Ofishin jakadancin China da ke Nijeriya ya musanta rahotannin da ke cewa yana daukar nauyin ayyukan ta’addanci a kasar a fakaice.
Wata sanarwa da ofishin jakadancin ya wallafa a shafinsa na yanar gizo ya karyata rahoton da jaridar The Times of the UK ta wallafa, inda ta ce “Beijing na ba da tallafin ta’addanci a kaikaice” a Nijeriya.
- Xi Ya Aika Sakon Murnar Cika Shekaru 100 Da Kafa Jami’ar Yunnan
- Da Dumi-Dumi: An Ga Watan Shawwal A Saudiyya
China ta ce rahoton ya samo asali ne daga bayanan da ba a tantance ba da kuma wadanda ba a tabbatar da su ba.
“Gwamnatin kasar Sin, da ofishin jakadancin kasar Sin da ke Nijeriya, a ko dabyaushe, suna karfafawa tare da yin kira ga kamfanoni da ‘yan kasar Sin da ke Nijeriya, da su kiyaye dokoki da ka’idojin Nijeriya, tare da aiwatar da dokokin gida da jagororin aiki, da muhalli, da lafiya da aminci, da sauransu, kuma za su ci gaba da kokarinsu a wannan fanni.
“Gwamnatin kasar Sin ta kasance kuma ba za ta taba shiga cikin kowane nau’i na taimakon ta’addanci ba.
“Zarge-zargen da ke kunshe a cikin rahoton ba su da tushe balle makama, kuma rashin da’a ne, kuma an yi la’akari da manufar rahoton.
“A cikin shekaru da dama da suka gabata, hadin gwiwar da ke tsakanin kasashen Sin da Nijeriya ya kawo fa’ida ta gaske ga alakar da ke tsakanin kasashen biyu da kyautata jin dadin jama’ar kasashen biyu.
“Za mu ci gaba da yin aiki tare da gwamnatin Nijeriya don inganta ci gaba da magance matsalolin tsaro, muna maraba da abokan huldar kasa da kasa da su shiga kokarinmu da gaskiya, amma za mu yi watsi da duk wani shiri ko matakin da zai bata mana hadin gwiwa,” in ji ofishin jakadancin a cikin sanarwar.
Rahoton a cikin The Times da aka buga a ranar 15 ga Afrilu, 2023 ya yi ikirarin cewa Beijing na ba da tallafin ta’addanci a kaikaice a Nijeriya don ruguza mafi girman tattalin arziki a Afirka.
A cewar rahoton, shugabannin ma’adinai na kasar Sin suna ba da tallafin kungiyoyin ‘yan ta’addan Nijeriya domin samun damar shiga ma’adinan kasar.
“Kamfanonin China da ke aiki a wasu sassan Nijeriya inda ake yawan kai hare-hare na kulla huldar tsaro da masu tada kayar baya…, in ji wani bangare na rahoton.