Ministan yada labarai da al’adu, Lai Mohammed, ya ce rashin tsaro a Nijeriya bai yi munin shekarar 2015 lokacin da Shugaba Muhammadu Buhari ya hau mulki.
A cewar kamfanin dillacin labarai (NAN), Mohammed ya bayyana haka ne a ranar Alhamis, a wajen watalacca ta jama’a, wadda wani bangare ne na ayyukan bikin cikar Nijeriya shekaru 62 da samun ‘yancin kai.
- ‘Yan Takarar Shugabancin Nijeriya Sun Sanya Hannu Kan Yarjejeniyar Zaman Lafiya
- NIS Reshen Jihar Bayelsa Ta Yi Shirin Tunkarar Zaɓen 2023
Kalaman ministan na zuwa ne a daidai lokacin da wasu ‘yan bindiga suka kai hare-hare a sassan kasar, wanda ya kai ga yin garkuwa da mutane da kashe-kashe da kuma lalata dukiyoyi.
Mohammed ya ce gwamnatin Buhari ta iya sauya labarin rashin tsaro, inda ya kara da cewa jihohin da a baya ba a isa zuwansu ba yanzu abun ya zama tarihi.
“Lokacin da gwamnatin Buhari ta hau kan karagar mulki, galibin yankunan arewa maso gabas ba sa iya shiguwa saboda ayyukan ‘yan ta’addan Boko Haram, wadanda suka mamaye yankin,” in ji shi.
“An rufe makarantu, kasuwanci. Sun rufe hanyoyin shiga yankin. A yau al’amura sun canja da sosai.”
Ya kara da cewa a matsayin kasa daya, karfin sojojin Nijeriya yana karuwa kuma zai ci gaba da samun karfin guiwa.
Ya kuma bukaci ‘yan Nijeriya musamman masu fada aji da su hada kai wajen kare kasar, yana mai cewa kowa na da rawar da zai taka domin dawo da zaman lafiya a kasar.
Ministan ya kara da cewa, “Shugaban kasa ya yi imanin cewa manyan mutane za su bunkasa abubuwa da kuma sanya su a cikin al’umma wajen samar da hadin kan kasa da kuma ba da gudummawa ga al’amuran kasa.”
Sai dai wasu na ganin wannan kalamai na ministan ba sh zauna musu duba da ganin yadda wasu yankuna musamman na arewancin Nijeriya ke ci gaba da fuskantar munanan hare-haren ‘yan bindiga.