Rabiu Ali Indabawa">

CBN Ta Bai Wa Sababbin Bankuna Biyar Lasisi

 A cikin makon nan ne mu ka samu labari daga Jaridar Business Day ta kasar nan cewa babban bankin Najeriya na CBN ya ba da lasisi ga wasu bankuna da ake shirin kafawa domin su fara aiki. Kamar yadda labari ya zo mana a Ranar 29 ga Watan Afrilun nan, bankuna 5 ne masu neman tasowa aka ba lasisin soma aiki a Najeriya. CBN ta dauki wannan mataki ne domin ganin ana shigo da kudi ana juyawa a Najeriya. Wannan sababbin lasisi da CBN ya raba zai kuma taimkawa mutanen da ba su mallaki asusun banki ba, su samu damar bude akawun domin su rika ajiye kudin su a cikin banki. Hakan zai bunkasa tattalin arzikin Najeriya.

Kamar yadda hasashe ya nuna. Wasu daga cikin bankunan nan za su fara aiki a watan gobe, yayin da wasun za su soma aiki a tsakiyar shekarar nan. Globus wanda yana cikin bankin da za a bude a kasar, ya shigo gari ne a ranar Alhamis, 2 ga Watan Mayun 2019. Elias Igbinakenzua shi ne babban Darektan wannan banki da za a kafa Hedikwatar sa a cikin Garin Legas. Haka zalika akwai wani banki da mutanen kasar Indiya su ka kawo Najeriya mai suna Titan Bank. Wani tsohon Darektan bankin nan na Heritage, shi ne zai soma rike wannan banki na kamfanin Chi wanda su ka yi fice a fadin Duniya. Ana tunani cewa wannan sabon bankin na Titan zai rika hulda ne da mutanen Indiya da kuma kwarorin kasar Lebanon da ke ayyuka a Najeriya.

Har yanzu dai babu wanda ya san sunayen sauran manyan bankuna 3 da su ka samu lasisi. ‘Yan jarida sun yi kokarin tuntubar bankin CBN amma ba a dace ba. Isaac Okarafor, wanda yake magana a madadin bankin bai amsa kiran da aka rika yi masa a waya domin jin ta bakinsa ba.

Exit mobile version