A ranar Laraba 6 ga Satumba 2023, zababbun gwamnonin suka cika kwanaki 100 a kan karagar mulki. Kamar yadda a makon da ya gabata muka kawo rahoto na musamman a kan kamun ludayin sabbin gwamnoni, wakilanmu na jihohi a wannan karon sun duba mana halin da ake ciki a jihohin Nasarawa, Bauchi, Gombe, Yobe, Borno da kuma Jigawa a bangaren ayyukan raya kasa na wadannan gwamnonin musamman ganin al’umma sun zaku su kwankwadi romon dimokradiyya.
Ya zuwa yanzu al’ummar wasu jihohin sun fara ganin kokarin gwamnonin a bangaren bunkasa harkar ilimi, kiwon lafiya, tsaro da bunkasa walwala da rayuwar al’umma, wannan yana zuwa ne ganin irin halin matsin rayuwa da al’umma suka shiga sakamakon janye tallafin mai da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta yi wanda ya haifar da hauhawar farashin kaya masarufi.
- Zabe: Obi Ya Gaza Bayyana Yadda Ya Samu Kuri’u Masu Rinjaye – Kotun Zaben Shugaban Ƙasa
- Kotu Ta Yi Watsi Da Karar Da Jam’iyyar APM Ta Shigar Kan Ingancin Shettima
Jihohi da dama sun fara raba kayan rage radadin da ake fuskanta sakamakon janye tallafin, amma ba a nan gizo ke sakar ba don kuwa al’umma da dama suna korafin cewa, an fara rabon kayan masarufin a bisa kurakurai, wanda al’amarin zai yi wuya a iya samun nasarar da ake bukata domin a wasu jihohin ‘yan siyasa sun kwace rabon sun bar sauran al’umma a igiyar ruwa. Ga dai rahotannin wakilan namu.
Jigawa
A jihar Jigawa, duk da kalubalen kuncin rayuwar da ake fuskanta, cikin kwanaki 100 da Gwamna Umar Namadi ya share kan karagar mulki, tuni ya dukufa wajen ganin ya dora jihar kan saiti ta hanyar gudanar da wasu ayyuka domin ci gaban jihar.
Tun da farko dai, bayan saba-laya a matsayin gwamna, duk da kasancewarsa tsohon mataimaki gwamnan da ya gada, Namadi ya fara da bibiyar ma’aikatu tare da bibiyar ayyukan da ake gudanarwa domin tabbatar da cewa komai na tafiya bisa ka’ida.
Gwamnan ya kafa kwamitoci daban-daban musamman a kan matsalar karancin ma’aikata wadda take barazanar gurgunta aikin gwamnati da harkokin fansho a jihar baki daya.
Haka kuma cikin kwanaki darin, gwamnan ya yi nasarar gudanar da ayyukan ci gaba wadda suka hada da raba wa mata dubu daya naira biliyan guda, yadda kowacce daya ta sami naira dubu hamsin.
Sannan ya tallafa wa manoma da tallafin ragin kudin taki daga naira dubu N28,000 zuwa dubu N16,000, sannan gwamnan ya bayar da zunzurutun kudi har kimanin naira biliyan daya domin sayen motocin noma (tantan) guda 54 domin tallafa wa manoma.
Gwamna Namadi a yunkurinsa na rage wa al’ummar jiharsa radadin rayuwa, ya amince da kashe tsabar kudi har kimanin naira biliyan N3.848 domin sayen kayan abinci wadda suka hada da buhun shinkafa 600 daidai da Tirela 70 da kuma buhun Masara da Gero 600 daidai da Tirela 54 domin rabawa al’umma a kananan hukumomi 27 dake fadin jihar.
Haka kuma duk a cikin kwanaki darin, gwamnan ya amince da kashe tsabar kudi har kimanin naira miliyan N167.024 domin biyan kudin karatun dalibai ‘yan asalin jihar da ke karatun digiri a jami’o’in FUD, BUK, KUST da kuma jami’ar UNIMAID.
