Connect with us

TATTAUNAWA

Cikin Jam’iyyu Sama Da 100 A Nijeriya PRP Ce Kadai Ta Haura Shekara 40 Da Kafuwa – Kwamared Abdulmajid

Published

on

KWAMARED ABDULMAJID YAKUBU DAUDU, Dan takarar Majalisar Tarayya a Karkashin tutar Jam’iyyar PRP, gogaggen dan gwagwamarya, Matashi mai kishin dabbaka akidar PRP musamamn batun ‘yanta Talaka daga kangin bautar dashi da ake karkashin wani yanayi mara dadi, a tattaunawarsa da wakilinmu a Kano ABDULLAHI MUHAMMAD SHEKA, Kwamared Abdulmajid Yakubu ya bayyana matsayin Jam’iyyar PRP a tsakanin sauran Jam’iyyun da ake fafatawa dasu a kasar nan, sannan kuma ya tabbatarwa da jama’ar kasa su dai na yaudarar kansu, su sani PRP ce kadai jam’iyyar da ci gaban rayuwar ralakawan kasar nan ke  gabanta. Ga dai yadda tattaunawar ta Kasance.

Za muso ka gabatarwa da mai karatu kanka da kanka?

Alhamdulillahi ni sunana Kwamared Abdulmajid Yakubu Daudu mai neman sahalewar al’ummar Karamar Hukumar Taraun domin zama wakilinsu a Majalisar wakilai ta tarayya  karkashin tutar  Jam’iyyar PRP mai albarka. An haife ni a cikin karamar hukumar Tarauni cikin shekara ta 1974, na fara karatun firamare a Gandun Albasa primary, sai kuma makarantar sakandiren Gwamnati ta Sharada, daga nan kuma na wuce zuwa Makarantar Kwalejin Rumfa dake birnin na Kano. Sai kuma makarantar share fagen shiga Jami’a (CAS) daga nan ne kuma na shiga Jami’ar Bayero dake Kano inda na samu digiri na farko a bangaren siyasa da Jagoranci.

Shin ko mene ne ya baka sha’awar shiga harkokin siyasa?

Alhamdulillahi na fara harkokin siyasa tun acikin shekara ta 1993 wannan kuma ya samo asali tun lokacin siyasar Jami’a da muka gudanar a baya, musamman kasancewa a lokacin akwai gwagwarmayar da duniya ke ciki ta fuskar siyasa wannan ya bani damar gogewa tare da fahimtar abubuwan da suka kamata duk wanin mai hankali ya fara tunani a harkokin siyasa.  Saboda haka tun daga wancan lokaci muka samu allurar gwagwarmayar siyasa har kuma zuwa lokacin da aka kafa Jam’iyyar SDP da NRC da kuma zuwa lokacin da aka kawo karshen mulkin soja wanda aka kafa Jam’iyyun PDP da irinsu APP, a shekara ta 1998 -1999.

Na rike mukamai da  dama a wancan lokaci wanda suka hada da darakta yakin neman zaben  Hon. Mu’azzam Mai Nasara, da irinsu Marigayi Kabiru Sanda da Barau I. Jibrin har zuwa kan Sanata Rabiu Musa Kwankwaso. Duk na yi aiki da wadannan a wancan lokaci. Na rike mukamin shugaban mazaba karkashin Jam’iyyar PRP sannan kuma na dan taba koyarwa akalla shekara 20 inda na koyar da darussa daban daban. Saboda haka ina da aure da kuma yara shida, abin da na fi sha’awa a rayuwa shi ne gwagwarmayar ‘yan ta Talaka.

Duk da yawaitar Jam’iyyu da kuma Kasuwar Bukata, mene ya baka sha’awar zabar shiga tare da daukar gabaren tallata Jam’iyyar PRP?

Na zabi shiga tare da yin takara a cikin Jam’iyyar PRP ne domin da ace jama’a da sauran shugabannin arewa da ma kasa da afirika baki daya za su duba za su fahimci cewar Jam’iyyar PRP itace jam’iyyar da tafi kowacce dadewa da kafuwa wadda yanzu haka ta kai shekara 40 da kafuwa, duk cikin sauran Jam’iyyu abaya aka samar dasu sakamakon kasuwar bukata. Kuma jam’iyyar PRP tun kafuwarta bata taba  mutuwa ba tana nan tana ci gaba da wanzuwa, kuma har yanzu idan ka tuntubi dattijai za su fito maka da katin ta, za kuma su yima kirarinta,  don haka Jam’iyyar PRP Jam’iyyace da bata bukata sake tallata ta, tana kan ma’anar da aka kafata dodar bata kaucewa daga kan akidun da aka kafata akansu ba.

