Alkaluman hukuma sun nuna Talatar nan cewa, jimillar kayayyakin da kasar Sin ta shigo da su, da wadanda ta fitar, ya karu da kashi 0.4 bisa 100, a watanni 7 na farko bana, zuwa yuan triliyan 23.55 kwatankwacin dalar Amurka triliyan 3.29 kan na makamancin lokaci na bara
A cewar babbar hukumar kwastam ta kasar, kayayyakin da aka fitar zuwa kasashen waje, ya karu da kashi 1.5 bisa 100 kan na makamancin lokacin bara, zuwa yuan tiriliyan 13.47, yayin da shigo da kayayyaki ya ragu da kashi 1.1 bisa 100 daga shekarar da ta gabata, zuwa yuan tiriliyan 10.08. (Ibrahim)