Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni ya bukaci mabiya addinin Kirista a Nijeriya su yi amfani da bikin Easter wajen yin addu’o’i na musamman domin samun nasarar mika mulki ga sabuwar gwamnati mai zuwa.
A sanarwar manema labaru mai sa-hannun mai magana da yawun gwamnan, Alhaji Mamman Mohammed ya ce, Buni ya sanar da hakan ne a sakonsa na bikin ranar Easter da ya aike wa mabiya addinin Kirista.
- Da Dumi-dumi: APC Ta Dakatar Da Dan Majalisar Wakilai Shehu KokoÂ
- Duk Da Tsadar Kujerar Aikin Hajjin Bana, Jihar Kaduna Na Bukatar Karin Kujera 500
Ya kara da cewa, abu ne mai mahimmanci a yi amfani da wannan lokacin wajen nuna kauna da soyayya tare da sadaukar wa a matsayin sakon da yake kunshe a bikin ranar Easter ga kasarmu Nijeriya.
“Kyakkyawan darasin da yake tattare da wannan rana shi ne kaunar juna da sadaukar wa, wanda suka dace a aiwatar da su wajen bunkasa zaman lafiya da hadin kai don ci gaban Nijeriya da ‘yan kasa baki daya.”
Har wala yau, gwamna Buni ya shaidar da cewa, wannan lokaci ne mai albarka wanda mabiya addinin Kirista suke gudanar da harkokin ibada a cikin na Easter, kuma a daidai lokacin da al’ammar musulmi suke gudanar da azumin watan Ramadan.
“Wanda saboda haka, wannan babbar dama ce garemu a matsayin yan kasa, muyi amfani da wannan lokacin mu yi addu’o’i na musamman ga kasarmu.” In ji gwamna Buni.
Gwamnan ya jaddada kira ga shugabanin addini da na al’amma, kowane lokaci su rinka yin wa’azuka da kira wajen samun dawamamen zaman lafiya da fahimtar juna.
“Matikar mun aiwatar da koyarwar addininmu, zamu samu ci gaba mai dorewa ta hanyar samun zaman lafiya.”
“Saboda a ‘yan shekaru kadan da suka gabata, ba za mu iya zuwa masallatanmu da coci cikin nutsuwa ba a jihar Yobe, sakamakon matsalolin tsaro da muka sha fama dasu, amma yanzu cikin taimakon Allah, zaman lafiya ya dawo kowa yana harkokin sa cikin limana.”
“Bisa ga wannan, mu yaki son zuciya tare da yaki da shaidan don kaucewa abubuwan da za su harzuka mu aikata abin da zai kawo tashin-tashina a jiharmu ta Yobe da Nijeriya baki daya.” In ji shi.