Connect with us

RAHOTANNI

Burinmu Ne Ciyar Da Al’umma Biredi Mai Inganci – Tahir Bread

Published

on

A ranar Asabar 25 ga watan Yuli ne hadaddiyar kungiyar masu sana’ar yin Biredi a Jihar Kaduna ta gudanar da wani taronta na shugabannin kungiyar gami da shugabannin kungiyar masu sana’ar dafa shayi ta Jihar Kaduna. Taron wanda aka gudanar da shi a babban ofishin kungiyar masu sana’ar yin Biredin da ke Unguwar Sanusi Kaduna, taron ya sami halartar dukkanin shugabannin masu sana’ar yin Biredin da kuma shugabannin masu sana’ar dafa shayin.

Da yake jawabi a kan dalilin shirya taron, Shugaban kungiyar masu sana’ar yin Biredin ta Jihar Kaduna, Alhaji Bashir Tahir, ya yi bayanin makasudin kiran taron da cewa, “Alhamdu lillahi, mun kira wannan taron na hadin gwiwa ne a tsakaninmu da shugabannin kungiyar masu dafa shayi a nan Jihar Kaduna domin fuskantar irin kalubale da matsalolin da ke fuskantar wannan masana’antar namu, domin samun hanyoyin warware su cikin lumana.

Shugaban ya ci gaba da bayanin irin matsalolin da sana’ar ta yin biredi ke fuskanta a kusan shekaru biyar da suka gabata. Matsalolin da a cewar shugaban hatta al’umma masu siyan biredin domin su ci su da iyalansu suke ta yaba namijin kokarin da kungiyar masu sana’ar yin biredin suka yi, in da ya kasance duk wasu kayayyakin da suke amfani da su a wajen yin sana’ar tasu komai ya kara kudi, amma su masu sana’ar yin biredin ba su kara wa biredin kudi ba a cikin wannan lokacin da ake Magana a kai. Ya bayar da misali da sukari wanda a baya kadan suke siyan buhunsa a kan Naira 9.500, wanda a halin yanzun suna siyan buhun sukarin ne a kan Naira 17,000, Hatta ledar biredin wacce kafin wannan lokacin muke siyan kilo dinta a kan naira dubu daya da naira hamsin, a yanzun muna siyan kilon ne a kan naira 1800, jiya muka yi wannan lissafin, misali ga duk mai yin kwaran biredi 5000 abin da aka kara masa a kudin leda kawai a wata shi ne naira 750,000, butter da muke saye 4,800, a yanzun 9,400, Yeast a baya kadan muna siyansa 5000 ne, amma yanzun 12,000 ne, hatta ashana da ake amfani da ita wajen kunna wuta ta kara kudi, haka nan fulawa da duk sauran abubuwan da suke amfani da su a wajen sana’ar tasu na yin biredi, wanda a yanzun abin ya kai makura ne da ya yi sanadiyar mutane da yawa sun fice daga cikin sana’ar a yanzun haka.

“A yau mun dan kira wani karamin taro ne na shugabannin wadannan kungiyoyi biyun wadanda za su wakilci sauran abokanan sana’o’insu. Abin ban sha’awa shi ne yanda shi kansa shugaban masu sayar da shayin ya bayar da bayanin cewa kusan duk matsalolin namu iri daya ne da na su, don haka muke son samar da hadin kai a tsakaninmu ta yanda za mu tallafa wa juna. Musamman domin ganin duk wani dan karin da za a samu a kan farashin biredin bai zama matsala ba ga mutanen da suke amfani da biredin saboda mu kanmu muna la’akari ne da irin mawuyacin halin da al’umma suke ci.

“Shugaban ya ce, a matsayinmu na shugabanni babban abin da ya fi damun mu shi ne yanda za mu tabbatar da ciyar da al’umma ingantaccen biredi. Alhamdu lillahi, mun sami wannan nasara sama da shekaru biyar da suka gabata, domin a baya in kana cin biredi za ka samu matsala kamar ka ji kana taunawa tare da kasa ko abin da ya yi kama da hakan, wanda a yanzun zai yi wuya ka sami wannan matsalar domin mun shigo da hukumomin lafiya a cikin sana’ar tamu, don haka ba mu da matsala kwarai wajen inganta sana’ar tamu.

A yanzun babbar matsalarmu dai ita ce kayayyaki sun yi tsada ta yanda an kure mutane sosai. Abu mafi mahimmanci shi ne a maimakon a bar mutane suna fita daga cikin sana’ar, gwamma mu duba mu ga yanda za a kyautata da kuma kara inganta sana’ar.

