Cikin watanni shida na farkon shekarar bana, jimillar darajar kudaden cinikayyar hajojin da Sin ke shigowa da su da wadanda take fitarwa sun karu da kaso 2.9 bisa mizanin shekara, inda kudaden suka kai Yuan tiriliyan 21.79, kwatankwacin dalar Amurka tiriliyan 3.05.
Babbar hukumar kwastan ta kasar Sin GAC ce ta fitar da alkaluman a Litinin din nan, inda ta ce adadin ya yi saurin karuwa fiye da kaso 2.5 bisa dari da kasar ta samu cikin watanni biyar na farkon shekarar ta 2025.
Har ila yau, alkaluman sun nuna karuwar hajojin da Sin ke fitarwa da kaso 7.2 bisa dari kan mizanin shekara, cikin watannin shida na farkon bana, yayin da adadin wadanda take shigowa da su ya ragu da kaso 2.7 bisa dari cikin wa’adin. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp