Connect with us

Madubin Rayuwa

Ciwon Sanyi Da Rabe-Rabensa

Published

on

Matukar ana yi zinace-zinace a kowane salo, to za a yi ta samun cututtuka iri-iri, kamar masu yin Luwadi, wato namiji da namiji, ko Madugo, mace da mace, ko mace da namiji, ko masu yi da tinkiya, ko akuya, ko Saniya ko Kare, ko Alade, Ko Jaki. Kai hatta masu yi da hannu, ko da ‘yar Bebin wato ‘yartsana, ko da farjin roba, ko dai masu amfani da wani abu don ya biya masu bukatarsu. Duka suna sawa Allah ya aiko da cututtuka iri-iri, sababbi da ba a ma san da su ba, tun ai da ba a sanda HIV ba yanzu ta fito, kuma ana ganin ita ce babbar a duniya.

To wallahi matukar ba a daina an koma ga aure ba, to sai wadda ta fi HIV ta fito, saboda Hadisin Manzon Allah da Ibnu Maja da Hakim suka fitar da aka samo daga dan Umar, inda Mnazon Allah yake ce da Sahabbansa, “Khamsun izabtulyum bihinna” wato abubuwa biyar idan aka jarrabeka da su, a nan Manzon Allah ya yi gini ne a kan (Maf ’ul) wal (Jaza’u) sai ya kasance ( Mahzuf ) kuma sai ya kasance (Khabar) din ba a kawo shi ba.

Wanda Manzon Allah yana cewa “ka ga wasu mutane da za su rika aikata wani har a jarrabe su saboda shi, wato a saukar masu da masifa, sai ya ci gaba da cewa “ Wa’ a uzu billahi an tudriku hunna” kuma ina neman tsarin kariyar Allah daga ku hadu da su. To a nan Manzon Alla mai tsira da amincin Allah kamar yana nuna cewa, babu ciwon sanyi a lokacinsu, tunda ya ce da Sahabbai su yi addu’a kar su hadu da ciwon. To amma binciken masanan tarihi na duniya ya tabbatar da cewa, tun kafin zuwan Manzon Allah akwai cututtuka da aka dauka ta hanyar Jima’i. misali kamar ciwon Sanyi mai suna (Zuhuri) wato Gunoriya, akwai shi tun lokacin Fir’auna da ya yi zamani da Annabi Musa (AS) Ka ga kusan shekara 2000 ke nan kafin zuwan Musulunci.

 

Ciwon Sanyi Na Chandroid

Shi wannan ciwon sanyi ya kasu kashi 16, woto a baya mun yi bayanin guda biyu wato (Seflis), yanzu kuma za mu shiga na uku wato (Alkurha) a yaren magabata kamar yadda Raazee ya kawo a littafinsa (Hawi fiddibi) da ya rubuta shi tun shekara 1134 da suka wuce, wanda likitocin yanzu suke ce masa (karhatulain). Su kuma likitocin bature suke ce masa (Chandroid).

Shi wannan nau’in ciwon sanyi yana da hadarin gaske, domin cinye naman cikin gaba yake, kuma yana da tsohon tarihi, domin lilkitoci marubuta sun nuna alamunsa a cikin littafinsu, tun sama da shekara 3000 da suka wuce. Kuma ya kan fi tsanani sosai ga masu dabi’ar jiki na Saudawi, kuma si ma ciwon sanyi ne da ake dauka ta hanyar Jima’i.

Kuma mata da suke amfani da junansu wato (Lesbian) su daina yaudarar kansu da cewa ai shi kenan sun huta da daukar cutukan sanyi(Kalla, wa Rabbul ka’abati) karya ne, in ka ga ba a dauka ba, to dukkansu babu ciwon a jikinsu, ko kuma Allah (SWT) ya nuna ikonsa.

Ai tunda farko ma macen da take da dabi’ar sha’awar mace, ba wai wadda take yi don wani dalili ba, kamar neman kudi misali, to ai ciwon ya kamata wanda dole sai ta zo wurinmu mu ba ta magani, saboda ita sha’awa za ta motsa iska ce take nunawa a marar mutum wadda da ita ne akejin sha’awar. To amma sai a samu gurvacewar dabi’ar jikin, wanda sai ya zam kayan jikin ba sa aikinsu daidai wanda hakan sai ya haifar da iskar ta dinga shiga jijiyoyi da bai kamata su dinga shiga ba. Sannan kuma hakan sai ya sake haifarwa da mace sha’awar sha’awar ‘yar uwarta mace.

Saboda haka, yin amfani da magani mai suna (La’abarmurra) da (Istizaj) a cikin ruwan kankana, yana tafi da wannan matsalar da iznin Allah. Kuma muna nan muna rubuta littafi a kan (Lesbian) da maganinsu a likitance da addinace.

To kada mu tsawaita anan gefen tunda ba akansa muke magana ba. Shi dai wannan ciwo na sanyi (Karhatullaiyin) ya fi cutarwa a gavvai voyayyu kamar koda da marainan namiji, da marainan mace da suke cikin mahaifarta, da cikin kwaroron zakarin namiji, da fatar farjin mace ta ciki, in har ya yi tsanani ne yake bayyana a jikin fatar waje, in da za ka ga gaban mutum yana yin vawo da wani rodi-rodi, wani lokaci mutum ya dinga jin kaikayi a matse-matsinsa, in yana sosawa sai ya dinga dayewa.

Wani lokaci har da jini, ko wari ma idan mutum ya shinshina hannunsa bayan ya sosa, kuma da yake shi irin wannan ciwon sanyin cin jiki yake, ya kan sanya mace in ta zo haihuwa ta samu karuwa, kuma ko ma ba haihuwa ta zo yi ba mijinta ya kasa gamsuwa da ita, saboda gabanta ya kan karu da fadi. Kuma yak an sa gabanta ya yi sanyi maimakon dimi, namiji kuma ya kan hana gabansa girma yadda ya kamata, kuma ya kan cinye ‘ya’yan maraina tun daga mafitarsu.

Don haka sai ka ga samun ciki yana cinye wani vangare na jikin jariri tun yana cikin Mamansa.

 

Advertisement

labarai