Yayinda aka buga wasannin mako na ƙarshe na gasar Firimiya Lig ta bana Chelsea, Manchester City, da Newcastle United duk sun sami damar shiga gasar cin kofin zakarun Turai na kakar wasa mai zuwa, Chelsea ta samu tikitin shiga gasar bayan ta doke Nottingham Forest da ci 1-0 a filin wasa na City Ground, bagan Levi Colwill ya jefa kwallo a ragar Forest a minti na 50.
Haka zalika Manchester City ta yi nasara a Craven Cottage, inda ta lallasa Fulham da ci 2-0 da ƙwallaye da Ilkay Gundogan da ya ci a minti na 21 sai kuma wadda Erling Haaland ya zura a bugun fenareti a minti na 72, duk da cewa ta sha kashi a gidan Everton da ci 1-0, Newcastle United ta samu gurbin shiga gasar cin kofin zakarun Turai sakamakon wasu wasannin da aka buga.
- Mohamed Salah Ya Zama Gwarzon Ɗan Wasan Firimiyar Ingila Na Bana
- Mun Fara Shirin Lashe Firimiya Ta Gaba –Slot
Carlos Alcaraz ne ya ci wa Everton ƙwallo ɗaya tilo a minti na 65 a wasansu da Newcastle, a ɓangare guda kuma fatan da Aston Villa ke da shi na buga gasar zakarun Turai ya ruguje yayin da Manchester United ta doke su da ci 2-0, Villa ta buga mafi yawan wasan da mutum goma bayan mai tsaron ragar ƙungiyar Emiliano Martinez ya samu katin kora saboda keta da yayiwa Rasmus Hojlund.
A sauran wasannin na gasar Firimiya Tottenham Hotspur wadda ta lashe gasar Europa League ta bana ta yi rashin nasara a gida bayan da Brighton And Hove Albion ta lallasa ta da ci 4-1, yayin da Arsenal ta lallasa Southampton da ci 2-1 a St Mary, wasa tsakanin Wolverhampton Wanderers da Brentford ya tashi 1-1.
Masu rike da kofin Firimiya Liverpool da Crystal Palace da ta lashe kofin FA sun tashi kunnen doki da ci 1-1, yayin da Ipswich ta sha kashi a gidan West Ham United da ci 3-1, a karshen kakar wasa ta bana Liverpool ce ta daya a teburin gasar da maki 84, sai Arsenal da maki 74, sai Manchester City da maki 71.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp