Abubakar Abba" />

CBN Ya Koka Da Rashin Sayen Kayan Masakun Nijeriya

Babban Bankin Nijeriya CBN, ya sanar da cewa, bangarori, ma’aikatun gwamnati da kuma hukumimin gwamnati suna saba umarnin yin amfani da kayan da aka sarrafa a cikin kasar nan, inda suke kin sayen kayan da masakaun kasar nan suka sarrafa.

Gwanan Babban Bankin Nijeriya, Mista Godwin Emefiele ne ya bayyana hakan a ranar kwanan baya a lokacin wata ganawa da manyan jami’an gwamnati, ‘yansanda da hukumomin tsaro na farin kaya, hukumar hana fasa kwauri da wakilan masakun da ke kasar nan da kuma na sauran kamfanoni .

Ganawar tana daya daga cikin ci gaba da kokarin da ake yi na farfado da masakun da ke kasar nan ta hanyar sayuen kayan da suke sarrafawa.

Babban Bankin Nijeriya CBN, ya bayyana bukatar ganin ‘yan Nijeriya sun rungumi dabi’ar sayen kayan da aka sarrafa a kasar nan.

A cewar Gwamnan Babban Bankin Nijeriya Mista Godwin Emefiele “Ganawara tamu da masu ruwa da tsaki ta nuna cewar, hukumomin na gwamnati ba su sayen tufafin da jami’ansu ke amfani da su daga masakun kasar nan.”

Gwamnan Babban Bankin Nijeriya Mista Godwin Emefiele ya yi nuni da cewa, kokarin da gwamnatin tarayya take yi na farfado da masakun kasar nan, zai yi wuya ta ci nasara in har ba a baiwa masakun cikin kasar nan goyon bayan da ya da ce ta hanyar sayen kayan da suke sarrafawa.

Mista Godwin Emefiele ya sanar da cewa, kin sayen kayan da ake sarrafawa a cikin kasar nan sabawa doka ta 003 ce ta tsarin kasuwanci da cinikayya.

Gwamnan Babban Bankin Nijeriya Mista Godwin Emefiele ya yi nuni da cewa, “idan muna sayen kayan da aka sarrafa a kasar nan, ta hakan ne kawai za mu iya bayar da gudunmawar mu wajen ciyar da tattalin arzikin kasar nan gaba”.

A karashe ya ce, za kuma a samar da ayyukan yi miliyan biyu, kara samar da kudin shiga ga matakan gwamnatii uku da ke kasar nan, rage dala biliyan hudu da ake kashewa wajen shigo da kaya a duk shekara cikin kasar nan, da kuma habaka masana’antun dake kasar nan”

Exit mobile version