• English
  • Business News
Wednesday, May 14, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Cittar Da Ake Fitarwa kasashen Waje Ta Ragu Da Kashi 74 Cikin 100

by Abubakar Abba
3 months ago
in Noma Da Kiwo
0
Cittar Da Ake Fitarwa kasashen Waje Ta Ragu Da Kashi 74 Cikin 100
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Wata kididdiga da aka fitar a hukumance ta tabbatar da cewa, shekarar 2024, a cikin wata tara; Cittar da ake nomawa tare da fitar da ita daga Nijeriya zuwa kasuwannin duniyua, ta ragu da kashi 74 cikin 100, sakamakon cutar da ta lalata gonakinta a fadin kasar.

A cewar Hukumar kiddiga ta kasa (NBS), wasu bayanai na kasuwancin katare ya nuna cewa, Cittar da Nijeriya ke fitarwa waje ta ragu da kashi 74 cikin 100, wadda kudinta a shekarar 2024, ya ragu zuwa Naira biliyan 6.28, sabanin Naira biliyan 23.76 2023 da ake samu a baya.

  • Bullar Cutar Da Ke Lalata Citta Ta Sa Farashinta Ya Sake Karuwa A Karo Na Shida
  • Dalilin Rahoton Farfesa Jega Na Bukatar Taimaka Wa Masu Kiwon Kajin Gidan Gona

Haka zalika, faduwar darajar Naira zuwa 1,500 a kan kowace Dala a 2024, ya kara haifar da matsalar; wanda kamata ya yi a ce, kimar Cittar ta karu a 2023; amma sai dai cutar ta yi mata illa a gonakin da aka shuka ta, hakan ya jawo raguwar fitar da ita kasashen ketare.

Kazalika, wasu kwararru a fannin; sun yi nuni da cewa, kimar Cittar zai ci gaba da raguwa a wannan shekara ta 2025, saboda Cibiyoyin bincike kan amfanin gona a kasar, sun gaza lalubo da mafitar dakile yaduwar cutar.

Cittar dai, na daya daga cikin jerin amfanin gonar da gwamnatin taryya ta tsara za su kara bunkasa tattalin arzikin kasar da kuma kara mayar da hankali wajen fitar da ita kasashen ketare.

Labarai Masu Nasaba

Gwamnatin Tarayya Ta Gabatar Da Wasu Shirye-shirye Na Bunƙasa Kiwon Shanu

Nazari Kan Dabarun Taimaka Wa Masu Kiwon Kifi Domin Jurewa Sauyin Yanayi

dimbin Asarar Da Manoman Cittta Suka Tabka:

Shugabar kungiyar manoman Citta da sarrafata ta kasa (GGPMAN) Florence Edwards, ta alakanta samun raguwar Cittar da ake fitarwa daga kasar nan zuwa kasashen ketare da barkewar cutar da ta lalata gonakin wasu manomanta.

Florence ta kara da cewa, akasarin irin samfurin Cittar da manoman ke shukawa a fadin kasar nan, sun shafe sama da shekaru 20 suna amfani da shi.

Ita ma wata manomiyar Cittar a Jihar Kaduna, Joy Bolus ta bayyana cewa, ta kashe sama da Naira miliyan daya a shekarar da ta gabata wajen aikin noman Cittar a tata gonar, ta hanyar yin hadaka da miinta, amma saboda barkewar cutar a bara, hakan ya jawo gonar ta lalace baki-daya.

“A kakar noman bara, ni da mijina mun yi asarar sama da Naira 800, 000, bayan barkewar cutar”, a cewar Joy.

Duk kokarin da gwamnatin tarayya ta yi na magance yaduwar cutar, hakan bai samar da wani sakamako na a zo a gani ba, musamman ganin yadda manomanta a Jihohin Kaduna, Kano da wasu yankuna biyu na kasar da aka fi yin noman ke ci gaba da kirgar irn asarar da suka tabka sakamakon barkewar cutar.

karamin Ministan Ma’aikatar Aikin Noma da Samar da Wadataccen Abinci, Sabi Abdullahi ya bayyana cewa, tun bayan barkewar cutar a 2023, manoman da annobar cutar ta afkawa a gonakinsu, sun yi asarar kimanin Naira biliyan 12.

A watan Oktoban 2023, gwamnatin tarayya; ta samar wa da manoman, musamman na jihohin da aka fi yin nomanta tallafin Naira biliyan 1.6 tare kuma da raba musu magungunan feshin cutar, domin rage musu radadin annobar.

Jaridar BusinessDay, tun da farko ta ruwaito cewa, farashin Cittar ya karu da rubi shida a shekaru biyu da suka gabata, inda kowane buhunta daya a 2023 ya kai Naira 50, 000, sannan kuma ya karu zuwa Naira 300,000 a shekarar 2025.

Wasu manoman, sun alakanta hauhawar farashin da barkewar cutar a 2023, inda hakan ya jawo wa manoman nata yin asarar kimanin Naira biliyan 12.

A cikin kasafin kudi na 2025, an kara wa Hukumar Samar da Ingantaccen Irin Noma ta kasa (NASC) kashi 36, kimanin Naira biliyan 3.8, sabanin Naira biliyan 2.8 da aka ware mata a kasafin kudi na 2024, amma abin takaici; har yanzu manoman kasar, ba su iya samun ingantaccen Irin ba.

A cewar Hukumar Samar Wadattacen Abinci da Bunkasa Aikin Noma (FAO) ta duniya ta ce, a fidin duniya kaf; Nijeriya na daya daga cikin kasashen da ke kan gaba wajen noman Citta, duba da yadda kasar ta noma kimanin tan 781,000 a 2023.

Mafi akasari, Nijeriya na fitar da Cittar da aka noma a kasar ne zuwa kasuwannin Gabas ta Tsakiya ko kuma Nahiyar Turai.

“Manoman Citttar, na bukatar samar musu da Irinta, mai bijer wa kowace irin cutar da ke yi wa gonakinsu illa tare kuma da yin gwajin kasar da ake noma ta, don gano inda cutar ke fara kunno kai”, in ji Florence.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: CittaGona
ShareTweetSendShare
Previous Post

Thomas Bach: Kasar Sin Ta Ba Da Gagarumar Gudummawa Ga Bunkasa Wasannin Olympics

Next Post

Sin: Manufar Zuba Jarin Amurka Na Matukar Kassara Hadin Gwiwar Kasuwancin Kamfanonin Sin Da Amurka

Related

Gwamnatin Tarayya Ta Gabatar Da Wasu Shirye-shirye Na Bunƙasa Kiwon Shanu
Noma Da Kiwo

Gwamnatin Tarayya Ta Gabatar Da Wasu Shirye-shirye Na Bunƙasa Kiwon Shanu

3 days ago
Nazari Kan Dabarun Taimaka Wa Masu Kiwon Kifi Domin Jurewa Sauyin Yanayi
Noma Da Kiwo

Nazari Kan Dabarun Taimaka Wa Masu Kiwon Kifi Domin Jurewa Sauyin Yanayi

4 days ago
Noman 2025: Dole Ne Manoma Su Kiyaye Hasashen Hukumar NiMet
Noma Da Kiwo

Noman 2025: Dole Ne Manoma Su Kiyaye Hasashen Hukumar NiMet

4 days ago
Masana Sun Bayyana Ingancin TELA Maize Ga Rayuwar Al’umma
Noma Da Kiwo

Masana Sun Bayyana Ingancin TELA Maize Ga Rayuwar Al’umma

5 days ago
Nazari Kan Dabarun Gargajiya Domin Jawo Hankalin Zuma
Noma Da Kiwo

Nazari Kan Dabarun Gargajiya Domin Jawo Hankalin Zuma

1 week ago
Ambaliya: Yankunan Da Ba Za Su Yi Noma A Kakar Bana Ba A Jihar Neja
Noma Da Kiwo

Ambaliya: Yankunan Da Ba Za Su Yi Noma A Kakar Bana Ba A Jihar Neja

2 weeks ago
Next Post
Sin: Manufar Zuba Jarin Amurka Na Matukar Kassara Hadin Gwiwar Kasuwancin Kamfanonin Sin Da Amurka

Sin: Manufar Zuba Jarin Amurka Na Matukar Kassara Hadin Gwiwar Kasuwancin Kamfanonin Sin Da Amurka

LABARAI MASU NASABA

Binciken Jin Ra’ayoyi Na CGTN: Ma’aikatar Harkokin Wajen Sin Ta Ce Harajin Fentanyl Ya Gurgunta Hadin Gwiwar Amurka Da Sin Kuma Fiye Da Kashi 90% Na Jama’a Sun Koka Da “Jarabar” Amurka Ta Cin Zarafi

Binciken Jin Ra’ayoyi Na CGTN: Ma’aikatar Harkokin Wajen Sin Ta Ce Harajin Fentanyl Ya Gurgunta Hadin Gwiwar Amurka Da Sin Kuma Fiye Da Kashi 90% Na Jama’a Sun Koka Da “Jarabar” Amurka Ta Cin Zarafi

May 13, 2025
Tsaro: Gwamna Lawal Ya Raba Motoci 140 Ga Jami’an Tsaro A Zamfara 

Tsaro: Gwamna Lawal Ya Raba Motoci 140 Ga Jami’an Tsaro A Zamfara 

May 13, 2025
Sin Tana Kara Kwatar Wa Kasashe Masu Tasowa ’Yanci

Sin Tana Kara Kwatar Wa Kasashe Masu Tasowa ’Yanci

May 13, 2025
Masarautar Saudiyya Ta Raba Magunguna Kyauta Ga Masu Matsalar Ido A Jihar Yobe

Masarautar Saudiyya Ta Raba Magunguna Kyauta Ga Masu Matsalar Ido A Jihar Yobe

May 13, 2025
Hadin Kai Da Cin Moriya Tare Ne Hanya Mafi Dacewa Wajen Daidaita Matsalar Dake Tsakanin Sin Da Amurka

Hadin Kai Da Cin Moriya Tare Ne Hanya Mafi Dacewa Wajen Daidaita Matsalar Dake Tsakanin Sin Da Amurka

May 13, 2025
Rashin Tsaro: Majalisar Dattawa Ta Bukaci Sake Tura Sojoji Cikin Gaggawa Zuwa Borno Da Yobe

Rashin Tsaro: Majalisar Dattawa Ta Bukaci Sake Tura Sojoji Cikin Gaggawa Zuwa Borno Da Yobe

May 13, 2025
Shugaban Kasar Sin Xi Jinping Ya Tattauna Da Takwaransa Na Kasar Brazil

Shugaban Kasar Sin Xi Jinping Ya Tattauna Da Takwaransa Na Kasar Brazil

May 13, 2025
Majalisa Ta Yi Watsi Da Ƙudirin Dokar Karɓa-karɓa A Kujerar Shugaban Ƙasa A Tsakanin Shiyyoyin Nijeriya

Majalisa Ta Yi Watsi Da Ƙudirin Dokar Karɓa-karɓa A Kujerar Shugaban Ƙasa A Tsakanin Shiyyoyin Nijeriya

May 13, 2025
An Nuna Fasahar Waken Pingtan Na Kasar Sin A Najeriya

An Nuna Fasahar Waken Pingtan Na Kasar Sin A Najeriya

May 13, 2025
Gwamnan Zamfara Ya Raba Katin ATM Ga Mutane 400,000 Da Suka Ci Gajiyar Shirin ‘Cash Transfer’ A Jihar

Gwamnan Zamfara Ya Raba Katin ATM Ga Mutane 400,000 Da Suka Ci Gajiyar Shirin ‘Cash Transfer’ A Jihar

May 13, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.