Wadanne abububawa Jam’iyyar ta PRP ta ban banta da sauran Jam’iyyun da ahalin yanzu ake damawa dasu?

Na farko har yanzu duk wani dan PRP zaka iske shi mai kishin Talaka ne, sannan kuma cikakken na gwagwarmayar kwatar ‘yancin talaka ne, sannan kuma Jam’iyyar PRP ce kadai Jam’iyyar da kullum aniyarta shi ne ya za a kyautata rayuwar al’ummar kasa, duk wadannan akidune dake dunkule acikin kundin tsarin mulkin Jam’iyyar PRP kuma har yanzu akansu muke dodar. Duk wadannan matsalolin da ke addabar al’umma a wannan lokaci sakacin da aka yi ne na barin akidun Jam’iyyar PRP.

Akwai matsaloli na rashin cancantar wakilan da ake turawa su wakilci al’umma, rashin cika alkawurra, matsalar yawaitar cinhanci da rashawa da rashin mutunta karami da mai karamin karfi. Saboda haka mu muna kara godewa Allah dA ya kaddara muna cikinta muna kuma rike da akidun irin na mazan jiya masu kishin al’umma, wannan ta sa muka zabi bin akidar PRP domin wanda bai san inda zashi ba to kamata ya yi ya waiga baya ya dubi yadda magabata suka gudanar da rayuwarsu.

Saboda haka tsarin Jam’iyyar PRP shi ne a gujewa karbar kudi a hannun dan siyasa, wanda duk za a tura wakilcin al’umma sai an tabbatar da sahihancin tarihin rayuwarsa, hakan ne zai tabbatar da nasarar da ake fata, musamman idan aka samu shugabannin masu akidar irin ta Malam Aminu Kano wanda kullum abin da yake kwana ya kuma tashi dashi shi ne me za a yi talaka ya samu saukin rayuwa.

Ganin irin gwagwarmayar da aka sha abaya kuma gashi ka fito takarar majalisar wakilai ta tarayya, shin kome ka hango wanda wadanda suke kai suka gaza samar dashi, kuma ka ke ganin idan an zabeka kwalliya na iya biyan kudin sabulu?

Gaskiya suna da yawa musamman idan aka dubi baiwar yawan al’umma da Allah ya yi mana, amma idan ka dubi tsarin harkokin ilimin mu al’amarin sai dai addu’a, saboda haka na ke fatan idan Jama’ar Tarauni suka amince da zabata babu shakka akwai abubuwa masu yawa da na ke dasu acikin kundin da na tanada daomin yiwa al’ummar mu hidima, haka kuma batun lafiya, akwai takaici tun dawowar siyasa duk wanda ya zo neman kuri’un jama’a sai ya yi alkawarin inganta harkar lafiya, amma ko hanya ba’a kama ba  ta fuskar kawo gyaran, ga kuma uwa uba matasanmu wadanda Allah ya yi masu baiwar kokarin neman na kansu, amma saboda rashin kishin shugabannin da suke dafe da madafun iko sun mayar da wadannan matasa ‘yan Jagaliya.

Don haka idan Allah ya bani wannan dama zanyi kokarin gabatar da kuduri agaban majalisar wakilai wanda zai samar da damar koyon sana’o’i tare da samar da jari mara ruwa domin matasa maza da mata su samu ayyukan yi. Mu tsarin PRP ba musan Jagaliya ba, kowane mutun na da daraja a idon PRP don haka ya zama wajibi a mutun dan adam, akwai kyakkyawan shiri da muka tanadarwa matasanmu, domin zama kamar sauran na kasashen da suka ci gaba ta fuskar fasaha da kere kere, wannan kuma zamu yi amfani da basirar wasun mu da Allah ya horewa domin bujiro da sabbin tsare tsaren ci gaban al’umma.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: