaran ne daga bangaren jagorancin Miji da Mata a gida?. Sai aka wayigari a Nijeriyar yau, mutum ba shi iya bugun kirji ya yi nuni zuwa ga nagartaccen shugabanci daga jerin rukunin wadannan mutane! Ta yaya ne za a ga daidai?. Ta kai ta kawo, hatta a shugabancin manyan makarantun ilmi na Kasar, Farfesa kan yi rub da ciki bisa lalitar tsangaya. Sune fa ke kyankyashe sabbin zubin shugabannin Kasar a nan gaba, amma sai ga laya na gardamar kin kyawon rufi.
Sai ga mutane an bazama daji, an kasa gano bakin-zaren. Wace jam’iyyar siyasa ce a yau cikin Kasar ba ta da gurbatattun shugabanni? Idan ba ka sani ba, to jira lokaci Malam Zurke. Na daga rashin sanin alkiblar sahihan jagorori, mutum kan dauki lokaci tare da wanke ko tsarkake wani shugaba nasa, ba abin mamaki ne ba, zuwa wani lokaci, a ji shi, yana antaya bakaken kalamai ga wannan tsohon jagora nasa!. Hatta shugabancin kungiyar Kwadago ta Kasa, NLC, bai subuce daga samun zarge-zarge ba. A lokaci guda, suma za a same su ne suna masu ta-da-jijiyar wuya ga wani shugabanci na daban, tare da wanke nasu da ruwan alkausara.
Bukatar Komawa Bisa Sirdi
Na’am, gyaruwar wani shugabanci kan zama silar gyaruwar wasu rukunin shugabancin. Gyaruwar shugabancin malaman addini da na masu mulki, na iya zama a sawun gaba, wajen muhimmanci, sai dai hatta suma, shugabancin gida, na tsakanin miji da mata, kan iya samar da kyakkyawan sakamako ga wadannan shugabanci biyu (na masu mulki da na maluma). Kuma gurbacewarsa kan iya taka muhimmiyar rawa wajen gurbacewarsu.
Yayinda aka tasamma samar da nagartaccen shugabanci a kasa, kowane nau’in shugabanci, daga kowane rukunin jama’a, kan iya taka muhimmiyar rawa wajen gyaruwar lamuran shugabancin a kowane mataki. Rashin gyaruwar shugabanci a ban kasa, komawa karkashin kasa kan zama mafi kyawon maslaha a wasu lokutan.
Wargajewar mangalar shugabanci a matakin karamar hukuma, kan tilasa Ciyaman nada gammon daukar mafi tarin kalubale sama da kowa a mazabar. Gwamna a jiha, dole ya kalli kansa a matsayin babba juji sama da kowa cikin jihar. A matakin kasa kuwa, shugaban kasa ne zai rungumi mafi tarin korafe-korafen jama’a sama da kowa a kaf fadin Kasar.
Shugabancin masu mulki ne ke da iko na yankan shakku, wajen tursasa wasu karkatattun shugabanci zuwa ga mikewa sama da kowa. Saboda haka, gyaruwarsu kan zama wani abu mai alfanu sama da akasarin nau’ikan shugabancin da ke wanzuwa a tsakankanin al’umar Duniya.
Idan idanun shugabanci ya dode, tunaninsa kacokan ya koma ga mene ne zai yi habzi da shi daga al’uma, sai a saurari gurbacewar lamura a Kasa bakidaya.
Yayinda shugabanci ya zamto za a dankarawa mutane ne, ko suna so, ko ba sa so, sai a jiraci yin kwalli da abubuwa na kaico.
Idan jahilci yai wa shugabanci kawanya, kwaba da mushen tunani ne a kullum zai rika kwararowa daga fadar shugabanni.
Idan batun shugabanci ya koma tuwona maina, za a dauki tsawon lokaci ne cikin kangin bauta da kaskanci ba tare da samun mafita nan da nan ba.
Idan sha’anin shugabanci ya koma tamkar wata hajar saidawa, sai a jima ne cikin takaici da da-na-sani a rayuwa.
Idan harkar shugabanci ta koma hannun “yan-dagaji, baragada da shirbici zai mamaye lamuran daidaikun mutane da kuma Kasa bakidaya.
Idan sha’anin samar da shugabanci ya zamto tamkar “yar-canke a tsakanin mutane, lamarin ka juye ne zuwa ga yanayin sanya kunama a wando, za a wahala ne iya wahala.
Idan jama’ar Kasa suka riki harkar shugabanci, riko irin na sakainar kashi, hakan ka iya bayuwa zuwa ga fargar jaji ga wannan al’uma.
Idan aka watsar da yin hannunka mai sanda ga shugabanci, a ko da yaushe tusa na iya kurewa bodari!!!.