Bullar Sabuwar Cuta A Jihar Kogi Ta Kashe Mutum 50

Rohotanni daga jihar Kogi na cewa, an samu bullar sabuwar cuta a jihar inda nan ta ke ta kasha mutum hamsin a kauyukan: Okunran, Okoloke da  Isanlu-Esa duk a karamar hukumar Yagba West dake jihar Kogi.

Da farkon bullar cutar, an bayyana ta a matsayin cutar zazzabin Lassa, daga bisani wata likita a asibitin ECWA dake garin  Egbe, Jannette Hathorn, ta sanarwa kwamishinan lafiya na jihar Kogi, Saka Audu a yau Alhamis cewa, cutar ba zazabin Lassa ba ne, wata sabuwar cuta ce da ta bulla a yankin.

A sakamakon binciken likitoci, duk wanda ya kamu da cutar zai fara gudawa, aman jini da zazzabi mai tsanani.

Jannette Hathorn, ta ce, mutum na farko da cutar ta fara kashewa shi ne wani yaro mai shekaru biyu da rabi wanda aka kawo shi asibiti a cikin sa’o’i 12 ya rasa ransa.

A yanzu haka ma’aikatar lafiya na binciken yadda za a magance bullar cutar.

Exit mobile version