Bauchi
A jihar Bauchi kuwa, Bala Muhammad Abdulkadir cikin kwana 100 a kan karagar mulki zango na biyu ya kirkiro karin ma’aikatu, kamar ma’aikatar harkokin tsaron cikin gida, ma’aikatar kula da ayyukan jin kai da kuma ma’aikatar kula da ilimi a manyan makarantu. Ana kallon matakin a matsayin ci gaba da zai kyautata sashin walwalar jama’a, ilimi da kuma tsaron cikin jihar.
Baya ga kwamishinoni, gwamnan ya nada manyan masu ba shi shawarwari na musamman su 17 a bangarori daban-daban domin tafiyar da harkokin mulki yadda ya kamata.
Duk da cewa gwamnan ya yi alkawura a lokacin da ya ke shan rantsuwar kama aiki, ciki har da cewa ya dage takunkumin daukan ma’aikata, har zuwa yanzu da ya cika kwanaki 100 bai dauka ba. Kodayake tuni ya amince da daukan ma’aikata dubbai kuma har an shelanta wa duniya.
A bangaren tsoffin ma’aikata masu amsar fansho da giratuti, za a iya cewa har zuwa yanzu na kwanaki dari suna zaman jiran tsammani, kodayake a cikin tallafin rage radadi da gwamnatin tarayya ta bayar, jihar Bauchi ta ce ta ware naira miliyan 800 domin biyan kudaden fansho.
Daga cikin nasarar da za a iya cewa Gwamna Bala ya cimma a kwanaki 100 dinsa, ya fara daukan matakin ba-sani-ba-sabo a bangaren aiki. Gwamnan a wani taron masu ruwa da tsaki da jami’an kula da harkokin ilimi, ya yi barazanar cewa zai kori duk wani jami’in kula da harkar ilimi na kananan hukumomin da aka samu da sako-sako da aiki da yin saddu wa kokarin kyautata harkokin ilimi.
Sannan, a lokacin da yake jagorantar zaman majalisar zartaswa ta jihar karo na farko, gwamnan ya gargadi cewa dole ne mata da matasa masu shiga ofis-ofis a sakatariyar jihar suna kwaramniya dole su daina domin kwamishinoni na ofis ne domin gudanar da aikin da ke gabansu ba wai tsayawa biye wa ‘yan bangar siyasa ba.
Gwamnan a cikin kwanakinsa 100 ya zauna da bangarorin jagororin tsaro daban-daban da nufin kawo gyara da sauyi a wannan bangaren.
Tun lokacin da aka fara shiga wahalar rayuwa sakamakon janye tallafin Mai, Gwamna Bala, ya sayo sabbin motocin sufuri har guda 30 inda aka ba za su a kan hanya domin saukaka sufuri.
A lokacin kaddamar da motocin kirar Toyota Hiace a kamfanin sufuri mallakin jihar ta Yankari, gwamnan ya ce an yi hakan ne domin rage wa jama’a radadin da suke ji sakamakon janye tallafin mai.
Bugu da kari, domin tabbatar da mulki mai cike da gaskiya, adalci, Gwamna Bala ya kaddamar da kwamitin OGP domin tabbatar da ana gudanar da mulki tare da al’umma da janyo kowa a jika domin yin mulki a bayyane.
Kazalika a cikin kwanakin nasa ya kaddamar da kwamitin rabon tallafin rage radadin rayuwa da aka samu kai a ciki sakamakon janye tallafin mai. Kuma tunin kwamitin ya sayo shinkafa na biliyan biyu domin fara raba wa jama’a.
A lokacin da aka samu yankewar wata gada a kan babban hanyar Bauchi zuwa Gombe hanyar da ta hada manyan jihohin kasar nan da dubban mutane ke wucewa ta kai duk rana ta yanke, gwamnan da takawaransa na jihar Gombe sun yi tsayuwar daka wajen ganin an gyara hanyar cikin kankanin lokaci.
Kazalika, gwamnan ya kaddamar da dashen Itatuwa da nufin kare jihar daga zaizayar kasa, kwararuwar hamada da sauransu.
Nasarawa
Bayan Rantsar da Gwamna Abdullahi Sule a kujerar Gwamnan Jihar Nasarawa, ya aza tubalin gina sabuwar Sakatariyar Gwamnatin Jihar Nasarawa a kan titin Shanda cikin birnin Lafiya.
Sannan Gwamnan ya yi kokari wajen kammala tagwayen titin Shandan road cikin birnin Lafia. Duk da cewa a kwana 100 na wa’adin nasa na biyu, ma’aikatan jinya sun tsunduma cikin yajin aiki. Inda suka bukaci a biyasu hakokinsu.
Haka zalika manyan Asibitochin Gwamnatin jihar an kara kudade masu tarin yawa ga majinyata.
Sannan Gwamnan Jihar Injiniya Abdullahi Sule ya tallafa wa al’umman jihar da abinci domin rage radadin cire tallafin man fetur.
Borno
A Jihar Borno, bayan shan rantsuwar kama aiki a wa’adin mulkin sa na biyu, Gwamna Farfesa Babagana Umara Zulum ya bayyana aniyarsa ta jan kafar wando wajen ganin ya dauki ingantattun matakan sake farfado da jihar, wadda ta sha fama a hannun rikicin Boko Haram, al’amarin da ya kawo cikas ga ci gaban jihar.
A matakin farko gwamnatin jihar ta nada da rantsar da kusan dukkan mukaman da suka dace don tafiyar da harkokinta na yau da kullum. Kana daga bisani, ta karkata akalarta wajen nemo sabbin hanyoyin da za ta bi wajen rage wa jama’ar jihar wahalhalun da cire tallafin man ya haifar.
Gwamnatin Borno ta tsara raba wa magidanta 400,000 tallafin kayan abinci da na masarufi ga mabukata, wanda ake sa ran kimanin mutum miliyan biyu za su ci gajiyarsa.
A ranar Talata Gwamna Zulum ya gabatarwa da kungiyar kwadago ta kasa (NLC) reshen jihar Borno bashin naira biliyan biyu (N2bn) wanda ba ruwa a ciki, don raba su ga ma’aikatan da suka cancanta, wanda za su biya cikin watanni 24, domin rage wa ma’aikatan wahalhalun cire tallafin mai.
Haka kuma, Zulum ya kara adadin kudin sallamar tsoffin ma’aikatan jihar daga naira miliyan 100 kowane wata zuwa 200, domin inganta rayuwar ma’aikatan da suka yi ritaya a jihar.
Har ila yau, gwamnatin jihar ta bai wa ma’aikatan jihar motocin bus-bas 30, wadanda zasu rinka zirga-zirga dasu kan farashi mai sauki a birnin Maiduguri.
Yobe
A jihar Yobe kuma, Gwamna Mai Mala Buni ya bayyana wa’adin sa na biyu a matsayin zango mai matukar muhimmanci a shirin gwamnatinsa na samar da ayyukan ci gaba, inganta wadanda take da su tare da kafa tarihi domin al’umma masu zuwa. Gwamnan ya bayyana hakan a lokacin da ya rantsar da sabbin kwamishinonisa 20 a watan da ya gabata, wanda a wannan karon, zubin majalisar zartaswar jihar ta zo da sauyi, idan aka yi la’akari da na baya.
Mai magana da yawun Gwamna Mai Mala Buni, Alhaji Mamman Mohammed, ya ce cikin kwana 100 Gwamna Buni ya aiwatar da wani kaso mai tsoka na manufofin gwamnatinsa, wajen ci gaba daga inda ta tsaya a wa’adin farko kan muhimman ayyukan da suka kunshi gina sabbin hanyoyin mota a yankunan karkara, gina cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko a kowane lungu da sakon jihar Yobe.
Ya ce a cikin kwana 100 gwamnatin jihar tana shimfida muhimman hanyoyin mota a yankunan da sun fi shekara 50 suna burin samun hanya abin ya faskara sai a wannan gwamnati ta saurari korafin su tare da aiwatar musu da burinsu; Gashu’a zuwa Masaba, Jaji-Maji zuwa Karasuwa Galu, da tsohuwar hanyar Jajere da makamantan su. Raba kayan tallafin abinci ga dubban al’umma mabukata tun kafin cire tallafin man fetur da bayan an janye ga tsoffin, nakasassu, masu karamin karfi da sauran al’umma.