Amma a duk tsawon wannan lokaci da aka samu canjin wannan yanayin babu abin da ya karu a cikin farashin na biredi, biredin da kake saye naira 150,00 ko naira 200,00, har yanzun yana nan a kan farashin na shi. To yanzun an kai mutane makura ne, yanzun ne ake ganin za a kara, sannan kuma karin da za a yin in Allah Ya so ba zai gagari mutane ba, muna cikin al’umma mun san damuwarsu, don haka ba za mu yi abin da zai tsawwala masu ba.

Ga masu yin tafiye-tafiye kuma za su shaidi Jihar Kaduna a matsayin tana daya daga cikin Jihohin da suka fi ko’ina arhan biredi, ga kuma kamar yanda ku ka ji masu sana’ar shayin suna bayar da shaida a nan, cewa a duk inda suke zuwa tarukansu, biredin Kaduna shi ne biredin da ya fi na ko’ina inganci. Tun kafin watan azumi aka yi shawarar yin karin a kan farashin na biredi, amma ganin kusan masu yin sana’ar yawanci Musulmai ne muka ce mu nemi falalar wannan watan na azumi. Duk da hakan, muna kara bai wa al’umma tabbacin cewa duk wani karin da za a yi ba wanda zai sosa masu zuciya ne ba, kari ne dan kadan, misali wani a kara naira 10 wani kuma naira 20, sannan kuma duk wuya za mu yi kokarin tabbatar da ingancin biredin namu.

Da yake na shi jawabin a wajen taron, shugaban kungiyar masu sanar dafa shayi ta Jihar Kaduna, Alhaji Aliyu Yahaya, ya yaba ne kwarai da irin kokarin da masu yin biredin suka yi duk da kasancewar farashin komai ya tsawwala, amma duk da hakan ba su yi kari a kan kudin biredin ba. Amma yanzun abin ya kai makura ga shi har sun kira kungiyarmu ta masu dafa shayi ta Jihar Kaduna domin tattaunawa a kan yin karin da ba zai wahalar da al’umma ba. A gaskiya kamar yanda kowa ya sani ne a Nijeriya kowane kamfani ya kara wa kayayyakin da yake yi kudi. Ko a kwanakin baya mun kira taro na ‘ya’yan kungiyarmu in da muka jinjina ma masu yin biredin a kan yanda sam ba su tsawwala wa mutane ba musamman a lokacin nan da ake zaman gida. Don haka muna yin kira ga gwamnati da ta shigo ta tallafa wa masu yin wannan sana’ar don talakawa su sami sauki.

Haka nan daya daga cikin shugabannin kungiyar mai suna Alhaji Aliyu Muhammad Hamdala Bread, ya yi karin haske ne a kan dalilinsu na yin karin da suke son yin, wanda a cewarsa tsadar kayayyakin da su ke amfani da su ne a wajen sarrafa biredin wanda abin a halin yanzun ya kai makura. In ka cire gwamnati, abu na biyu wajen samar wa da al’umma ayyukan yi a halin yanzun shi ne ayyukan gidan biredi.

Shi ma Umar Salisu, mai gidan biredin Umraza, ya bayyana farin cikinsa ne da samun hadin kan da aka yi a tsakanin ‘ya’yan kungiyar ta masu sana’ar yin biredin wanda ya ce an rasa hakan a baya, sannan kuma har ga shi an kara samun hadin kai a tsakanin masu yin biredin da kuma masu sana’ar dafa shayi. Sannan ya yi fatan alheri da kuma ci gaba gami da bunkasan kungiyar na su. ina kuma kara yin godiya ga abokanan sana’ata masu gidajen biredi a bisa irin taimakon da suke yi wa gwamnati, misali kamar ni ina da sama da ma’aikata 400 masu aiki a gidan biredi na, ka ga a nan ba karamin taimako ne muke yi wa gwamnati ba, don haka ya kamata gwamnati ta shigo ciki domin ganin ta taimaka wa sana’ar.

Shi kuwa Alhaji Mu’azu Umar, EL-Mukhtar Bread, godiya ga Allah ya yi a kan samun hadin kai a tsakankanin masu sana’ar ta yin biredi wanda ya ce a baya a wargaje su ke amma yanzun kansu ya hadu.

“A gaskiya masu sana’ar biredii su na cikin wani hali, amma da yardar Allah tun da aka sami hadin kai za a sami mafita,” in ji El-Mukhtar Bread.
Advertisement

labarai