Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Mista Godwin Emefiele ya bayyana cewa, bankin na shirin tallafawa manoman rani na kakar bana don su noma kadada miliyan daya a karkashin shirin aikin noma na Anchor Borrowers.
Mista Godwin Emefiele ya bayyana hakan ne a garin Minna da ke a cikin jihar Neja a lokacin kaddamar da rabarwa da manoman shinkafa da kayan aikin gona na shekarar 2020 tare da rabar ma su da bashi.
A cewar Gwamnan na Babban Bankin Nijeriya (CBN) Mista Godwin Emefiele, bankin na CBN na son ganin a kalla an noma tan miliyan biyar na shinkafar cikin gida a kakar noman rani ta shekarar 2020.
Kayan da bankin na CBN ya rabar, an rabar da su ne a karkashin inuwar kungiyar manoman shinkafa ta kasa (RIFAN) wacce tuni, ta jima ta na amafana da shrin na CBN na Anchor Borrowers.
A cewar Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Mista Godwin Emefiele, an kuma yi hakan ne da nufin zakolo sauran manoma a kasar nan da za su iya bayar da ta su gudunnwar wajen kara wadata kasar nan da abinci mai dimbin ya wa.
Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Mista Godwin Emefiele ya sanar da cewa, ana sa ran kuma kimanin manoma guda 75,000 daga jihohi 26 da ke a fadin kasar nan za su amfana.
Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Mista Godwin Emefiele ya ci gaba da cewa, a a kakar damina ta shekarar 2018, manoman da su ka amfana sun karu zuwa kimanin 275,000 yaykin da aka tallafa ma su su ka noma kadada 220,000.
A cewar Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Mista Godwin Emefiele, a kakar noma ta shekarar 2019 kimanin kadada 500,000 aka nomaz kuma muna sa ran a kakar noman rani ta shekarar 2020, manoman rani za su noma kadada miliyan daya.
Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Mista Godwin Emefiele ya kuma sanar da cewa, aikin ya wuce kan noman shinkafa kawai Emefiele, inda ya kara da cewa an kuma fadada shi kan zuwa sauran amfanin Gina kamar su masara, rogo, waken soya da sauransu.
Shi ma a nasa jawabin a wurin taron, Gwamnan jihar ta Neja Alhaji Abubakar Sani Bello ya bayyana cewa, jihar za ta iya samar da tan miliyan biyu daga cikin tan miliyan bakwai na shinkafa da ake bukata a duo shekara a kasar nan.
A cewar Gwamna Alhaji Abubakar Sani, jihar ta na kuma da kimanin kadada miliyan tara, amma a yanzu, mu na noma kimanin kadada 300,000 be kacal, inda kuma ya yi nuni da cewa, akwai bukatar a kara samar NDA wadataceen abinci a kasar nan.
Ma su kiwon kaji sun nuna rashin jin dadinsu game, inda su ka kara da cewa, jihar ba ta bayar da wani taimako.
Daya daga cikin masu kiwon a jihar, Etoro-Obong Inyang, ya bayyana cewa, masu kiwon kaji a cikin jihar suna fuskantar matsaloli masu wahala wajen samun kaji da abinci.
Ya ce, ya kwashe tsawon shekaru 12 yana kiwon kaji, wannan shi ne lokaci na farko a cikin shekaru da ma su kiwon kaji suka yi matukar cutarwa ta kowane bangare na kudi da wadanda ba na tattalin arziki ba, inda ya kara da cewa, abin bakin ciki, babu mutumin da zai sami damar bayar da duk wata ma’ana.
A cewarsa, babu wata hukuma da ta bi ka’ida game da kasuwancin kaji yana kaiwa kusan Naira 6,000, inda ya kara da cewa, a shekarar 2016, gwamnatin tarayya ta bayyana cewa ta gina wata kasaitacciyar masana’antar kiwon Kaji kuma an yi niyyar ne don tabbatar da samuwar kaji na yau da kullum cikin farashi mai rahusa amma, wannan kokarin bai samar da wani sakamako na zahiri ba amma duk da haka suna samun kajin su na yau da kullun daga wajen jihar.
Etoro-Obong Inyang ya bayyana cewa, mutum zai yi tsammanin masu za su iya siyan tsofaffin kajin a farashi mai rahusa, inda ya ci gaba da cewa, tssoffin kajin da muke samu a kasuwanin su ne, Amo, Chi, Sayed, da Chikun, da sauransu.