Bugu da kari, Gwamna yana ci gaba da aikin farfado da harkar ilimi, noma da bunkasar tattalin arzikin jihar Yobe, wanda a makon da ya gabata ya bayar da kwangilar gina katafariyar cibiyar hada-hadar kasuwancin zamani a birnin Damaturu, aikin da tuni an fara tare da tayar da babbar tashar Damaturu da bayanta, domin inganta rayuwar al’umma.
Gombe
Alhaji Muhammadu Inuwa Yahaya, shi ne gwamnan jihar Gombe mai ci a karo na biyu bayan samun nasarar da ya yi a karkashin jam’iyyar APC. A daidai lokacin da gwamnan ke cika kwanaki 100, ya yi karin naira dubu 10 ga kowani ma’aikacin jihar domin rage radadin da ake fuskanta sakamakon cire tallafin mai.
A bangaren biyan fansho za a iya cewa baina-baina, sai dai kuma kudaden giratuti har yanzu shiru a cikin wadannan kwanaki 100 din. Kodayake gwamnan ya yi alkawari a lokacin rantsar da shi cewa zai biya dukkanin basukan fansho da giratuti da gwamnatocin baya suka lafta masa kafin karewar wa’adin mulkinsa.
Duk da cewa Gwamna Inuwa Yahaya ya samu nasarar zabar kwamishinoni 17 da yake son su kasance masu dafa masa wajen tafiyar da harkokin mulki, za a iya cewa har zuwa ranar Laraba da wakilinmu ke hada wannan rahoton majalisar dokokin jihar ba ta tantance da amincewa da kwamishinonin ba. Wannan matsayar ta haifar da nakasu wajen gudanar da wasu ayyukan da gwamnan ke son cimmawa a cikin kwanakinsa 100.
Sai dai bincike ya nuna cewa an samu matsalar rashin tantance kwamishinonin har zuwa wannan lokacin ne sakamakon rashin jituwar da ta kunno kai tsakanin gwamnan da ‘yan majalisun dokokin jihar kan kudaden alawus-alawus dinsu kamar yadda wata majiya daga majalisar ta shaida wa ‘yan jarida. Sai dai ana sa ran za a iya tantance kwamishinonin a kowani lokaci.
Duk da cewa zuwa kwanaki 100 ba tare da kwamishinonin ba matsala ne, amma gwamnan ya samu nasarar yin wasu nade-nade kamar masu ba shi shawarori a bangarori daban-daban domin kyautata aikin gwamnati.
Bugu da kari, Gwamna Muhammadu ya kaddamar da majalisar ba da shawara ta musamman mai mutum 10 don jagorantar aiwatar da kyawawan manufofi da tsare-tsaren gwamnatinsa a kokarinsa na sauya kalubale zuwa damammaki da kuma samar da ingantattun hanyoyin magance matsalolin da Jihar Gombe ke fuskanta.
Domin kyautata harkokin wutar lantarki, Inuwa na Gombe ya ce jihar za ta yi amfani da sabuwar dokar wutar lantarki don habaka fannin wutar Lantarki don dogaro da kai, da ci gaban tattalin Arziki.
Yahaya ya jaddada aniyar gwamnatinsa ta hada hannu da kamfanoni masu zaman kansu don cin gajiyar wutar lantarkin Jihar Gombe, ta yadda za a inganta wutar a jihar, da bunkasa masana’antu da tattalin arziki da wadata a cikin al’umma.
Har ila yau a watan Yuli, Gwamnan Jiharya amince da kafa kwamiti mai mambobi 25 don tantance gandun kiwo da dazuka da kuma burtalolin shanu a Jihar Gombe. Dukka a wannan bangare, Gwamnan Jihar Gombe Muhammadu ya bayyana cewa gwamnatinsa ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen farfado da burtaloli da gandun kiwo da kuma dazukan jihar domin kyautata harkokin tsaro da dakile rashin jituwa da ake yawan samu.
Duk a cikin kokarinsa na kyautata harkokin sufuri, cikin kwanakinsa 100, Gwamna Inuwa ya samu nasarar kulla kyakkyawar alaka da kamfanin jiragen sama na Oberland Airways domin fara jigila daga Abuja zuwa Gombe, da Gombe zuwa Abuja. Kuma ana sa ran nan bada dadewa ba kamfanin zai fara wannan aikin.
Gwamna Inuwa ya raba kayan tallafin rage radadi ga mutum 450,000 a jihar a matsayin kashin farko.
Har ila yau, a watan Agustan, gwamnan jihar Gombe Muhammadu Inuwa ya ce, kawo yanzu gwamnatin jihar ta kashe Naira biliyan 7 da miliyan 600 wajen ginawa da samar da kayan aiki na zamani a babbar tashar motar zamani ta jihar. Gwamna Inuwa ya bayyana hakan ne ya yin da ya kai ziyarar duba tashar.
A wani mataki na tabbatar da da’a da ladabi a jihar, Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya, ya ba da umarnin rufe dukkannin gidajen casuu da raye-raye da aka fi sani da gidajen ‘Gala’ a jihar.
Domin tausaya wa al’ummar jihar Gombe musamman manoma, Inuwa ya kara sanya tallafi a farashin takin da ake sayar wa manoma, inda yanzu ya koma Naira 15,000 a kowane buhu sabanin farashin farko na Naira 19,000 don rage radadin cire tallafin man fetur ga tattalin arziki.
Daga cikin ayyukan da gwamnan ya samu yi a cikin kwanakinsa 100, ya kaddamar da shirin kare muhalli da kiyaye zaizayar kasa da farfado da muhallan da suka lalace mai suna ACReSAL, shirin da ke samu tallafin babban bankin duniya. Gwamnatin jihar ta samu nasarar biyan naira miliyan sama da 500 a matsayin kudaden hadakar aiwatar da shirin a jihar.
Sannan, a bangaren kiwon lafiya kuwa, a watan Agustan gwamnan ya sanar da shirin gwamnatinsa na daukan sabbin ma’aikatan kiwon lafiya 200 da nufin shawo kan matsalolin da ake da su a bangaren kiwon lafiya tare da shan alwashin sayowa da samar da kayayyakin aikin bukata a asibitoci.
Sannan a karshe-karshen watan Agustan, Inuwa ya jaddada aniyarsa ta farfado da kimar yankin nan na BAP/4 da ke fadar jihar don dacewa da tsarin ci gaban Jihar Gombe. Don haka ya umurci Babban Daraktan Hukumar Kula da Taswira da Zamanantar da Harkokin Filaye ta Jihar (GOGIS), Dr Kabiru Usman Hassan ya yi amfani da dokar sashin zartarwa mai lamba 4 da gwamnan ya sanyawa hannu a 2021 don daukar duk matakan da suka dace na farfado da yankin. Gwamnan ya jaddada hakan ne yayin da yake duba barnar da zaizayar kasa ta yi a yankin na BAP/4 dake bayan Otal mallakin Jihar Gombe da ke cikin yankin ci gaba na musamman da aka tsara a fadar jihar.
Sannan, Inuwa ya Amince da kafa kwamitin shirya gasar karatun Al-Kur’ani Mai Girma na Jihar Gombe daga shekarar 2023 zuwa 2025.
Gwamna Inuwa ya yi alkawarin ci gaba da gyare-gyare da kawo sauyi a fannin ilimi yayin da ya kai ziyarar duba aikin gina hanyoyin mota da wasu gine-ginen azuzuwa na zamani da ake gudanarwa a makarantar Sakandare ta Gwamnati da ke Dadin Kowa a karamar Hukumar Yamaltu Deba ta Jihar Gombe.
Ga matasa kuwa, Inuwa Yahaya ya jaddada aniyar gwamnatinsa na kimtsa matasa don zakulo dimbin basira da damammakinsu don gina makoma mai dorewa. Ya jaddada cewa shirin 3G ya wuce gangamin dashen itatuwa kawai; wani yunkuri ne dake jaddada sadaukarwar, ya ce za su kara fito da tsare-tsaren da gwambawa za su ji dadi har ma su yi murna da lale da sake zabinsa.