• English
  • Business News
Tuesday, October 14, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Cacar Baki Ta Ɓarke Tsakanin el-Rufai Da APC Kan Tazarcen Tinubu A 2027

by Leadership Hausa
2 months ago
Baki

A yanzu haka dai cacar baki ta ɓarke tsakanin tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai da jam’iyyar APC mai mulkin Nijeriya kan tallar tazarcen Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu a 2027.

El-Rufai wanda ya kasance tsohon ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, ya yi gargaɗi cewa Nijeriya za ta iya rushewa kwata-kwata idan Shugaba Tinubu ya sami nasara a wa’adin mulki na biyu a 2027.

  • INEC Ta Ayyana 16 Ga Agusta Don Gudanar Da Zaben Cike Gurbi A Jihohi 12
  • Yadda Rarrabuwar Kawunan Jam’iyyu Zai Iya Sauya Alkiblar Zaben 2027

El-Rufai ya bayar da wannan gargaɗin ne a Jihar Sakkwato a lokacin kamfen da haɗakar jam’iyyar adawa ta ADC ta shirya a ƙarshen mako.

Sai dai daraktan yaɗa labarai na APC, Bala Ibrahim, ya bayyana shugabannin ADC a matsayin tarin ‘yan siyasa da suke cikin ruɗani waɗanda ba su da abin da za su iya yi wa ‘yan Nijeriya.

Idan za a iya tunawa dai shugabannin adawa sun amince da ADC a matsayin jam’iyyar da za ta ƙalubalanci Shugaba Tinubu a zaɓen 2027.

LABARAI MASU NASABA

PDP Ta Ɗage Babban Taronta Biyo Bayan Ficewar Wasu Manyan Jiga-jigai

Zaman Gidan Yari Ya Nuna Min Mutanen Da Ya Kamata Na Yi Hulɗar Siyasa Da Su — Faruk Lawan

Mambobin haɗakar jam’iyar sun ƙunshi tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar da tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar LP, Peter Obi da tsohon gwamnan Jihar Ribas, Rotimi Amaechi da tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir Lawal da tsohon shugaban jam’iyyar APC, John Oyegun, da sauran manyan mutane da dama.

A cikin wannan tsarin, haɗakar jam’iyyar ta naɗa tsohon shugaban majalisar dattawa, Daɓid Mark da tsohon ministan cikin gida, Rauf Aregbesola, a matsayin shugaban da sakatare na riƙon ƙwarya.

Tun daga wannan lokaci, jam’iyyar tana ta karɓar masu sauya sheƙa daga sauran jam’iyyun adawa da kuma gudanar da tarurruka domin ƙara masun mambobi a faɗin ƙasar nan kafin zaɓen 2027.

El-Rufai, wanda ya kasance ɗaya daga cikin asalin mambobin APC, ya fice zuwa jam’iyyar SDP a rubi’in farko na wannan shekarar. Haka kuma ya kasance cikin jam’iyyar haɗaka ta ADC.

Ya bayyana cikakken goyon bayansa ga ADC kuma ya yi alƙawarin taimakawa wajen jan hankali ‘yan Nijeriya domin tabbatar da cewa APC ta sha kaye a 2027 a lokacin taron Sakkwato.

Tsohon gwamnan Kaduna ya jaddada cewa idan Tinubu ya samu wa’adi na biyu zai zama barazana mai tsanani ga makomar ƙasar nan.

“Na yi imanin cewa in muka yarda wannan jam’iyya da gwamnatinta ta ci gaba da mulki a zango na biyu, za ta wawuri dukkan abin da ya rage na tattalin arzikin Nijeriya, kuma ba za mu sami ɓarɓushin ƙasarmu ba ko kaɗan. Don haka, wannan yaƙi ne don rayukanmu,” in ji shi.

El-Rufai ya ce dawowarsa cikin harkokin siyasa ba ta ƙashin kansa ba, said ai akwai buƙatar dawowarsa don yaƙar gazawar wannan gwamnati.

Da yake mayar wa El-Rufai martani, sakataren jam’iyyar APC na ƙasa, Sanata Ajibola Basiru, ya buƙaci El-Rufai ya dakatar da yaƙin neman zaɓe 2027 har sai lokaci ya yi, kuma ya jira ya gani yadda jam’iyya mai mulki za ta ƙara yin nasara.

Sakataren APC ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai ta wayar tarho a ƙarshen mako.

Yayin da yake martanin, sakatare APC ya yi kira ga tsohon Gwamnan Jihar Kaduna da ya nemi aiki yi da zai sa ya zama mara zaman banza kafin zaɓen 2027.

