Leadership News Hausa
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership News Hausa
No Result
View All Result

Bukatar Rage Yawan Yaran Da Basu Zuwa Makaranta

by
11 months ago
in MUKALA
4 min read
Bukatar Rage Yawan Yaran Da Basu Zuwa Makaranta
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram
ADVERTISEMENT

A kullum idan na duba yadda yara ke gararanba a kan titi daga safe har zuwa yamma, sai inga kamar babu fata akan yaran da za su zo nan gaba, musamman a nan.

Abun da aka saba ko kuma abun da yakamata shi ne kullum da zarar yaro ya tsahi da safe bayan ya yi sallah ya karya sai ya wuce Makaranta.

Duk mutumin dake zaune a musamman wanda ke zama a kauyaku, yasan yankin na fama da matsalar zuwa Makaranta. Yara da dama na wuni ne akan anguwa suna wasa.

Labarai Masu Nasaba

Hukunce-Hukuncen Sallar Idi

Hana Zuwa Kasar Waje Neman Ilimi Zai Daukaka Darajar Ilimi A Nijeriya

A wasu lokutan kuma yara idan iyayensu sun tura su makaranta, yaran da kansu suke labewa a hanya suki zuwa Makarantan, ko kuma bayan sunje makarantan idan malamai basu ganinsu sai su gudu.

Babban abun mamakin shi ne, Jihohin Arewa da aka sansu da neman ilimi duk inda yake a fadin duniya yau kuma su ne fama dasu akan zuwa makaranta.

Me ke jawo wannan dabi’a? Idan mai Karatu bai manta ba ranar sha daya ga watan June na shekarar dubu biyu da ashirin da daya (11/6/2021), nayi rubutu wanda na yi ma taken ; “Bukatar kara Muhimmatar Da Ilimin Yaya Mata”.

Cikin abubuwan da na kawo akwai cewa iyaye a na guje ma ba yayansu mata Karatun da ya Kamata ne saboda wai idan sun girma ba za su waywaye su ba. Idan mun yarda da wancan hujjan da suke kawowa, tambayar da zamu yi masu shi ne; idan baza su kai yayansu mata Makaranta ba, toh mai yasa suke barin wasu daga cikin yayansu maza a gida ba tare da sun tura su makaranta domin koyon Karatun da ya Kamata ba?
Akwai dalilai da wasu iyaye ke kawo wa, amma duka dalilan idan ka kalle Su da idon basira toh zaka gano duk shirme ne. A Wasu lokutan zaka sam ba laifin iyaye bane, yaran ne da kansu ke yanke hukuncin barin makaranta ba tare da sun shawarci kowa ba, amma duk da haka zaka iya mayar da laifin kan iyaye. Idan mutum na bibiyan wannan shafi, idan bai manta ba a ranar sha takwas ga watan June shekara ta dubu biyu da ashirin da daya (18/6/2021) na kawo hanyoyin dakile shaye shayen miyagun kwayoyi.

Daga cikin dalilan da na kawo wanda ke sabbaba shaye shayen akwai halin ko in kula da iyaye ke nunawa wajen tarbiyyan yayansu (musamman maza) da zarar yaro ya kai wasu shekaru sai kaga Kaman iyayen tsorin shi suke ji.

Wannan ma na iya zama daya daga cikin dinbin dalilan dake sabbaba samari su daina zuwa makaranta. Tunda ko sun daina zuwa babu wanda zai iya cewa su koma makaranta, musamman ma idan suna kawo ma iyayensu abun tabawa (wato Kudi).

Daga cikin halin ko in kula da iyaye ke nunawa akwai rashin kula da me aka koya ma yayansu a Makaranta, wasu iyayen basu duba littafan yaransu idan sun dawo makaranta domin su ga abun da aka koya masu.

Duk yaran da iyayensu basu damu da Wannan ba to zaka samu yaran basu damuwa da zuwa makaranta. Kuma ba su maida hankali dari bisa dari suyi Karatu saboda sun san ko da sun dawo gida babu wanda zai tambaye su. Wasu iyayen tun da suka kai yayansu makaranta lokacin da zasu yi masu rijista toh basu kara komawa makarantan koda malaman makarantan sun neme su.

Hakane kuma baya ba yara kwarin guiwar cigaba da karatu.
A duk lokacin da mahaifi ko mahaifiya suka dauke kafa ga barin zuwa makarantun da yayansu ke karatu, ba zasu taba sanin halin da yayansu ke ciki ba. Wasu lokutan idan dalibi yayi laifi, Malamai kan nemi ya Kira iyayen shi, idan iyayen suka ki zuwa toh yaron ya samu damar aikita abun da yake so tunda babu mai kwaba mai.

Gaskiyar magana shi ne iyaye basu da hujjan kyale yayansu ba tare da ilimi ingantacce ba. Akwai masu fakewa da talauci a matsayin dalili, idan ka tambaye su sai su ce maka basu da kudin da zasu tura yayansu makaranta. Talauci kuma ba akan mu yan arewa ya kare ba, sauran jihohin sassan Nijeriya ma na fama da matsanancin talauci, amma duk da haka sun daure, sun takura kansu sun tura yayansu makaranta saboda suna sa ran cewa nan gaba za su taimakesu.

Wasu ahalin zaka samu mutum daya suka takura kansu domin su tura shi Makaranta. Mu baza mu iya yin hakan bane? Abun zuciya ne ba tarin dukiya ba. Dauriya kawai ake bukata na dan lokaci kadan da yardan Allah kuma zamu ga anfanin hakan. Kuma akwai Makarantun Gwamnati masu inganci inda ake koyar da Karatu kyauta, ba sai iyaye sun biya ko sisi ba.

A wasu Jihohin har kayan makaranta ake ba dalibai kyauta. Kaga Kenan ba mu da Wani hujja da zai hana mu tura yayan mu makaranta.

A wannan zamanin da ko a ina kake zaka iya yin Karatu ba tare ka shiga aji ba bai Kamata ace muna fama da rashin zuwa makaranta ba.

Yakamata muma yan Arewa mu kutsa, mu shiga ko Wani fagen ilimi, domin a rika gogawa damu a kowani fanni na rayuwa. Ba wai ba zamu iya bane, muna da hazikan mutane da za su iya shiga kowani fanni na Karatu, daga fannin kere kere, likitanci da sauransu, duka zamu iya shiga.

Ina rkon iyaye da su yunkura su daure domin yayansu su samu ingantaccen ilimi a dukkan matakin rayuwa. Ina Kira ga yan uwa na dalibai da kar mu ba iyayenmu kunya mu dage domin ganin cewa yankin mu ya cigaba. A bangaren Gwamnati kuma ina Kira da su kara ware kudi daga cikin kudaden da suke ware ma bangaren ilimi, domin cigabantar da Ilimin yara, mata, da kuma matasa.

Like this:

Like Loading...
SendShareTweetShare
Previous Post

Waiwayen Kanun Labarai: Daga 17 Zuwa 20 Ga Watan Zulkida 1442

Next Post

Manchester United Ta Dauki Jadon Sancho

Labarai Masu Nasaba

Sallar idi

Hukunce-Hukuncen Sallar Idi

by S.P Imam Ahmad Adam Kutubi
3 weeks ago
0

...

Ilimi

Hana Zuwa Kasar Waje Neman Ilimi Zai Daukaka Darajar Ilimi A Nijeriya

by
3 months ago
0

...

Mai

Mafita A Kan Turka-turkar Tallafin Mai A Nijeriya – Dakta Ahmed Adamu

by
3 months ago
0

...

Masari

Siyasar Katsina: An Fara Zare Ido Kan Neman Kujerar Gwamna

by
10 months ago
0

...

Next Post

Manchester United Ta Dauki Jadon Sancho

Domin bayar da talla ko neman ƙarin bayani a tuntuɓe mu a: +2348039216372

  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us | English Edition | Fashion Magazine | Business News

© 2022 Leadership Media Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2022 Leadership Media Group .

Go to mobile version
%d bloggers like this: