Umar A Hunkuyi" />

CAN Ta Bukaci A Yi La’akari Da Addini Wajen Nada Shugabannin Majalisa

Kungiyar Kiristoci ta kasa (CAN), ta ce, ko dai ya kasance shugaban majalisar Dattijai na gaba a zaman majalisar na 9 ko kuma Kakakin majalisar wakilai ta kasa ya kasance Kirista ne domin gyara daidaito a yanayin shugabanci na siyasan kasar nan.
Shugaban kungiyar ta CAN na kasa, Samson Ayokunle, ne ya yi wannan bukatar cikin wata sanarwa da mai taimaka masa na musamman a kan harkokin sadarwa da manema labarai, Adebayo Oladeji, ya sanyawa hannu a ranar Litinin, a Abuja.
Mista Ayokunle, ya bukaci sabbin shugabannin na majalisun kasa da su tabbatar da samar da daidaiton Addini da na kabila a wajen zaban shugabanni a majalisun kamar yanda tsarin mulkin kasa na 1999 ya tanada domin gujewa wani ya danne wani.
“Mu a Kungiyar Kiristoci ta kasa mun san mahimmancin majalisun kasa wajen tabbatar da zaman lafiya da ci gaban kasa.
A cewar malamin na Kirista, “Duk da cewa, Majalisar Dattijai da Majalisar Wakilai ta kasa suna da shugabanni masu yawa, amma abin nufinmu a nan shi ne shugaban majalisar Dattawa da mataimakin sa, Kakakin Majalisar Wakilai ta kasa da mataimakin sa.
“Kamar yanda ake yi tun daga 1999, a duk lokacin da ya kasance shugaban majalisar Dattijai ya zamana Kirista, sai Kakakin majalisar Wakilai ya zamana Musulmi, ko kuma sabanin hakan, hakan ne kuma yake kasancewa ga mataimakan su.
“Amma a halin yanzun, da shugaban Majalisar ta Dattijai, da mukaddashin Alkalin Alkalai na kasa duk Musulmi ne, rokonmu a nan shi ne, ko dai a bar shugaban majalisar Dattijai ko kuma Kakakin majalisar wakilai ya kasance Kirista ne domin gyara lamarin ta fuskacin Addini.
“Hakan kuma zai karfafi hadin kan kasa, da samar da cikakkiyar biyayya ga shugabanni. Ba ya kasance wasu kalilan daga wasu Jihohi ko yanki ko wata kabila ko wani Addini sun mamaye ko’ina ba.
Hakan kuma ya kamata a yi wajen raban mukamai a kananan hukumomi, ko duk wata hukuma ta gwamnati, domin samar da daidaito a wajen mulkan al’umman da ke wajen,” in ji shi.
Ya kuma tabbatarwa da ‘yan majalisun da samun addu’o’in zaman lafiya daga kungiyar domin samun nasarar gudanar da sha’anin su.
Mista Ayokunle, ya yi roko ga fadar shugaban kasa da kuma shugabannin Jam’iyyar APC, da su goyi bayan matakin da kungiyar ta dauka domin samar da zaman lafiya mai dorewa da ci gaban kasa.
“In muka yi hakan, za mu sami nasarar gyara wasu matsaloli da suke addaban kasar mu a yau, da suke da nasaba da Addini, kabilanci da batun wani ya danne wani a kowane mataki na gwamnati.

Exit mobile version