ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Sunday, December 21, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ci Gaba Da Musaya Zai Ingiza Kyautatuwar Aminci Tsakanin Sin Da Amurka

by CMG Hausa
2 years ago
Amurka

Yayin da manyan jami’an Sin da na Amurka ke kara bunkasa musaya tsakaninsu, masharhanta na kallon hakan a matsayin hanya mafi dacewa, ta farfado da alakarsu, tare da kawar da tarnakin dake mayar da hannun agogo baya, a wannan muhimmiyar dangantaka mai tasiri ga su kansu kasashen biyu, da ma sauran sassan duniya baki daya.

A baya bayan nan, mamban hukumar siyasa, kana direktan ofishin hukumar kula da harkokin waje ta kwamitin kolin JKS, Wang Yi ya gana da sakataren wajen Amurka Antony Blinken a birnin Jakarta, a gefen taron ministocin kasashe mambobin kungiyar ASEAN, inda suka yi musaya don gane da batutuwan dake jan hankalin kasashensu. Kaza lika kafin hakan mista Blinken ya ziyarci kasar Sin a watan Yuni da ya gabata, baya ga ziyarar da sakatariyar baitulmalin Amurka Janet Yellen ta kai kasar Sin, tare da zantawa da firaministan kasar Li Qiang, da ma mataimaki sa He Lifeng a farkon watan nan na Yuli. Har ila yau, wakilin musamman na shugaban kasar Amurka game da sauyin yanayi John Kerry, shi ma ya ziyarci kasar Sin ba da jimawa ba, inda ya tattaunawa da manyan jami’an kasar game da batutuwan da suka jibanci farfado da hadin gwiwar sassan biyu kan batun sauyin yanayi.

  • Sin Ta Bukaci Japan Da Kada Ta Bi Ra’ayinta Kan Batun Zubar Da Ruwan Dagwalon Nukiliya Cikin Teku

Ko shakka babu, alakar Sin da Amurka na da matukar muhimmanci, da tasiri ga kyautatuwar rayuwar al’ummunsu, da ma na sauran kasashen duniya baki daya, kamar dai yadda jami’an sassan biyu suka sha jaddadawa.

ADVERTISEMENT

To sai dai kuma, kamar yadda muka sha gani, akwai ’yan siyasar Amurka da dama dake siyasantar da alakar kasarsu da Sin, suna yunkurin gurbata tarihin dangantaka, da gurgunta cudanyar Amurka da Sin. Irin wadannan ’yan siyasa burinsu shi ne lahanta moriyar kasar Sin, ta hanyar shafawa kasar bakin fenti.

Lallai yunkurin irin wadannan ’yan siyasa marasa hangen nesa, na iya yin tasiri ga tunanin Amurkawa da dama, wanda hakan ka iya haifar da kyama, ko kin jinin Sin a cikin gida, matakin da ka iya yin tarnaki ga warware sabanin ra’ayi ko mahangar kasashen biyu cikin sauki. La’akari da haka, muna iya cewa, irin wadannan ’yan siyasa na haifar da babbar illa ga alakar Sin da Amurka, maimakon su zamo wakilai na gari masu kokarin dinke baraka.

LABARAI MASU NASABA

Wajibi Ne Tawagar MONUSCO Ta Wanzar Da Cin Gashin Kai In Ji Wakilin Kasar Sin

An Nuna Jigo Da Tambarin Shagalin Murnar Bikin Bazara Na Shekarar 2026 A Moscow

Bisa kimar alakar Sin da Amurka, da tasirinta ga ci gaban harkokin kasa da kasa, ya dace a yi watsi da ra’ayin tsirarun ’yan siyasar Amurka, masu kokarin gurgunta tafiya mai kyau tsakanin kasashen biyu. Kuma hanyar yin hakan ita ce Amurka ta nacewa biyayya ga ka’idoji, da sanarwar hadin gwiwa uku da shugabannin kasashen biyu suka amincewa, kana Amurkan ta daina tsoma baki cikin harkokin gidan kasar Sin, kuma sassan biyu su ci gaba da tuntubar juna, bisa martaba moriyar juna, da kiyaye kimar manyan batutuwan dake jan hankalin su.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Wajibi Ne Tawagar MONUSCO Ta Wanzar Da Cin Gashin Kai In Ji Wakilin Kasar Sin
Daga Birnin Sin

Wajibi Ne Tawagar MONUSCO Ta Wanzar Da Cin Gashin Kai In Ji Wakilin Kasar Sin

December 20, 2025
An Nuna Jigo Da Tambarin Shagalin Murnar Bikin Bazara Na Shekarar 2026 A Moscow
Daga Birnin Sin

An Nuna Jigo Da Tambarin Shagalin Murnar Bikin Bazara Na Shekarar 2026 A Moscow

December 20, 2025
An Fara Aiki Da Na’urar Fasahar Samar Da Lantarki Daga Iskar CO₂ Da Aka Sarrafa A Lardin Guizhou Na Kasar Sin
Daga Birnin Sin

An Fara Aiki Da Na’urar Fasahar Samar Da Lantarki Daga Iskar CO₂ Da Aka Sarrafa A Lardin Guizhou Na Kasar Sin

December 20, 2025
Next Post
Hamza Abara Ya Zama Sabon Kocin Niger Tornadoes

Hamza Abara Ya Zama Sabon Kocin Niger Tornadoes

LABARAI MASU NASABA

Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

December 21, 2025
Sarakuna Na Da Rawar Takawa Wajen Kare Muhalli A Nijeriya – Ministan Muhalli

Sarakuna Na Da Rawar Takawa Wajen Kare Muhalli A Nijeriya – Ministan Muhalli

December 21, 2025
Me Ya Sa Ake Fifita Ilimin Boko A Kan Na Addini?

Me Ya Sa Ake Fifita Ilimin Boko A Kan Na Addini?

December 21, 2025
Yadda Itacen Dorawa Ke Warkar Da Cututtuka Daban-daban

Yadda Itacen Dorawa Ke Warkar Da Cututtuka Daban-daban

December 21, 2025
‘Yansanda Sun Kama Ɗan Bindiga Da Kuɗin Fansa Naira Miliyan 5 A Delta

An Cafke Wani Mutum Da Ya Lakada Wa Dansa Duka Har Lahira A Edo

December 21, 2025
Bambance-bambancenmu Shine Ƙarfinmu — Uba Sani

Bambance-bambancenmu Shine Ƙarfinmu — Uba Sani

December 21, 2025
Kotu Ta Fara Sauraren Korafe-korafen Dalibai A Kan Jami’ar MAAUN

Kotu Ta Fara Sauraren Korafe-korafen Dalibai A Kan Jami’ar MAAUN

December 21, 2025
Tinubu Ya Sauya Sunan Jami’ar Azare Don Karrama Sheikh Dahiru Usman Bauchi

Tinubu Ya Sauya Sunan Jami’ar Azare Don Karrama Sheikh Dahiru Usman Bauchi

December 20, 2025
Wajibi Ne Tawagar MONUSCO Ta Wanzar Da Cin Gashin Kai In Ji Wakilin Kasar Sin

Wajibi Ne Tawagar MONUSCO Ta Wanzar Da Cin Gashin Kai In Ji Wakilin Kasar Sin

December 20, 2025
Matasa Miliyan 80 Ne Ba Su Da Aikin Yi A Nijeriya

Matasa Miliyan 80 Ne Ba Su Da Aikin Yi A Nijeriya

December 20, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.