Cibiyar Sheikh Isyaka Rabi’u Ta Yaye Ɗalibai Sama Da 250

Daga Mustapha Ibrahim Kano

Cibiyar Sheikh Muhammadu Rabiu da ke ƙarƙashin shugabancin Khalifa Sheikh Ishaƙa Rabiu Khadimul Ƙur’an shugaban ɗariƙar Tijjaniya ta gama shirin ɗaukar ɗalibai kimanin 3000 wanda za su haddace littafin Allah mai tsarki Al’kurani a wani shiri na Gajeran zango da cibiyar ta ke ɗaukan nauyin gabatarwa duk shekara bayanin hakan ya fito ne daga bakin Alhaji Rabiu ƙarami wanda aka fi sani da IRS a wajen bikin yaye ɗalibai kimanin 250 da suka haddace Al’kurani a wannan cibiya dake ƙarƙashin Khadimul Ƙur’an wanda aka gabatar a wannan lokaci a harabar masallacin Shehu Ibrahim Inyas da ke unguwar Gadon Ƙaya cikin birnin Kano.

Alhaji ƙarami ya ƙara da cewa Khalifa Ishaƙa Rabiu ne ya ke ɗaukar nauyin abincin waɗannan ɗalibai da sauran kayayyakin buƙatu na ɗalibai da cibiyar ke buƙata har zuwa biyan Malamai da sauran su inda ya ce burinmu mu temakawa Khalifa ba dan Khalifa bazai iya ba a’a muna san yin hakan ne domin neman Albarka da kuma neman shiga cikin wannan aiki na alkhairi duniya da lahira.

Shima a jawabinsa Alhaji Ibrahim Isah wanda aka fi Sa ni da JARIYA babban jami’in karɓar baƙi na Khalifa Ishaƙa Rabiu wanda ya yi magana a madadin Khalifa ya ce ba abun da Khalifa ya fi sha’awa kamar yiwa Al’kurani da makarantansa hidima dan haka kullum burin Khalifa ya ga ya inganta karatun Al’kurani mai girma kuma suna jin daɗi akan yadda Khalifa ke ɗaukar duk wani hadiminsa a matsayin “ɗa ta hanyar riƙe su da amana da haƙuri da kuma gaya musu gaskiya komai ɗacinta ga duk wanda ya yi ba dai dai ba.

Shi kuwa mai baiwa shugaban ƙasa Muhammadu Buhari shawara akan harkar Rediyo da Telebijin Honarabil Sha’aban Sharaɗa ya ce Najeriya na amfana da ga irin addu’oi neman zaman lafiya da ƙaruwar arziƙi da Khalifa da mabiyansa da masoyan ƙasan nan ke yi a koda yaushe dan haka ya ya bawa Khalifa akan wannan aikin alkhairi.

 

Exit mobile version