Chelsea Ta Dakatar Da Magoya Bayanta Hudu

Jami’an ‘yan sanda sun gana da wani mutum a tsanake bayan nuna wariyar launin fata da a ka yi wa dan wasan gaba na Manchester City, Raheem Sterling a lokacin da Chelsea ta doke Manchester City a farkon wanna watan.
Abun dai ya faru da Sterling, dan shekara 24 a lokacin da aka ci kungiyarsa ta Manchester City kwallo 2-0 a filin wasa na Stamford Bridge a ranar 8 ga watan Disambar nan da muke ciki kuma rashin nasara ta farko da kungiyar tayi a wannan kakar.
‘Yan sanda a Birtaniya na duba bidiyo na kyamarar tsaro domin dubawa ko an aikata laifin kuma sun samu bayanan dukkanin wadanda ake zargin suna da hannu a ciki, amma kawo yanzu ba su kama kowa ba.
Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ta dakatar da mutum hudu daga halartar wasanninta a yayin da ake gudanar da bincike kuma kungiyar ta bayyana cewa tana ‘’goyon bayan ‘yan sanda dari bisa dari.
Chelsea ta kara da cewa idan aka tabbatar da zargin nuna wariyar launin fatar, za su yi ‘’tsananin hukunci akan duk wanda aka kama da laifin kuma zasu cigaba da wadatar da filin wasansu na tsaro domin hana faruwar abin anan gaba.

Exit mobile version