Tuna baya na nufin kara neman ci gaba cike da kyakkyawan burin. Shekaru 80 ke nan bayan yakin duniya na II, amma dan Adam na kan wata hanya mai muhimmanci na zabi tsakanin hadin kai ko rabuwar kawuna, tattaunawa ko fito na fito, moriyar juna ko nasara daga faduwar wani.
Wani nazarin da kafar CGTN ta gudanar, wanda mutane 11,913 daga kasashe sama da 40 suka amsa ya nuna cewa, goyon bayan sakamakon nasarar yakin duniya na II da tsarin duniya bayan yakin ya samu karbuwa matuka.
- Beijing Zai Bunkasa Amfani Da Fasahohin Zamani A Wuraren Adana Kayan Tarihi
- Sojoji Sun Kama Mutane 69 Masu Fasa Bututun Mai A Yankin Neja-Delta
Nazarin ya nuna cewa, kaso 62.1 na mutane a fadin duniya sun yi imanin cewa, kare sakamakon yakin duniya na II abu ne mai matukar muhimmanci wajen tabbatar da odar duniya bayan yakin. Haka kuma, wasu kaso 67.9 sun amince cewa tsarin tafiyar da harkokin duniya karkashin MDD shi ne ginshinkin tabbatar da oda a duniya bayan yakin, kuma wannan batu ne da daukacin mutanen da suka bayar da amsa a nazarin, daga dukkan kasashen 40 suka amince da shi.
Kimanin kaso 58 na masu bayar da amsa sun yi imanin cewa odar duniya bayan yakin yana lalacewa, inda kaso 58.9 kai tsaye suka bayyana Amurka a matsayin babbar mai haifar da tsaiko ga oda a duniya.
Kafar CGTN da jami’ar Renmin ne suka gudanar da nazarin ta hannun cibiyar inganta tuntubar juna tsakanin kasa da kasa a sabon zamani. An kuma gudanar da nazarin ne tsakanin mutanen manyan kasashen duniya da na kasashe masu tasowa. (Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp