Kocin Manchester City Pep Guardiola ya bayyana cewar har yanzu yana da kwarin gwiwa a kan yan wasansa duk da cewa ya buga wasanni 6 ba tare da samun nasara ba, a baya-bayan nan City ta barar da damarta bayan cin kwallaye uku rigis kuma ta kasa samun nasara a wasan da ta buga da Feyernood a ranar Talata.
Man City ta buga kunnen doki da ci 3-3 da Feyenoord a gasar cin kofin Zakarun Turai duk da cewa a minti na 75 Man City ce kan gaba da kwallaye uku amma kuma Feyernood ta tabbatar da ta samu maki daya a wasan bayan itama ta jefa kwallaye uku a minti 25, da wannan ne
- Ba Kare Bin Damo Tsakanin Man City Da Arsenal A Etihad
- Leicester City Ta Kori Kocinta Bayan Rashin Nasara A Hannun Chelsea
Manchester City ta buga wasanni shida ba tare da samun nasara ba a dukkan gasar da ta buga.
Guardiola ya ce rashin nasarar da kungiyar ke yi a baya-bayan nan yana shafar kwarin gwiwarsu amma dai duk da haka ba za su bari su barar da damarmakin da suke da su na lashe manyan kofuna a bana ba, mun yi rashin nasara a wasanni da yawa kwanan nan, akwai ‘yan wasanmu da suke fama da rauni kuma suke jinya tsawon lokaci ba tare da sun buga wasanni ba.
Kowa ya san halin da ake ciki, ba lallai ne mu daidaita komai ba dole ne mu ci gaba da atisaye, domin murmurewa sannan mu shirya tunkarar wasannin gaba domin har yanzu muna da damar gyarawa domin fuskantar kalubale,” in ji Guardiola.
Hakika wannan kaka ta kasance kakar wasa mai wahala a gare mu amma dai kungiyar ta himmatu ga abubuwa da yawa, amma abin takaici wasu abubuwa sun gindaya wanda hakan ya sa muke wahala kuma muke rashin nasara a cewar kocin na Manchester City wanda aka zurawa kungiyarsa kwallaye 17 a wasanni shida da suka buga na baya-bayan nan.
Masu sharhi akan wasannin kwallon kafa sun bayyana rashin katabus din da kungiyar ke fama da shi bai rasa nasaba da raunin da manyan ‘yan wasanta ke fama da shi da suka hada da gwarzon kwallon kafa na Duniya a kakar da ta wuce Rodri Hernandez, Jeremy Doku, Kobacic da sauransu.
Wanda dukkansu suna da rawar da za su taka a City idan aka yi la’akari da yadda dukkan wadannan ‘yan wasan suka taimaka wa City wajen lashe kofin gasar Firimiya a kakar wasannin da ta gabata.