Wani dogon rahoto da Jaridar THE NATION ta fitar a ranar Lahadin nan ya ce, hankalin Jama’a da dama mazauna yankin unguwar Salanta da ke cikin birnin Kano ya tashi, yayin da mazauna unguwar suka yi tir da matakin da gwamnatin jihar ta dauka a yankin na ci gaba da rusa wasu gine-gine da ake zargin sun sabawa doka.
Wuraren da gwamnatin Kanon mai ci ta rushe sun hada da wani gini mai hawa uku mai dauke da shaguna sama da 90 a filin wasan tsere, Nasarawa GRA, wanda kudinsa ya haura Naira biliyan 100 da kuma Otal din Daula mai daki 90 da ya lakume zunzurutun kudi har sama da Naira biliyan 10.
- Abba Gida-Gida Ya Ba Da Umarnin Rushe Gine-Ginen Da Aka Yi A Filayen Gwamnati
- Abba Gida-Gida Ya Jagoranci Rusa Wani Gini Mai Hawa 3 Dauke Da Shaguna 90 A Kano
Mutane da dama ne suka rasa wuraren sana’o’insu saboda rugujewar da aka yi kuma ana ci gaba da ruguje wasu gine-gine domin yin takunkumi ga abin da gwamnati ta kira mamaye filayen jama’a.
A jiya ne gwamnati ta tabbatar da mutuwar mutane biyu da ta bayyana a matsayin masu kwasar kaya bayan rugujewar.
Gwamnatin ta jajantawa iyalan wadanda suka rasu, amma ta gargadi Jama’a da su nisanci gine-ginen da aka ruguje, inda ta yi gargadin cewa kusantar wuraren yana hatsari ga lafiyar dan Adam.
Gwamna Abba Yusuf ya bada damar gudanar da ci gaba da ruguje wuraren kwanaki shida bayan hawansa mulki. Ya zargi magabacinsa Abdullahi Ganduje da bayar da filayen gwamnati ga mutane masu zaman kansu.
Gwamna Ganduje ya yi watsi da zargin kuma ya ce wasu daga cikin gine-ginen majalisar zartarwa ta amince da su a matsayin ayyukan haɗin guiwa na tsarin nan na (PPP).
Motocin gwamnati sun fara aikin ruguzau a filin wasan tseren dawaki na Kano inda ta rushe wani gini mai hawa uku mai dauke da shaguna 90.
Daga nan sai gwamnan ya umarci masu aikin gine-gine a yankin sansanin alhazai da su dakata da gine-gine.
Sai dai da dare ya yi, sai ga masu satar kayan gini sun farwa gine-ginen sansanin alhazan inda suka daidaita dukkan gine-ginen da ke wurin.
Kazalika an rushe otal din Daula wanda aka kammalla aikinsa da kaso 90 bisa 100 da kuma babban shatale-talen gidan gwamnatin Kano da aka yi don cikar Kano shekaru 50 da kafuwa, na kimanin Naira miliyan 160, wanda gwamnatin ta ce ta ruguje ne saboda yana dauke da giciye (Kuros) a jikinsa, inda ta bayyana hakan da cewa sam bai dace ba a Jiha kamar Kano mai dimbin al’ummar Musulmi masu rinjaye.
Sai dai rugujewar ta dauki wani salo a jiya yayin da mazauna unguwar Salanta suka nemi a dakatar da rushe musu gine-ginen nasu da gwamnati take zargi ba tare da ba su sanarwa ba da kuma biyansu diyya.
Sun yi ikirarin cewa sun bi duk tsarin da ya dace wajen sayen filayen daga gwamnatin Ganduje.
Daya daga cikin mazauna unguwar da ya samu rauni a kansa a lokacin da Jami’an tsaro suka shiga tsakanin su da masu rusau kamar yadda Jama’a da dama suka gani a wani faifan bidiyo yana kiran wani ta wayar tarho ya kawo masa agaji.
An ji wani yana cewa: “Ba zai yuyu ku rusa kadarorinmu cikin daren nan ba tare da sanar da mu ba, muna da duk takardunmu na cika ka’ida. Dukanmu muna da iyalanmu a nan, kuma wannan zalunci ne. Sun zabo mana bala’i.
“Sun ruguza shagunanmu a kasuwa, kuma yanzu sun koma gidajenmu ba tare da an biya mu diyya ba. A nan za mu mutu.” Cewar mazaunin yankin.
Wasu kuma sun yi ta fadin Allahu Akbar! (Allah ne mafi girma) kuma sun sha alwashin kare dukiyoyinsu daga masu rugujewa.