Bullar cutar da ke lalata Citta, ya sa farashinta ya karu har sau shida; cikin shekaru biyu kacal, ana sayar da duk buhu guda a kan Naira 50,000 a 2023, inda yanzu kuma farashin ya tashi zuwa Naira 300,000.
Manoman cittar, sun alakanta karin farashinta nata, sakamakon bullar wannan mummunar cuta da ke harbin ta ‘Blight’, wadda ta bulla a 2023, ta kuma jawo wa manoman asarar kimanin Naira biliyan 12.
- Nazarin CGTN: Tsauraran Manufofin Amurka Na Shan Suka
- Asibitin Aminu Kano Ya Musanta Cire Mahaifar Mara Lafiya Ba Tare Da Izini Ba
Ita dai wannan cuta, tana harbin jijiyar Cittar da aka shuka ne, sannan kuma tana yaduwa zuwa sauran sassan jikinta.
Har ila yau, wannan mummunar cuta, ba karamar illa take yi wa gonakin da ake yin noman wannan Citta ba, musamman a Jihar Kaduna da wasu sauran jihohin wannan kasa, wanda hakan ya yi sanadiyar sama da kashi 90 na gonakin tabka mummunar asara.
Jihar Kaduna dai, ta kasance kan gaba wajen noman Citta a fadin Nijeriya baki-daya.
Wata manomiyar wannan Citta, mai suna Joy Bauna da ke Karamar Hukumar Jema’a ta Jihar Kaduna, ta koka kan irin asarar da ta tabka sakamakon wannan annobar, inda ta sanar da cewa, “Cutar ta lalata mana daukacin Cittar da muka shuka, domin kuwa duk ta rube, inda na yi asarar sama da Naira 200,000.”
“Na gaza sake yin wani noman a 2024, domin kuwa ba ni da ingantaccen Irin da zan sake shukawa”, in ji Joy.
“Wasu daga cikinmu, ba su samu wani taimako daga wurin gwamnati ba, wanda hakan ya sa muka gaza sake yin wani noman, idan har fadin da ake yi na cewa, duk farashin buhu guda yanzu ya kai Naira 300,000, babu shakka lamarin ya munana, sai dai idan gwamnati ta taimaka mana da Iri, musamman mu kananan manoma, wannan ne zai ba mu damar sake yin wani noman a kakar bana”, a cewar Joy.
Karamin Ministan Aikin Gona da Samar da Wadataccen Abinci, Aliyu Sabi Abdullahi ya sanar da cewa, a 2023 bayan bullar wannan cuta, manoma sun yi asarar kudi kimanin Naira biliyan 12.
Ya bayyana cewa, manoman da suka yi inshorar amfanin ne kadai, suka samu kudin dauki daga kamfanonin inshorar.
Hukumar Kula da Samar da Abinci ta Duniya (FOA) ta bayyana cewa, Nijeriya ce kan gaba wajen noman Citta a duniya, domin kuwa tana noma Cittar da yawanta ya kai kimanin tan 523,000 a duk shekara.
Kazalika, Hukumar Kula da Fitar da Kaya zuwa kasashen waje (NEPC) ta sanar da cewa, Nijeriya na da kashi 14 cikin 100 a kasuwar duniya na yawan Cittar da ake hada-hadar kasuwancinta.
“Ana fitar da kimanin kashi 90 a cikin 100 na wannan Citta, domin kuwa wadda ake nomawa a kasar nan, ta sha ban-ban da sauran wadda ake nomawa a sauran kasashe, sakamakon irin kyan da take da shi”, in ji NEPC.
Babban Shugaba, kuma Babban Sakare na Gidauniyar Bunkasa Aikin Noma ta Kasa (NADF), Mohammed Ibrahim ya bayyana cewa, a lokacin da cutar ta bulla a 2023, kimanin manoma 5,000 da ke kanannan hukumomi bakwai na Jihar Kaduna, gwamnatin tarayyya ta taimakawa da kayan noman Cittar a 2023.
Ya ce, kananan hukumomin sun hada da; Kachia, Zango-Kataf, Kaura, Kagarko, Jema’a, Jabba da kuma Sanga.
“Duk a cikin daukin bayar da kudi, gidauniyar ta NADF ta kuma taimaka wa Masa’antar Sarrafa Citta, ta ‘Illaj Ginger Factory’ da ke Jihar Kaduna, wanda hakan na daya daga cikin kokarin shirin farfado da nomanta a fadin wannan kasa”, in ji Ibrahim.
Kazalika ya sanar da cewa, an kuma kaddamar da shirin dakile yaduwar cutar, ta hanyar kirkiro da Jami’an GBECT.