Tsohon Shugaban sojin kasan Nijeriya Laftanar Janar Tukur Buratai ya kai karar mawallafin jaridar Sahara Reporters, Omoyele Sowore zuwa gaban babban kotun da ke zamanta a cikin birnin tarayya bisa zargin wallafa labari na karya.
Buratai na neman diyyar ba ta masa suna na biliyan 10 saboda a cewarsa, Sowore, mawallafin jaridar yanar gizo ta Sahara Reporters, ta alakanta shi da wani labarin biliyoyin naira da hukumar yaki da cin hanci da rashawa (ICPC) ta kama a wani gida da ke Abuja.
A cewar Buratai ta cikin kara mai lamba FCT/HC/CV/252/2022 da ya shigar ta hannun lauyansa Dakta Reuben Atabo, SAN, ya bukaci a hana Sowore da kafarsa wallafawa ko buga wani labarin bata suna a kansa.
Babban Lauyan ya roki kotun da ta ayyana labarin da kafar ta wallafa a ranar 23 g watan Yunin 2022 mai kanu “ICPC ta gano biliyoyin naira da aka ware domin sayen makamai da alburusai na yaki da Boko Haram a Abuja a gidan tsohon Shugaban sojin saman Nijeriya Buratai a matsayin labari ne na bata kima kuma a umarci wanda ake kara da ya janye labarin tare da neman afuwa a bayyanar jama’a da zai zama dole ya wallafa ban hakurin a manyan jaridun kasa guda biyu.
Tare da neman kotun ta hana kafar wanda ake karan sakewa ko cigaba da wallafa irin wannan labarin a gaba wanda yake karewa.
Kan hakan ya nemi diyyar biliyan goma na bata suna, yada karya da kage a kansa.