Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya bai wa ma’aikatan Nijeriya tabbacin shirin gwamnati na sake duba yiwuwar karin albashi ha ma’aikata don rage radadin cire tallafin man fetur.
Shugaban majalisar dattawan ya ba da wannan tabbacin ne a lokacin da ya karbi bakuncin gwamnan jihar Ekiti, Abiodun Oyebanji da ‘yan majalisar dokokin jihar a wata ziyarar ban girma da suka kai masa.
Akpabio ya kuma bayyana cewa cire tallafin man fetur da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi ne domin magance matsalar cin hanci da rashawa a bangaren man fetur.
A cewar Akpabio, “Nijeriya a matsayin kasa ba za ta ci gaba da rayuwa idan ba a cire tallafin man fetur ba, amma za a duba yiwuwar karin albashi ga ma’aikata domin a tabbatar da cewa ‘yan Najeriya sun samu rangwame.”
Da yake karin haske, Akpabio ya shaida wa gwamnan cewa “Majalisar Dattawa na matukar alfahari da wakilansu a majalisar ta 10.
Da yake jawabi tun da farko, gwamnan jihar Ekiti, Abiodun Oyebanji, ya yaba wa shugaban majalisar dattawa bisa nasarorin da ya samu a ofishinsa a cikin wata daya da ya gabata.
Ya bayyana cikakken goyon bayan al’ummar jihar Ekiti domin samun nasara a matsayin shugaban majalisar dattawa ta 10 da kuma shirinsu na hada kai da majalisar domin ciyar da kasar gaba.