Abba Ibrahim Wada" />

Cazorla Ya Dawo Daukar Horo A Babbar Kungiyar Arsenal

Dan wasan tsakiyar kungiyar kwallon kafa ta Arsenal, Santi Cazorla, dan kasar Sipaniya ya dawo daga doguwar jinyar da yayi ta watanni 18 inda a yanzu yafara daukar horo da babbar kungiyar Arsenal a ranar Asabar.

Dan wasan mai shekara 33 a duniya yatafi jinya ne tun a shekara ta 2016 sai dai yasha fama da tiyata kala-kala a kafarsa ta hagu wanda hakan yasa ya dade bai dawo ba bayan da aka fara rade radin cewa bazai iya cigaba da buga kwallo ba a kwanakin baya.

Dan wasan yace yana farin cikin dawowarsa cikin fili domin cigaba da daukar horo da ragowar yan wasan kungiyar wadanda ya dade baiyi kwallo da suba wasu ma bai taba buga wasa dasu ba.

Ya ci gaba da cewa bai taba tunanin zaiyi irin wannan dadewar bai dawo fili saboda da farko yayi zaton ciwon nasa bai kai haka ba amma daga baya sai aka gano cewa yana bukatar aiki tukuru akan kafarsa idan har yanason ya dawo ya ci gaba da wasa.

Ya kara da cewa amma kawo yanzu abubuwa sun danyi sauki kuma likitocin kungiyar sunyi kokarin ganin ya samu lafiya domin cigaba da buga wasa saboda haka nan bada dadewa ba zai dawo domin cigaba da fafatawa.

Kwantaragin Cazorla dai zai kare a karshen wannan kakar sai dai ana tunanin kungiyar za ta kara masa yarjejeniyar shekara daya domin ya sake gwada damarsa a kungiyar ta Arsenal wadda yakoma daga kungiyar Malaga ta kasar Sipaniya.

 

Exit mobile version