Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo a ranar Litinin din da ta gabata ya yi alkawarin biyan Naira N25,000 ga ma’aikata da kuma Naira N15,000 ga ‘yan fansho akan albashinsu don rage musu radadin cire tallafin man fetur.
Da yake jawabi ga ma’aikatan yayin wani gangamin hadin kai da aka gudanar a sakatariyar jihar da ke Ibadan, Makinde ya ce za a biya karin kudin ne har na tsawon watanni shida.
Gwamnan, a lokacin da yake zantawa da shugabannin kwadago, da suka hada da Kayode Martins (NLC), Bosun Olabiyi (TUC), Olaonipekun Oluwaseun (JNC Public), ya ce, wannan zai zama daga cikin “karin Naira biliyan 2.2 ga lissafin albashin ma’aikatan jihar”
Talla