Daga Khalid Idris Doya
Shugaban Nijeriya Muhamadu Buhari zai shafe wata uku yana aiki daga gidansa, bayan ya shafe wasu wata ukun yana jinya a Landan. Wani Kakakin fadar Gwamnatin ne ya ce Beraye ne suka mamaye ofishin shugaban. lokacin da yake Landan, kuma suka lalata na’urar sanyaya daki. Shugaba Buhari ya sha suka a shafukan sada zumunta game da kin bada karin haske kan rashin lafiyar tasa, a jawabin da yayi ga al’umman Nijeriya a ranar litinin.
Ga hirar BBC kamar haka da:
GARBA SHEHU: Na farko ina son na yi jawabi cewar shugaban Nijeriya yana da ofis guda biyu a cikin nan fadar gwamnatin tarayya. Shuwagabanin da duk aka yi a baya nan Nijeriya, sukan yi amfani da wancan ofis ko kuma wannan ofis.
GARBA SHEHU: Mun dai cika bayan cewa a tarihin mulkin fadar shugaban kasar Nijeriya, shugaba Abacha shekarun da yayi yana mulki a wancan ofis na gida yake aiki. Sabili da haka wannan lalura ta kawo haka. kamar misali kwana dari 100 da ba a amfani da ofis sabili da haka a kulle yake, yayin da baya nan KWARI da BERAYE da sauransu sun damejin wayoyi na Air conditioner (na’urar sanyaya daki) har da Carpet da sauransu suka yayyaga.
BBC: Dukka kusan fiye da watanni ukun da ya kwashe a can ba a gano da wannan barnar ba sai da ya dawo?
GARBA SHEHU: Lokacin da aka gano an bude ofishin, inda aka ce idan zai dawo sai a bude a karkade a gyara sai aka ga wannan barnar. Kamfanin Julius Berger yanzu haka su ke aiki a ofishinsa. Su karkade duk wani barna da aka yi su gyata, in ma wani abu ake so a canza sai a canza.
BBC: Kamar tsawon watanni ukun da aka yi ba a taba tunanin a leka tun da idan waje na rufe an san za a samu kura ko dan wasu tarkacen kwari ba. to meye sa da ya tafi, lokacin da zai dawo ba a shiga an gyara ba tun da an san in ya dawo zai koma ofis?
GARBA SHEHU: Maganar da ake yi shi ne san da zai dawo lokacin ne za a bude ofis a karkadeshi a gyara. Ai sai da dalili, kuma kai waye kai? Da zaka zo ka ce a bude maka ofishin shugaban kasa kawai ka je ka duba?
BBC: Tsawon wani lokacin zaka dauka ana wannan gyara?
GARBA SHEHU: Yauwa to ina son ku tambayi kamfanin Julius Berger ku ji domin su suka zo suka kiddige aikin da ake bukata za a yi, su kuma aka ce su zo su yi wannan gyarar.
GARBA SHEHU: Ni tambaya ce ban yi ba, amma su da suke kwangilar sun san iya lokacin da zai dauka.
BBC: Wannan shi ne kamar karo na biyu da aka ce zai ke ringa aiki daga gida a maimakon ofis, shin baka ganin ko har zuwa yanzu bai samu karfin da zai iya zuwa ofis ya yi aiki sai yake yi daga gida?
GARBA SHEHU: Ai duk wanda ya ga shugaba Muhammadu Buhari ai ba zai yi wannan maganar ba. amma ita siyasa ta Nijeriya ai haka ta gada.
BBC: Kana ganin daga gidan zai ke aikin da suka kamata yayi kamar yanda zai yi a ofis na waje?
GARBA SHEHU: A!! Ba abun da zai rage yanzu haka da ne ke yi miki magana, dukkanin shuwagabanin sassa daban-daban na tsaro na kasar nan suna tare da shi suna ganawa.
BBC: To da yake ga shi ya dawo ya fara aiki kamar da me zai fara?
GARBA SHEHU: Da tattaunawa da shuwagabinin sassa daban-daban. Yau kuma hankalinsa ya karkata wajen harkar tsaro ta kasa.
BBC: A jawabin da yayi a ranar litinin da safe ana maganar bai yi magana kan tattalin arziki ba?
GARBA SHEHU: Dama jawabin ba a ce za a yi jawabin da zai kunshi komai da komai ba; shi shugaba Muhammadu Buhari zaman lafiya da tsaron kasa ya kankama kafin a zo a tattauna kan wasu abubuwan.
BBC: Malam Garba Shehu kenan mai baiwa shugaban Nijeriya shawara akan harkokin yada labarai.