Hukumar kiwon lafiya ta kasar Sin NHC, ta ce kasar ta yi rawar gani a fannin yaki da annobar COVID-19 cikin shekaru 3 da suka gabata, inda baya ga kare rayuka da lafiyar Sinawa, kasar ta kuma ba da gagarumar gudummawa wajen tallafawa yaki da annobar a matakin kasa da kasa.
Da yake tsokaci kan hakan, yayin taron manema labarai game da batun yaki da annobar, kakakin hukumar ta NHC Mi Feng, ya ce Sin ta aiwatar da kwararan matakai na yaki da cutar tun daga farkon yaduwar ta, wanda hakan ya baiwa sauran sassan duniya damar samun isasshen lokacin shiryawa. (Mai fassarawa: Saminu Alhassan)