Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta sake yin abin da ta saba, yayin da ta lashe kofin gasar zakarun turai a karo na 15 a gaban magoya baya fiye da 60,000.
Wasan gasar na karshe an buga shi ne a babban filin wasa na Wembley da ke birnin Landan.
- Sirrin Zaman Lafiyar Da Ake Mora A Jihar Nasarawa –Kakakin Gwamnan Jihar
- Masarautar Argungu Da Al’adunta (1)
Wasan wanda ya matukar kayatarwa ya nuna yadda giwaye biyu a fagen kwallon kafa suka nuna kwarewa da jajircewa a mintuna 45 na farkon wasan, wanda ya kare ba tare da an jefa kwallo a raga ba.
Bayan dawowa daga hutun rabin lokaci mataimakin kyaftin din Real Madrid, Dani Carvajal ya jefa kwallo a ragar Dortmund a minti na 74, kafin Vinisius JR ya jefa ta biyu a minti na 82.
Real Madrid ta lashe kofin Zakarun Turai a karo na 15 a tarihinta wanda kuma babu wata kungiya a duniya da ta taba kafa irin wannan tarihi da suka kafa a fagen tamola.