Manoman Nijeriya kamar takwarorinsu na wasu kasashen Afrika suna fama da matsalar karancin Takin zamani, wanda shi ne daya daga cikin abubuwa masu muhimmanci da ake bukata a gona don samar da abinci tare da kawo karshen matsalar rashin abinci da ake fuskanta a kasar nan dama nahiyar Afrika gaba daya.
Dumamar yanayi da matsalolin da ya haifar ya kai ga tilasta amfani da Takin zamani a gonakinmu don kara bunkasa albarkar kasa wanda hakan zai kai ga samar da yabanya mai yawa.
- Sin Ta Yi Watsi Da Rahoton MDD Game Da Batun Kare Hakkin Bil Adama A Xinjiang
- Jami’an KAROTA Sun Cafke Tirela Makare Da Giya A Kano
Tabbas amfani da Takin zaman ya taimaka wajen samun karin girbin abin da aka shuka wanda hakan kuma yana taimakawa wajen tabbatar da wadatar abinci a fadin kasar nan dama yankin Afriki gaba daya.
Amma kuma duk da muhimmanci Takin zamani ga harkar noma a wannan lokacin, Takin ya yi matukar karanci ga shi kuma da tsananin tsada, Taki na neman gagarar kanana da matsakaitar manona, musamman ganin yadda aka siyasantar da rabawa in gwamnati ta samar don manona su amfana.
Bayani ya nuna cewa, a halin yanzu farashin Takin NPK da Urea ya kai Naira 20, 000 a kasuwannin mu.
Abin takaici a nan shi ne yadda tallafin da gwamnati ke ikirarin tana sanya wa don amfanar talaka baya isa ga wadanda suka fi bukata, Takin ya fada hannun mugayen ‘yan kasuwa wadanda suka tsawalla masa kudi, suka kuma boye shi don a wasu wuraren ko da kudin ka samun Takin yana da mautukar wahala ga kanana da matsaikaitan manoma.
Mun damu matuka a kan karancin Takin zamani don kuwa hakan ya kara matsalar da manoman mu ke ciki ne, musamman ganin suna fuskantar matsaloli a wasu wuraren da suka hada da ayyukan ‘yanta’adda, wadannan matsaloli ne masu tayar da hankula don a wasu wuraren harkar noman ma ta tsaya cik.
Saboda haka fuskantar tsadar Takin zamani a irin wannan lokacin abu ne da zai dagula lissafin manoma gaba daya zai kuma haifar da karancin abinci a cikin al’umma.
Kwanakin baya, babban sakataren Kungiyar Masu Sarrafa Takin Zamani a Nijeriya, (FEPSAN), Gideon Nagedu ya yi ikirarin cewa, Takin Urea, ne kadai ake fuskantar karancinsa a Nijeriya, wai kuma hakan na faruwa ne saboda karancin Iskar Gas da ake fuskanta a Nijeriya, sai dai kuma wasu bayanai sun nuna cewa karancin Takin da ake fuskanta ba wai ya tsaya a kan Takin Urea kada ba ne.
 Duk kuwa cewa, muna sane da cewa, annobar cutar Korona da aka fuskanta a Duniya da yadda aka takaita zirga-zirga da kuma yakin da ake yi a halin yanzu a tsakanin Rasha da Yukiren ya taimaka wajen haifar da karancin Takin zamani, amma muna kira ga Gwamnati a dukkan matakai da su tabbatar da daukar matakan da suka dace don kawo kaeshen karancin Takin da ake fuskanta a halin yanzu don kuwa barazana ce ga samar da wadataccen abinci ga al’umma.
A daida wannan lokaci kuma ya kamata mu ne jin dalilin da ya sa Kamfanonin Takin Zamani na cikin gida suka kasa fuskantar samar da issasun takin zamanin ga manoman Nijeriya.
In har da gaske ake yi na kokarin samar da issashe Takin zamani ga manoman Nijeriya to ya zama tilas kamfanonin takin zmani na cikin gida su farfado don ganin sun cike gibin Takin da ke bukata a cikin gida har a fara tallafa wa wasu kasashen Afrika.
Wadannan matakan sun zama dole saboda ganin muhimmancin Takin zamani ga harkar noma a wannan lokacin.
Idan za a iya tunawa a shekarar 2016, gwamnatin tarayya ta sanya hannun a wata yarjejeniyar samar da Takin zamani tsakaninta da wani kamfanin kasar Morocco, an shirya amfani da Iskar Gas ta Nijeriya da kuma sinadarin phosphate daga kasar Maroco don samar da issashen Takin.
Gwamnati ta bayyana cewa, yarjejeniyar ta samar da shirin yadda za a yi amfani da Iskar Gas na Nijeriya da Phosphate daga kasar Moroco don samar da Tan 750,000 na sinadarin Ammonia da tan Miliyan daya na Takin Phosphate a duk shekara daga nan zuwa shekarar 2025.
Babu tantama zuba jari a bangaren samar da Takin zamani zai matukar taimakawa Nijeriya a kokarinta na samar da isashen abinci ga al’ummarta hakan kuma zai taimaka wajen bunkasa tattalin arzikin kasa.
Dole a wannan gabar a yaba wa Kamfanin Dangote a bisa kokarinshi na samar da takin zamani a cikin gida ta yadda ya kafa katafaren kamfanin Takin zamani da aka kiyasta kudinsa ya kai Dala Biliyan 2.5.
Mun tabbatar da cewa, kamar mafi yawa ‘yan Nijeriya, Kamfanin Taki na Dangote zai bayar da gaggarumar gudummawa wajen ganin an samu wadataccen Takin zamani a kasa yayin da za a iya fitar da rarrar zuwa kasashe Afrika da sauran kasashen duniya.
Akwai dalilai da dama da dole gwamnati ta sanya hankali a kula da bangaren harkar noma, ciki kuwa akwai cewa a halin yanzu bangaren yana samar da aikin yi ga fiye da kashi 33 na ‘yan Nijeriya, gona ne kuma bangaren tattalin arzikin kasa da ya fi kowanne samar wa da al’umma aikin yi, don haka dole gwamnati ta sanya ido a kan ganin bunkasar bangaren.