• English
  • Business News
Wednesday, May 14, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Burina Masu Basira Su Rika Amfana Da Basirarsu -Haidar Blog

by Leadership Hausa
2 years ago
in Nishadi
0
Burina Masu Basira Su Rika Amfana Da Basirarsu -Haidar Blog
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Fasihin mawakin Hausa, kuma dan kasuwar dake dillancin wakokin Hausa a yanar gizo, mai suna Aliyu Abubakar, da ake wa lakabi da Haidar Blog, ya bayyana wannan kyakkyawan fata da buri da yake da shi ne a kan mawaka da dukkan wadanda Allah Ya yi wa baiwar basirar na suna amfanuwa da basirar tasu don kara samun kwarin gwiwa gare su.

Tare kuma da yin kira ga matasa da su kara kaimi wajen neman ilimi, wanda da shi ne rayuwar bawa take yin haske kuma komai ke zuwar masa a saukae, a wata tattaunawa da ya yi da wakilinmu. Ga dai yadda tattaunawarsu da ADAMU YUSUF INDABO ta kasance:

  • Sin Ta Bukaci Amurka Da Ta Daina Muzgunawa Kamfanonin Waje
  • Ramadan: Lokutan Sahur Da Buda-baki Na Azumi Na 3 A Wasu Birane

Wane ne Haidar Blogger, cikakken suna da takaitaccen tarihinka?

To a takaice dai asali suna na shi ne Aliyu Haidar Abubakar. Kuma asalina haifaffen Garin Zaria ne, a wata unguwa mai Suna Gyellesu. Na yi makarantar primary har zuwa secondary. Sannan yanzu haka ina ci gaba da karatu na a ABU Zaria. Sunana na Haidar Blog ya samo asali ne tun lokacin da muke secondary saboda ina son Ilimi a kan na’ura mai kwakwalwa wato  computer. Don haka sai na kasance mai bincike da bin kwakkafi a kan computer tun wancan lolacin. Hakan ya taimaka min sosai wajen sanin abubuwa da dama da suka shafi computer, har ma na yi wani website mai Suna  HaidarBlog a inda nake rubuce-rubucena a kan harkar Entertainment. Toh ka ji Yadda na samo Sunan Haidarblog.

Sunan Haidar Blog sananne cikin mawaka da ma industry, to ya aka yi ka tsinci kanka a cikinsu?

Labarai Masu Nasaba

Har Yanzu Da Bazar Mahaifina Nake Rawa -Hanafi Ibro

Rashin Hadin Kai Ke Dakile Ci Gaban Masana’antar Kannywood -Ayatullahi Tage

To farkon fara wakena dai na fara ne da yin wakokin yabon fiyayyan halitta (S.A.W.) tun a makarantar Islamiyya. Daga nan kuma son waka ya shiga raina ya zauna daram, har ya kai ni ga shiga cikin mawaka ina kulla abota da su. Don dama ka san ‘yan Hausa suka ce “Ba a abota sai hali ko ra’ayi sun zo daya.”

To wacce waka ka fara rubutawa, kuma cikin tarin wakokin naka wacce ce bakandamiyarka?

To wakar da na fara rubutawa da hannuna ita ce SAYYIDIL ANAMI wacce take ta yabo ce tsantsa ga fiyayyan halitta. Allah Ya sa ya cece mu a ranar da babu wani maceci bayan shi Ameen. Amma wakar da na fara shiga studio na rera ta, ba ni na rubuta ta ba, abokina ‘Ghali Ladabin Bege’ shi ne ya rubuta ta ni kuma na rera. Bakandamiya a cikin tarin wakokina kuwa ita ce wacce na yi mata lakabi da DIWANI.

To ya batum wakokin nanaye, ko na ce wakokin soyayya?

Nakan Rubuta wakokin soyayya, amma dai ba ni nake rerawa ba.

Da alama ka fi karkata ga wakokin yabo. To ya aka yi ka yi kicin-kicin a cikin harkokin wakokin da ba na yabo ba?

Eh Toh ni Mutum ne mai son ganin masu basira Suna amfanuwa da basirarsu. To don haka sai na kutsa ciki. Bincike, na yi binkice na ga da yawan mawakan Arewa ba su san ta ya ya kamata a ce sun amfana da basirarsu ba. To a nan ne na fara binkicen wadanne hanyoyi ne ake samun kudi da waka? Ma’ana yaya za a yi Mawaki ya sayar da wakar sa a Internet, tunda yanzu babu CD, babu cassette. A haka kuma Allah da ikon sa muka yi binkice. Har dai ma na yi makaranta a Online, a kan yadda zan bi wajen Siyar da waka a online daa dai sauransu.

To yanzu ya kasuwancin wakokin yake a yanar gizo, shin ko kwalliya na biyan kudin sabulu?

Eh a gaskiya tana biya, amma ga Wanda ya san yadda zai bi ya samu kudi. Sakamakon da yawan mawakan mu na arewa wasu  ba su san yadda na za su Distribution din wakaba. Ballan tana a ce promotions (marketing), ko Music Publishing, ko syc licensing.

To a matsayinku na manyan mawakan dake da ido a kan yadda za a  tafi da zamani, ko akwai wani taimako da kuke bawa matasan mawaka musamman ta bangaren marketing a yanar gizo?

Eh sosai ma kuwa. Muna iya yin mu wajen nuna wa da yawansu hanyoyi da ya kamata su bi wajen tallata kansu da hajojinsu ba tare da sun biya ko sisi  ta hanyar yanar Gizo. Wasu kuma sukan biya mu mu yi musu Promotion koh kuma mu zama manager dinsu. Ban da haka ma, nakan bayar da courses a online, kamar a zoom  meeting da wasu Mawaka Koh kuma. Artist Management. Don yanzu haka Ina Management na Artist kamar Kawu Dan Sarki, Sani Ahmad, Zainab Ambato, Rabil Jo’s. Da dai sauransu. Ma’ana ni ne mai kula da music Distribution, Music publishing, Music copyright, Sync licensing  da social media management nasu.

Na ji ka ambaci ‘music publishing’ ka kuma maimaita ta. Wai me take nufi ne?

Music publishing  wani abu ne da ake yi wa Maruruta waka da ma mawakan, wajen ganin Kowa ya karbi rabon sa a wannan wakar,kamar yanzu a ce wani dan America ya kunna wakar Hamisu breaker a club Koh gidan Abinci. To in dai su Hamisu Breaker sun yi publishing wakar tasu to za a biya su wannan kudin kunna wakarsu da ya yi. To wadancan mawaka da na lissafa ma a sama, ni ne nake musu publishing wakokinsu shi ya sa a kullum suke kirga ribar wakokim da suka wallafa har na shekarun da suka shude.

Ikon Rabbi, lallai ilimi kogi ne. To daga shigarka wannan harka, ta managing and music publishing zuwa yau wadanne nasarori ka cimma?

Alhamdulilah a wanna harkar ba ni da abin cewa Allah Sai godiya, na samu nasori da yawa, domin na fara wannan aiki ne da wayata ta hannu. Amma yanzu kuma ga shi har ina da Office da yara da muke harkoki tare.

Kuma ya batun kalubale?

Kalubale wannan kuma dukkan wanda ya yi nasara a rayuwa Sai Ya fuskaci kalubale.

Kasancewar harkarku harka ce ta tara masoya. To ta wacce hanya masoyanka za su iya samun ka?

Mutane Suna iya samu na a Shafina da INSTGRAM koh tweeter koh tiktok.

A karshe, wanne kira ko fata za ka yi ga masoyanka da kuma abokan harkarka da mawaka baki daya?

Kira zan yi ga dukkan Samari da mu dage wajen neman ilimi a kan dukkan wata harka da za ka yi, domin in kana da sani a wannan fanni Komai zai zo maka da sauki.

To Malam Haidarblog mun gode.

Ni ne da godiya.


Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: haidar BlogMawakiNishadi
ShareTweetSendShare
Previous Post

Rukunin Na’urori Na Biyar Na Tashar Samar Da Wutar Lantarki Ta “Lower Kefu Gorge” Dake Zambiya Sun Fara Aiki

Next Post

An Bude Dandalin Tattauna Harkokin Samar Da Ci Gaba Na Kasar Sin

Related

Har Yanzu Da Bazar Mahaifina Nake Rawa -Hanafi Ibro
Nishadi

Har Yanzu Da Bazar Mahaifina Nake Rawa -Hanafi Ibro

3 days ago
Rashin Hadin Kai Ke Dakile Ci Gaban Masana’antar Kannywood -Ayatullahi Tage
Nishadi

Rashin Hadin Kai Ke Dakile Ci Gaban Masana’antar Kannywood -Ayatullahi Tage

3 days ago
Ya Kamata Mata ‘Yan Fim Su Rike Mutuncin Kansu – Aisha Tafida Gombe
Nishadi

Ya Kamata Mata ‘Yan Fim Su Rike Mutuncin Kansu – Aisha Tafida Gombe

1 week ago
Saboda In Nuna Wa Duniya Asalin Al’adar Bahaushe Ya Sa Na Fara Fina-finan Turanci A Arewacin Nijeriya – Jammaje
Nishadi

Saboda In Nuna Wa Duniya Asalin Al’adar Bahaushe Ya Sa Na Fara Fina-finan Turanci A Arewacin Nijeriya – Jammaje

2 weeks ago
Daga Kaina An Gama Harkar Fim A Zuri’ata – Moda
Nishadi

Daga Kaina An Gama Harkar Fim A Zuri’ata – Moda

2 weeks ago
Rarara Zai Angwance Da Aisha Humaira Yau A Maiduguri
Manyan Labarai

Rarara Zai Angwance Da Aisha Humaira Yau A Maiduguri

3 weeks ago
Next Post
An Bude Dandalin Tattauna Harkokin Samar Da Ci Gaba Na Kasar Sin

An Bude Dandalin Tattauna Harkokin Samar Da Ci Gaba Na Kasar Sin

LABARAI MASU NASABA

gaza

Kasafin Kudi Na Naira Tiriliyan 1.78 Na Abuja Ya Tsallake Karatu Na Biyu A Majalisa

May 14, 2025
Kasar Sin Za Ta Inganta Cikakken Tsarin Fitar Da Ma’adanai Zuwa Ketare Don Kiyaye Tsaron Kasa

Kasar Sin Za Ta Inganta Cikakken Tsarin Fitar Da Ma’adanai Zuwa Ketare Don Kiyaye Tsaron Kasa

May 14, 2025
Tinubu Ya Yaba Wa Sule Lamiɗo A Taron Ƙaddamar Da Littafin Tarihin Rayuwasa

Tinubu Ya Yaba Wa Sule Lamiɗo A Taron Ƙaddamar Da Littafin Tarihin Rayuwasa

May 14, 2025
Manyan Ayyuka Guda Biyar Za Su Raya Makomar Al’ummomin Kasar Sin Da kasashen Latin Amurka Da Caribbean Ta Bai Daya

Manyan Ayyuka Guda Biyar Za Su Raya Makomar Al’ummomin Kasar Sin Da kasashen Latin Amurka Da Caribbean Ta Bai Daya

May 14, 2025
Yadda Aka Gina Ofishin ‘Yansanda Na Zamani A Abuja

Yadda Aka Gina Ofishin ‘Yansanda Na Zamani A Abuja

May 14, 2025
JAMB Ta Amince Da Maki 140 Da 100 Mafi Karancin Maki Na Shiga Manyan Makarantu

JAMB: Tangarɗar Na’ura Ne Ya Haifar Da Gagarumar Koma Baya A Sakamakon UTME Na 2025

May 14, 2025
A Sa Hikima Da Dabara Yayin Da Ake “Wasan Kati ” Da Kasar Amurka

A Sa Hikima Da Dabara Yayin Da Ake “Wasan Kati ” Da Kasar Amurka

May 14, 2025
Ɗan Wasan Super Eagles Na Tsaka Mai Wuya Bayan An Yi Masa Tiyata

Ɗan Wasan Super Eagles Na Tsaka Mai Wuya Bayan An Yi Masa Tiyata

May 14, 2025
Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Bunƙasa, Amma Farashin Kayayyaki Na Ci Gaba Da Tashi – Bankin Duniya

Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Bunƙasa, Amma Farashin Kayayyaki Na Ci Gaba Da Tashi – Bankin Duniya

May 14, 2025
Sin Ta Daidaita Harajin Fito Kan Hajojin Amurka Da Ake Shigarwa Kasar

Sin Ta Daidaita Harajin Fito Kan Hajojin Amurka Da Ake Shigarwa Kasar

May 14, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.