Ya nuna cewa za a bayyana jadawalin zaɓen 2027 ne a watan Fabrairun 2026, ya yi mamakin yadda tsohon gwamnan Jihar Kaduna ya fara yaƙin neman zaɓen da ya rage saura shekara biyu.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

‘Yan Majalisa 60 Sun Yi Barazanar Ficewa Daga PDP
Siyasa

PDP Ta Ɗage Babban Taronta Biyo Bayan Ficewar Wasu Manyan Jiga-jigai

October 14, 2025
Zaman Gidan Yari Ya Nuna Min Mutanen Da Ya Kamata Na Yi Hulɗar Siyasa Da Su — Faruk Lawan
Manyan Labarai

Zaman Gidan Yari Ya Nuna Min Mutanen Da Ya Kamata Na Yi Hulɗar Siyasa Da Su — Faruk Lawan

October 14, 2025
Barin PDP Zuwa Wata Jam’iyyar Alamun Rashin Jarumta Ne – Gwamnan Bauchi
Siyasa

Barin PDP Zuwa Wata Jam’iyyar Alamun Rashin Jarumta Ne – Gwamnan Bauchi

October 11, 2025
Next Post
Philippines Za Ta Girbi Sakamakon Rura Wutar Rikici Kan Taiwan

Philippines Za Ta Girbi Sakamakon Rura Wutar Rikici Kan Taiwan

LABARAI MASU NASABA

Xi Jinping Ya Gana Da Shugaban Ghana Da Firaministar Mozambique

Xi Jinping Ya Gana Da Shugaban Ghana Da Firaministar Mozambique

October 14, 2025
‘Yan Majalisa 60 Sun Yi Barazanar Ficewa Daga PDP

PDP Ta Ɗage Babban Taronta Biyo Bayan Ficewar Wasu Manyan Jiga-jigai

October 14, 2025
An Kashe Mutum 3, Wasu 7 Sun Jikkata Sakamakon Ɓarkewar Rikici A Jihar Jigawa

An Kashe Mutum 3, Wasu 7 Sun Jikkata Sakamakon Ɓarkewar Rikici A Jihar Jigawa

October 14, 2025
Rashin Tsaro A Nijeriya Ba Zai Ƙare Ba Matuƙar Ba A Samar da Ayyukan Yi Da Mulki Na Adalci Ba – Amaechi

Rashin Tsaro A Nijeriya Ba Zai Ƙare Ba Matuƙar Ba A Samar da Ayyukan Yi Da Mulki Na Adalci Ba – Amaechi

October 14, 2025
Amnesty International Ta Soki Tinubu Kan Yi Wa Masu Laifin Take Haƙƙin Ɗan Adam Afuwa

Amnesty International Ta Soki Tinubu Kan Yi Wa Masu Laifin Take Haƙƙin Ɗan Adam Afuwa

October 14, 2025
‘Yan Bindiga Sun Sace Ɗan Jarida A Kan Hanyarsa Ta Zuwa Ɗaukar Horo A Kwara

‘Yan Bindiga Sun Sace Ɗan Jarida A Kan Hanyarsa Ta Zuwa Ɗaukar Horo A Kwara

October 14, 2025
Zaman Gidan Yari Ya Nuna Min Mutanen Da Ya Kamata Na Yi Hulɗar Siyasa Da Su — Faruk Lawan

Zaman Gidan Yari Ya Nuna Min Mutanen Da Ya Kamata Na Yi Hulɗar Siyasa Da Su — Faruk Lawan

October 14, 2025
Majalisa Na Shirin Sauya Lokacin Zaɓen 2027 Zuwa Nuwamba 2026

Majalisa Na Shirin Sauya Lokacin Zaɓen 2027 Zuwa Nuwamba 2026

October 13, 2025
Yajin Aiki: Malaman Jami’a Sun Ce Barazanar ‘Ba Aiki, Ba Biya’ Ba Zata Tsorata Su Ba

Yajin Aiki: Malaman Jami’a Sun Ce Barazanar ‘Ba Aiki, Ba Biya’ Ba Zata Tsorata Su Ba

October 13, 2025
Nazarin CGTN: Jama’ar Duniya Sun Jinjinawa Rawar Da Mata Ke Takawa A Harkokin Ci Gaba

Nazarin CGTN: Jama’ar Duniya Sun Jinjinawa Rawar Da Mata Ke Takawa A Harkokin Ci Gaba

October 13, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.