Hukumar kula da Ɗa’a ta Ma’aikata (CCB), ta ce tana binciken laifukan cin hanci da rashawa da suka shafi tsoffin ministoci, manyan jami’an gwamnati da manyan masu rike da mukamai a matakin tarayya da jiha.
Shugaban CCB, Dr Abubakar Bello, ya bayyana hakan a wata hira da ya yi da Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya ranar Lahadi a Abuja.
“Mun fara binciken manyan mutane. Akwai tsohon minista da muka riga muka kai shi kotu.
“A yanzu haka, muna binciken wani tsohon minista kuma a yanzu haka, babban jami’in gwamnati ne.
“Ba zan ambaci sunaye ba saboda har yanzu muna matakin bincike. Ba ma son mayar da shi shari’ar ta zama a dandalin sada zumunta,” in ji shi.
ADVERTISEMENT














